Sashe 56
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Falon Alhaji babba ta nufa inda tana daf da shiga ta ji Muryar Alhaji babba yana cewa,"mus ab tun lokacin da aka fitar da zahida US cikin ikon Allah ta samu taimakon gaggawa daga manya kuma kwararrun likitoci shine dalilin da yasa aka samu wannan ci gaban,yanzu haka tafiya ce kawai bata yi kuma kullum ana samun ci gaba dan bakinta ma yana fitowa kuma dayan hannun shima tana iya amfani da shi tafiyar ce dai sai a hankali,shi yasa na zauna na yi nazari da tunani akan maganar ka da ita,na ce me zai hana tunda ta yi nadama kuma akwai rabon da a tsakaninku ka mayar da ita dakinta ka bata dama ta karsh....faduwar Aminatu da suka ji ya hana Abba karasa maganarsa,da gudu duka fito dan ganin abinda ke faruwa,aminatu suka gani kwance babu alamar nunfashi yayin da har jini ya fara bin kafafunta,cikin kidima da ficewar hayyacin da ba a taba ganin mus ab a ciki ba ya sunkuceta yayi waje,da gudu m jauro ya karaso ya shiga ya tayar da motar tare da fugarta suka bar gidan,shima Abba da nana mota suka shiga suka bi bayansu, lokaci daya hankalin jama ar gidan ya tashi da ganin jinin dake bin jikin aminatu.
Kai tsaye ABM hospital m jauro ya wuce da su,mus ab gaba daya ya rude fuskarta kawai yake mari yana kallon jinin da ke zuba a jikinta wanda tuni shima ya bata shi,suna shiga aka matso da gadon marasa lafiya dan a dorata a kai amma mus ab tuni ya sunkuceta yayi ciki da ita ba tare da ya tsaya sauraren gadon ba,da gudu likitoci kusan biyar suka bi bayansa, dama su kullum a shirye su ke bare kuma an zo kan me kankat ai basu ga ta bata lokaci ba,dakyar suka lallaba mus ab ya fita daga dakin,daidai lokacin su Nana suka karaso da sauran yan gidan da duk suka biyo su daga baya,kowa ka kallesa hankalinsa a tashe,mus ab kuwa tun da ya kifa kansa jikin kofar dakin bai dago ba, bare a fahimci halin da yake ciki,Abba kuwa gab daya ji yayi kamar shine ya zama sanadi dan ya tabbata maganar da yayi aminatu ta ji har hakan ya zama sanadin faduwarta.
Tunda zahida ta ga an yaye an tafi asibiti ta kuma jin wani irin karaya, tale ta sawa zuciyarta hakuri da mus ab Dan yansu ta kuma tabbatar da cewa ta rasa shi rasawa ta har abada,har yanzu kishin nan nata yana nan dan haka koda ta koma auren mus ab ba zata taba zama lafiya da zuciyarta ba ko da ace bata cutar da aminatu ,kuma yasan bazata taba samun farin ciki faga ko wanne bangare ba saboda ita tana da babban tabo na uba da kuma ita kanta,kuka ta ci ta koshi ta bawa kanta hakuri da niyar ta bar mus ab har abada.
******
Fitowar Dr ema shi ya sa mus ab dago kansa, dan ba dan a hankali ya bude kofar ba da mus ab zai iya faduwa saboda yadda ya hada kansa da kofar,zubawa Dr ema din ido yayi ba tare da ya iya bude bakinsa ba, jan hannunsa Dr ema yayi suka wuce office dinsa,zama yayi akan kujera yana kallon mus ab da ya yi masa tsaye hannayensa goye a bayansa idanunsa kyam akan ema ɗin ko kiftawa ba yayi,duk sai ya dabarbartar da ema din da tsananin kwarjininsa ya rasa ta ina zai fara maganarsa ma,gane hakan da mus ab din yayi ne yasa shi dauke idanunsa da kansa yana fesar da numfashi me zafi, cikin sauri ema ya fara masa bayani"firgitar da ta yi ne yasa ta fadi, mun yi ƙoƙarin tsaida cikin dake jikinta,duk da hakan yana da nasaba da saurin kawota da aka yi,in sha Allah zata farka lafiya, sai magungunan da za a bata wanda zasu taimakawa cikinta wajen inganta lafiyarsa"shi kansa Dr ema sai da ya sauke tasa a jiyar zuciyar bayan yaji saukar ta mus ab,hannu ya mika masa ssu kayi masabaha yana cewa,"zan iya ganinta"?yes zaka iya ganinta amma ba a bukatar hayaniya "fita mus ab yayi,gaba daya suka yo kansa, kasa ce musu komai yayi dan ba shi da bakin da zai iya zaman yi musu dogon bayanin da Dr ema yayi masa,ganin ya shige dakin qminatun yasa Abba ya tafi wajen eka din ya jiyo bayanin da kansa,yana sanar da su kuwa suka shiga hamdala fuskarsu na bayyana irin farincikin da yake kasan zuciyarsu.
A hankali ya zauna daf da kanta yana kallon fuskarta da ta yi fayau kamar wadda ta yi jinyar kwanaki,shi kansa bai san tsawon jimarwa a wajen ba, ji yayi kawai ta ɗora hannunta saman nasa da yake kan goshinta, a hankali ya bude idanunsa da suke a lumshe,tare da sunkoyowa ya sumbaci labbanta da suka dan bushe yana fadin me kike ji ina yake miki ciwo?"maimakon amsa sai hawaye da suka shiga zarya akan fuskarta,lumshe idanunsa yayi yana jin zafin zubar hawayennata a cikin zuciyarsa da gangar jikinsa,hannunsa dake kanta ta ture tana ƙoƙarin tashi, kamata yayi ya taimaka mata ta tashi zaune hannu yasa yana share mata hawayen da suka ki tsayawa,yana cewa pls abinda kika ji ba zai yiwu ba, sminatu ba zan iya rayuwa da wata mace bayan ke ba,saboda Annabi umartarmu yayi da cewa mu yi aure idan har mun san zamu yi adalci, to Ni mus ab sulaiman jaafar ba zan taba iya adalci tsakanin Aminatu da wata mace a duniya ba ko a aljanna kin isheni a matsayin mata, saboda nasan zaki bani farin cikin da mata dari ba zasu iya bani shi ba,ki yarda dani dan Allah kar ki mana asarar yar so"daddy ba kai ne da kanka ba kana da iyaye kuma ba kai ne ka nemi wannan auren ba abba fa da kansa yake baka umarni, abba kuma mutum ne mafi kololuwar daraja a wajenmu matsayinsa ya wuce yayi umarni mu ki bi, wallahi daddy mutuwa zan yi ba zan hana ba ba kuma zan bijire ba sai dai nasan daga wannan rana ba zan kara lafiya ba wata kila wannan batun shine sanadin mutuwat....."ba zaki mutu ba qminatu in sha Allah Ni ba zan zama sanadin mutuwar ki ba, ko da bake CE kika zama sanadin dawowata cikin farin ciki na ba,kuma ba umarni na bawa mus ab ba shawara ce, dan haka daga nan mun kulle maganar nan har abada ba zata kuma tashi ba,dan haka ki kwantar da hankalinki kar ki min sanadin tawa matar son"ya karasa maganar da mayalwacin murmushi akan fuskarsa, maganarsa ta bawa wanda suke bayansa dariya ta kuma bawa qlinatu kunya sai gata cikin kirjin mijinta,da sauri abba ya juya yana cewa su Nana "ku muje gida kawai zasu taho daga baya "hakan yasa suka koma basu karasa shiga dakin ba duk da cewa sun so ganin aminatun sosai.
Suna fita mus ab ya kuma yi mata shinfida a cikin jikinsa yana cewa ashe matar so haka take da kishi ban sani ba"mintsininsa ta yi a ciki wanda yasa shi sakin faffadan murmushin da yanzu ya daina yiwa aminatu wuyar gani inndai suna a tare daga ita sai shi,idan kuwa acikin mutanene sai dai ya dinga binta da mayen kallon da yake huda tsokar jikinta yana shigewa jinin jikinta.anan suka zauna har sai da ta cika awa biyu cif sannan aka sallame su ,suka tafi gida.
A nan zahida ta kuma ganin tsagwaron son da mus ab da ahlinsa suke yiwa aminatu, abinci ma a baki Nana ta bata tana wani lallaiyata kamar kwai innawuro na sannu Hajara na kaiwa da kawowa wajen ganin ta wadatata da komai,Anne ma har da ja mata yatsun kafa saboda kwanciyar da tasha,ita kan sai komawa ɗaki ta yi tana faman ciwon rai da nadamar da har ta mutu ba zata daina yinta ba.
Sai wajen karfe tara sannan Anne ta ce aminatu ta tashi su rakata dakinta, kallon annen ta yi sannan ta leka mus ab da yake daga can karamin falon Abba, sannan ta kuma dawo da dubanta kan Anne tana cewa "kiji min mata mijina yana nan zaman jirana amma ki bude baki kice wai zaki rakani"tabe baki Anne ta yi tare da cewa to yar Sarkin miji a umma ta gaida ashsha"dariya aminatu ta yi sannan su kayi sallama.
Suna fitowa waje aminatu ta coge tare da rike kugu tana yatsina fuska, kallon ta yayi da alamar tambaya?tura baki ta yi kama cikin Muryar ta ta sangarta da in ta yi take sanya musu ab cikin wani hali na tsananin shaukin ta ta ce"to ba yar so ce ta ce ita bazata iya tafiya ba sai dai daddy ya goyata "juyawa kawai yayi ya kurkusa ta haye gadon bayansa tana dariya har da cewa kuma ka yi a hankali kar ka yi sauri saboda kar ta gaji"cikin sauri zahida ta yi baya daga jikin windown ɗakinta tana maida numfashin ta da taji kamar za a zareshi.
Bai dauke ta a ko ina ba sai dakin su dan babu abinda suka raba komai nasu a tare yake, mus ab ya ce aminatu ta zama rayuwarsa rabuwa da rayuwa kuwa sai lokaci yayi.duk da cewa ta sha wanka a bangaren Nana amma sai da ta kuma yi tare da yarimanta inda tun daga bayin lissafinsu ya fara kwancewa,a haka har suka fito kai tsaye masaukin da zasu amayar da zazzafar kaunar da suka tara suka nufa,cikin bargo suka shige aminatu na cewa daddy kashe mana wuta fyadams duk ta kwashe mana sirrinmu tana ta barbadawa fans dinta na yar gudan yarbawa da matar dan birni, b azamu bata sirrin yau ba saboda me tsada ne "daga haka kuwa naji dif sun kashe fitila da lalube na samu na baro dakin ina cizon yatsa dan nasan yau da dakyar idan oga mus ab bai kuma yin kuka ba.
*****