← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 57

Sashe 16

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dubansu Alhaji Garba yayi idanunsa duk sun zurma a iya wannan awannin da suka yi cikin damuwa,ya ce"Jamil anya kuwa ba bakin mutanen nan ne ya fara bin mu ba?anya kuwa ba tsinuwarsu da la antarsu ce ta fara tasiri akanmu ba?idan ba haka ba ta yaya lokaci daya abubuwa irin waɗannan zasu fara taba mu,na farko dai ga AMINATU duk da cewa mune muka shigo da ita cikin rayuwarmu amma tunda ta waɗo muka Gara ganin ba daidai ba cikin rayuwarmu da kasuwancinmu,sai kuma ga Hajara wadda muke kallonta a karamin alhaki,daga karshe da lalacewar ta yi yawa sai kuma ga mus ab wanda shi kadai gayyane,bana tunanin idan mus ab ya gano kasuwancin mu zai daga mana kafa duk da mun kasance iyayensa"Alhaji Kabir ya karbe da cewa sai yanzu na fahimci dalilin damuwar Jamil akan tunawa da wancan tsohon al amarin,tabbas idan muka bari mus ab ya fara bincike akanmu to allura zata tono garma kuma wallahi kashinmu ya bushe,kunga kenan hanasa cika burinsa na zama br be mana rana ba dan kuwa tsohon mikinsa ne zai motsa ya fanshe takaicinsa akanmu sabodn shi din dan baiwa ne mu sheda ne akan hakan"tunda suka fara magana abby ya kasa tankawa sai fuskarsa da yake ta faman shafawa, sai daga can ya daure ya daga kansa sama tare fara magana da cewa,jikina ya fara bani daya daga cikinsu ya fara bibiyata ko shi ko waccan shu'umar yarinyar me kama da aljanu"zuba masa ido su kayi gaba daya kafin cikin karfin hali Garba ya ce"ya akayi ka gane hakan?"kai tsaye ya bashi amsa da cewa "yau din nan yau naga abubuwan da suka saka Ni cikin kokwanto duk da cewa ban ga alamar shiga ko fitar wani ba, daga kan kofofi zuwa abubuwan da suke ajiye sai kuma na ga alama ta jin motsi da kuma ganin shaidar digon wani abu kamar ruwa kamar kuma fitsari sai da zan fito na taka ban kawo komai ba har sai da na ahiga mota na dau hanyar dawowa nan sannan tunanina da kissafina suka sauya daga kan tunanin babu wamda ya shiga bangarena"tabbas an shiga"cewar Alhaji Kabir yana mikewa tsaye hannayensa goye a bayansa, sannan ya dora da cewa "ke nan wannan shine lokacin da ƙarfan kafa ya bamu na komawa gare sa?".

Alhaji Garba ne ya karbe da cewa "tabbas wannan shine lokacin da yayi mana misali dashi kuma tun dazu da zahida take wannan haukan na shiga wannan nazarin kenan tunaninmu yazo daya da kai Kabir?"

Hannu abby ya dora sai duka suka dora nasu akan nasa tare da runtse idanuwansu ko wannensu da abinda yake faɗa take kasan wajen ya fara budewa suna yin kasa a hankali a hankali har suka nutse cikin ƙasan gurin, ya koma ya shafe tamkar babu halittar da ta taɓa tsayawa a wajen.

Kana kallonsa gaka mahaukaci tuburan,saboda yanayin sutturar dake jikinsa, dattijo ne wanda a ƙalla zai kai shekara sittin da ɗoriya, a zaune yake gefen wani katon kwalbati dan ba dan kayan jikinsa da yanayin dattin da yake tare da shi ba za a iya kiransa da me hankali,baya un baya um'un sai ido da yake bin mutane dashi, AMINATU ce tazo wucewa ta wajen har ta wuce sai ta dawo ta tsaya a kansa tana yi masa magana,sai ga wata mata tsohuwa tukuf har da sanda a hannunta ta tsaya gefen aminatu tana cewa "baya magana tun tsawon lokacin da muka sansa a matsayin mahaukaci"daga haka matar ta tafi ta bar aminatu tsaye tana kallon mutumin da shima kallonta ya ke yi,juyawa ta yi zata tafi ga mamakinta sai ta ji mutumin yana cewa ko da kin tafi ina fata zaki dawo saboda ni, ko da kina nesa da inda nake ina fata ALLAH ya kawo ki inda nake ,duk inda kike ina fata ALLAH yasa miki tunani da son taimakona kizo ki nemeni a duk inda nake a fadin duniyar nan,amma dai yanzu ki tafi domin shirin dawowa gareni domin ki fidda Ni halin da nake ciki dan ina jin cewa kece wadda Allah ya tiro dan ki zama sanadin kubuta,idan kin shirya zuwa temakona kizo garin k........jansa da wasu mutane su kayi shi ne ya hansa karasa mata sunan garin,da gudu aminatu ta busu tana cewa ku barsa ya fada min ku sakesa ku daina dukansa ku barsa ya fada min dena hango ƙurar mutanen da ta yi ne ya sa ta zubewa a wajen tana wani irin kuka tana fadin "ku barsa ya fada min ku dena dukansa dan Allah ku rabu dashi,.ku barsa ya fada min. ku barsa ya fada min.kubarsa ya fada min........

Kamar a cikin mafarki yaji kukan aminatu tana dukansa tana fadin "ku barsa ya fada min ku dena dukansa"abinda take ta fada kenan tana kuka sosai.

Riketa yayi sosai yana tofa mata addu'a dan ya tabbatar firgicin mafarki ne,da kyar ya samu ta daina kuka da sambatun ta yi luf ajikinsa tana maida numfashi kamar wadda ta yi gudun ceton rai.

Damuwar da ta ga yana ciki ne yasa ta yin shuru amma ba wai dan ta yi baccin ba,saboda mafarkin da ta yi ya tsaya mata tamkar yadda lamarin baffanta ya tsaya mata a rai, sosai fuskar mutumin ya tsaya mata a rai, dan ko yanzu ta gansa tsaf zata ganesa, luf ta kuma yi a jikinsa tana jin saukar bugun zuciyarsa da yake tafiya a nutse,shin da me zata fara ne?bata jin zata iya mantawa da al amarin mutumin nan domin kuwa bata barsa a mazaunin mafarki kawai ba,tana ji a jikinta cewa akwai wannan mutumin kuma tasan yana nan yana jiranta kamar yadda ya fada,ji ta yi zuciyarta ta kuma yin wani irin rauni idanunta suka kuma cika da kwalla tausayin mutumin yana neman hanata sukuni, ji take kamar ba ita ce ta jiyan nan da take ta zuba shaƙiyanci a store da wajen cin abinci ba,ji take kamar ba aminatun da take cikin walwala da farin ciki ba aminatun da bata san meye damuwa ba,aminatun da bata san meye nauyin zuciya ba,ashe bata sani ba aminatu bata gama kammala ba ne,lokacin mafarin shafin kaddararta bai yi ba ne,sai yanzu lokaci yayi, lokaci ɗaya a rana ɗaya dare ɗaya kaddararta ta juya sabanin farinciki wadda bata da tabbacin iya yaushe Ubangiji ya diba mata na kammaluwar babin kaddarar da jarrabawar rayuwarta,iya ƙarshen rayuwarta ne ko kuma Ubangiji zai kawo lokacin yankewarta kafin zuwan numfashinta na ƙarshe?"bata da wannan amsar hakan yasa nauyin kirjinta ya ƙaru,tuni kukanta ya kuma karuwa saboda komai sabo take jinsa gata me kananun shekaru bata jin zata iya dauka,to amma shi fa Ubangiji babu ruwansa da girmanka ko kankantarka idan yaso jarrabarka ze jarrabeka ne duk ta inda yaso a lokacin da yaso ya kuma yanke maka a lokacin da yaso idan be so ba kuma ka kare rayuwarka cikin jarrabawa mafi muni da kalubalen rayuwa iri iri,ko kuma ya jarrabeka ta bangaren da idan ba ka kasance me ilmi ba ba zaka taba cewa rayuwarta ka ma jarrabawa ba ce,domin zai baka lafiya kudi ilmi iyaye mata yaya miji kai gaba daya zaka ga rayuwarka na tafiya daidai tamkar kaine ka tsara abarka,sai dai kuma ita rayuwa me kyau ko akasin haka gaba dayanta jarrabawa ce, Allah ya bamu iko cinye jarrabawar rayuwarmu.

Sam babu bacci a cikin idanunta ko da ta rufe idanunta mutanen nan ga da uku take gani ko wannensu na dora a hanyar bukatarsa,baffanta da wannan matar da bata san ko fuskarta ba bare ta gane ta santa ko bata santa ba, sai kuma mutum me suffar mahaukaci,bazata iya bacci ba dan haka a hankali ta zamewa daga jikinsa tare da sauka kasan kafin ta mike nufi bathroom,a ranta tana tuna nasihar malam wadda a lokacin da yake mata hankalinta ma baya kansa saboda bata fahimtar komai akan abinda yake fada din domin bata taɓa ta imanin zata riski kanta acikin makamancin yanayin da yake magana a kai ba.

"AMINATU bana so naga kina wasa idan muna karatu saboda ke marainiya ce samun ilimiki shine zai taimakeki duniya da lahira wannan karatun da muke a cikinsa zaki gane yadda zaki fuskanci rayuwarki domin ita rayuwa tana zuwa da kalubale iri iri, idannkika samu ilmin jare kanki to duk a yanayin da rayuwa tazo miki za karbeta hannu bibbiyu saboda kin tanadi makaminki a hannunk"to Ni Malam wace irin rayuwa ce zata zo min nan gaba da har kake irin wannan maganar?"a lokacin malam dariya yayi kafin ya dora da cewa aminatu ai ita rayuwa gaba daya jarrabawa ce sai dai kowa da irin yadda tasa take zuwan masa,ina gaya miki wannan ne saboda gaba duk da cewa bana miki fatan shiga wani hali sai dan ita nasiha da ilmi ba sai ka zo wajen ba ya kamata a dinga tuna maka da su saboda zata yi amfani ko ga waninka ne"to malam me ye jarrabar Nan ne kuma kaine zaka yi min ita?"girgiza kai yayi tare da cewa bani zan miki ba Ubangiji da ya halicci rayuwarki ya halicceki ne tare da jarrabawarki tun kafin kizo duniya Ubangiji ya tsara miki rayuwa tare da kaddarorinki wadda itace jarrabawar da nake fada miki,to ko da zaki kasance cikin rayuwar nan guda biyu wato jarrabawa me kyau ko akasinta,ki kasance me godiya ga Ubangiji ki kasance me kusantarsa ta hanyar ambatonsa sannan ki rike istigfar da talatin Annabi ki yi yakini da duk bukatarki a wajen Ubangiji saboda shi salati maganin komai ne kuma ba a kebance wata bukata ance ita kadai salati yake magani ba, a'a shi salati komai ne haka istigfar neman kusanci ne, idan kin shiga damuwa kinji lissafi ki ya kwace tashi ki gayawa Allah a lokacin da ya fi buƙatar rokon bayinsa yake amsa addu'a ba tare da hijabi ba,nasan wata rana ko a yanayin farinciki kike za ki tunani kuma zakiin addu'a saboda na dora ki a kan hanyar nasara mikakkiya""......
Chapter 16 · 0% Book details