Sashe 14
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk abinda suke fada a kunnen Hajara, hakan yasa ta juya da gudu ta shige dakinta, bata tsaya a nan ba ta kauna fadawa bathroom, tana shiga ta kalli window da tun farkon zuwanta ta fara aikin ciresa saboda shirin zuwan irin wannan rana,dan dama bata saki jiki ba ta tabbatar inda shu umarci da zaluncinsu zahida ya kai inda take zatonsa to tabbas sai sun ganota kuma ba zasu barta ba, shi yasa ta fara neman hanyar matsera,sai dai kuma kasancewar window ba irin karabici ba ne yasa har yau din bata gama ciresa ba,kuma bata da wata hanyar tserewa dole sai ta window sha dinma sai idan ta ciresa,sai dai kuma da alama wankin hula yana neman Kaita dare dan kuwa window zai dauke ta lokaci kafin ta samu nasarar ciresa gaba daya,wata kila kuma kafin hakan ta faru sun riga sun cimmata,tana cikin wannan halin kaikawo da fargabar ta tsunami muryoyinsu zahida na ce musu "ku shiga dakinta ku ɗauko ta,wani irin tsunkewar zuciya ta yi lokacin da ta ji takun sawayensu suna shigowa cikin dakin wanda sam ta manta bata rufe dakin ba saboda tsananin tashin hankali,sai dai ta yi kokarin rufe kofar bathroom din, Dan haka ta ci gaba da kokarin fincike window kafin Allah ya basu ikon karasowa bathroom din.
"Bata cikin dakin nan"ta ji wata ƙatuwar murya ta fada da alama daya daga cikin yaran danturkyi ne yayi wannan maganar, Muryar zahida ta ji tana cewa ku duba bathroom tana ciki tunda an duba ko ina a gidan nan bata nan kuma ina da tabbacin cewa bata bar gidan nan ba saboda bata samu abinda take nema ba"hakan da zai da ta fada yasa suka tunkari bathroom din kai tsaye.....
*****
Har abby ya dora hannunsa kan hadle ɗin kofar sai kuma ya dakata tare da ɗan sakin karamin tsaki, saboda tunawar da yayi key din dakin yana cikin ɗayan ɗakin nasa, hakan yasa ya juya ya nufi ɗakin dan ɗauko key ɗin.
Da sauri AMINATU ta shiga tattare takardun wanda harda hotuna a cikinsu,ba tare da ta tsaya dubawa ba ta cusa su tsakiyar littafin,.kana ta nufi kofar da gudun sauri ta murda tare da fitowa,...daidai lokacin shina Abby ya fito daga dakinsa hannunsa rike da key din dakin da AMINATU ta fito daga ciki,wani irin bugawa ƙirjin AMINATU yayi idanunta tuni sun cika da wani irin yajin tashin hankalin da bata taba tsammatar akwai irinsa a duniya ba.da sauri abby ya dago kansa dake kan key din dake hannunsa tare da zubawa wajen da yaji alamun motsi ido,tabbas yaji motsi hakan yasa ya shiga karewa falon kallo har zuwa yar doguwar corridor da ta raba tsakanin falon da dakin, leƙe_leƙe ya shiga yi har ta kaisa ga daga abubuwa kamar bayan kofa bayan firinji har da su karkashin kujeru yake lekawa,yana fara daddaga labulayen falon aminatu dake boye cikin labulen da ya zagaye bangon da zai ya raba falon da dakin ta ji zuciyarta na neman fitowa waje,yayin da gumi ya jikata sharkaf kai me karatu zaka yi zaton ruwa aka sheka mata,idan kuwa ka saurara Zaka iya jin ƙarfin gudun bugawar zuciyarta.
A hankali abby ya kai hannunsa kan labulen da AMINATU take cikinsa,yayin da bugun zuciyar AMINATU ke karuwa, hawaye tuni suka ɓalle mata, fitsarin tsoron da yake makale avmararta tuni ya fara zuba,bakinta kuwa tuni ya shiga karkarwa,ya Allah take fadi kawai a zuciyarta, zuciyar AMINATU na gab da yin bindiga wayar abby ta shiga ruri inda yayi saurin dauke hannunsa akan labulen da yake daf da janyesa,yana mai daga wayar da Muryar ta fita a amsa kuwa, Muryar zahida ce take ce masa "abby me ake ciki a nan din? Kaga daddyn Khalid din?kun yi magana? Abby Ina shegiyar aminatun? dan Allah abby ku hakura da abinda kuke nema wajen aminatu haka mu kawo karshen numfashinta a duniya abby rayuwar AMINATU barazana ce a cikin tamu rayuwar, idan muka kasheta dole musu ab zai hakura da duk wani abu da ya fara dan ita dan Allah Abby "iya abinda qminatu ta samu ji kenan ta fice daga falon da mugun gudu wanda yake tafiya tare da bugun zciyarta da take neman fashewa.
Da sauri abby ya dawo da baya yana watsa idanunsa akan kofar falon,yayin da zahida take ta faman surutai baya fahimta saboda yanzu ta kuma tabbatar da cewa wani ya shigo bangarensa"kashe wayar yayi ba tare da ya tankawa zahida ba,kai tsaye ya nufi kofar falon tare da tabawa dan yaji ko a bude take, amma sai ya ji kofar gam babu alamun an bude ta an fita,to amma fa yaji karar taku kamar ma gudu ake yi,ganin yana bata lokaci wajen dogon nazari yasa ya koma dakin ya fara duba abubuwansa masu muhimmanci duk da cewa baya tunanin ko an shigo zaka a iya daukar wani abu a dakin, yana da tabbacin duk abinda aka taba ba zai tabu ba bare ya dauku,idanunsa ne suka tsaya kan littafin da yake tamkar mahaɗin numfashinsa wanda dama yasan ko da yaki da aljanun duniya basu isa iya daukar littafin ba saboda aikin da aka yi akansa,ajiyar zuciya ya sauke tare da jin duk wani kokontonsa ya kau, sai da ya kuma.shafa littafin yana murmushi sannan ya dauki abinda zai dauka a dakin ya fito...
******
Cikin tashin hankali Hajara ta ci gaba da sa duk wani karfinta wajen cire window saboda jin sun fara jijjige kofar bathroom ɗin kuma gab suke da ɓalle kofar saboda dukkan su suka taru akan kofar.hannunta ne ya taba kugunta take ta tuna da yar karamar wayarta da take a kashe sai lokaci lokaci take kunnata idan bukatar hakan ya taso,da sauri ta cirota tare da kunnawa,kai tsaye sunan mus ab ta lalubo duk da cewa bata da tabbacin zai taimaka mata tsakani da Allah, sai dai idan ta tuna abinda yayi akan innawuro sai taji kwarin gwiwa hakan ya sa ta shiga kiransa.
******
Fotowarsa daga bathroom kenan ya dauro alwala ya ga karamar wayarsa na kawo haske,bai yi jinkiri wajen dayawa ba,saboda shi dama baya kashe wayarsa kuma yana yin haka ne saboda masu neman taimakonsa,"nice wadda na baka wasika ranar nan a asibitin JGK a halin yanzu ina cikin masifa dan haka ina bukatar taimakonka,ina gidan surukanka, ka temaka min ta hanyar da ba zasu san kai ne ba saboda bana son jefa rayuwarka cikin hadari"a daidai nan ta samu damar cire window, dan haka ta katse wayar.
Zubawa wayar ido MUS'AB yayi kafin kumq ya ɗan fesar da huci ta cikin bakinsa,a nutsensa ya lalubo wata nomber, kira daya aka daga,"ka duba na yi maka test"daga haka ya kashe wayar tare da nufar kebantaccen wajen yin ibadarsa ya tada iƙamar ƙiyamullali.
Hajara na samun damar haurawa su kuma suka samu damar ɓalle kofar,ganin window a cire a kasa yasa suka gane cewa ta fice ta nan, dan haka da gudu suka fita dan mara mata baya,Hajara kuwa bata yi kokarin bin tafkekiyar kofar gate din gidan ba dan tasan zasu iya cimmata, kai tsaye ta bi doguwar katangar da ko barawo sai yayi da gaske zai iya haureta,amma dake abin daga Allah ne idan yayi niyar baka kariya ko a bakin kura kake sai ka tsere, sai ga Hajara ta haure doguwar kantanga duk da cewa ta ji ciwo sosai dan kuwa a dirgowar da ta yi sai da taji alamun karaya, bata tabbatar ba sai da ta kasa mikewa alojacin kuwa har sun danturkyi sun fito wajen gidan,"gata can ɗan turƙyi ya faɗa suna nufarta da gudu,sai dai kafin su karasa inda take wata bakar mota ta isa wajen kafin kiftawar ido sun nemi Hajara su ransa ko kyallin motar basa hangowa bare su yi tunanin zasu iya cimmata.
Wani irin ihu ɗan turƙyi yayi irin na baƙi cikin anga samu anga rashi,da gudu suka koma gidan dan ɗauko mota su bisu,sai Alhaji Kabir ya hana su yana cewa "baza ku bisu ba kuna da tabbacin waye ya dauketa?ba kuyi tunanin ko MUS'AB ba ne kuke son gin wannan gangancin?"wani irin kuka me hade da ihu zahida ta sa tana cewa "ba zai yuwu ba ba mus ab ba ne,abba kayi min wannan bakin idan hakan ta kasance,zan gwammace mutuwa akan abinda zai biyo bayan rayuwata,daga Ni har ku,babu wanda zai sha,dole ne a nemo Hajara duk inda ta shiga saboda ta wajenta ne kawai za mu samu amsar tambayinmu,dan kun san cewa bibiyar daddyn Khalid ba abu ne me sauki a wajen ko wa nene ba,har gwara waccen yar iskar yar rigar amma itama in dai har bakinsu daya da shi bibiyarta zai zama abu me matukar wuya"ta karasa maganar tana jan wani irin numfashin tashin hankali, idanunta sun kada sun yi jajur kamar garwashin wuta,babu abinda take hangowa sai daukakarta karfinta kudinta da kuma mus ab dinta,yadda take jin tsoron rabuwa da waɗannan abubuwan bata tsoron mutuwa dan ita manta ta ma take a lissafinta.
Duban su ɗan turqui daddyn zahida yayi tare da yi musu nuni da su tafi kawai shima br fele umarnin tafiya ya bashi akan cewa idan sun dan samu nustuwa zasu neme su,zama suka yi gaba daya su biyun suna kallon zahida da take yi musu dan karamin hauka,duban juna su kayi suna tuna wani abu shu dadde makamancin wannan wanda basa son yawan tuna shi ma a cikin rayuwarsu..
******
Abby yana fitowa kai tsaye mota ya nufa ya shiga tare da tayar da ita,ya fice daga gidan bayan security sun bude masa kofar,mus ab dake tsaye can saman barendar dakinsa yana kallon fitar abbyn ya lumshe idanunsa tare da ɗan shafa kwantacciyar sumarsa,yana jin wani abu me nauyi a ransa, ta bangare guda tambayoyi ne suke ta shawagi saman kansa,wai mutanen na suke shiryawa a rayuwarsu?me yake shirin faruwa da gidansu? Ya a kayi AMINATU da innawuro suka shigo cikin labarin?me ye ainihin abinda iyayensu suke dauke dashi tun fil azal,tabbas akwai wani gingimemen al'amari a cikin duka rayuwarsu, lamarin yana bukatar lissafi da nutsuwa ya tabbatarwa da kansa hakan.