← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 57

Sashe 43

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A cikin wannan yanayinne Allah ya kawo MUS'AB garin,wanda da farko mutane sun nuna rashin yardar su akansa,amma sai aka samu sabanin hakan daga wajen me gayya me aiki wato baffa Yusuf,tunda baffa Yusuf ya karɓi mus ab hannu bibbiyu dole suma suka bi sahunsa,iya ƙauna baffa ya nunawa dan birni kamar yadda kuka ji a cikin labarin mus ab da ya rubuta a cikin jota, wannan shine abinda ya faru kafin zuwan mus ab.

Bayan tafiyar mus ab da kwanaki baffa wuro ya sake dawowa da baffa Yusuf magana akan zuwan likita, a lokacin baffa Yusuf ya amince, wanda hakan ba karamin murna wuro yayi ba, baƙon likita ya shigo cikin garin, an kuma ga ya shiga dakin baffa da kayan aiki da wata bakar akwatu,babu wanda yasan me ya faru da baffa sai wayar gari aka yi ya ce ga garinku nan, wannan shine dalilin da yasa baffa wuro ya samu damar kuma jonewa da mutanensa Garba Jamil da kuma Kabir,daga nan suka zaba masa inda zasu ci gaba da rayuwa domin ya dinga yi musu gadin aminatu da innawuro,dan sun sha alwashin sai sun yi ruf da ciki akan dukiyar da baffa yake ta wahalar da su akanta dan duk abinda suke yi suna yi ne saboda dukiyar Yusuf din ga kuma irin bakar azabar da suke sha a duk lokacin da suka taba wani abu na Yusuf din,dan ko lokacin da suka tafi da matarsa mahaifiyar aminatu sun gane kurensu, lokacin da suka yi aiki suka cire zuciyarta kuwa anan suka gane cewa shayi ruwa ne dan da Allah yasosu da shirya da alokacin zasu shiryu dan ko bacci sai da ya ya gare su,amma dake sun yi nisa bada jin kira suna samun kansu suka dora fiye da yadda suke a baya, wannan dalilinne yasa suka bar aminatu a raye saboda suna son dukiyar ubanta kuma dole sai wanda aka bawa dukiyar ya dawo ga Aminatun ne zasu samu abinda suke so,daga nan zasu cire zuciyar inna wuro da tuni suka yi cinikin ta da kuma ta aminatun bayan sun samu yadda suke so wanda aka bawa amanar dukiyarta ya bayyana, wannan shine lissafinsu sai dai kuma hakan bata samu ba,dan lissafinsu ya fara kwancewa ne tun bayan da suka dauko aminatu suka dawo da ita kusa da su.

Su kansu ba su isa su ce ga abinda yake cikin rayuwar Aminatu ba,saboda sun sha wahala akanta da mahaifinta da suka zama sanadin mutuwarsa dan wannan likitan da suka turo likitansu ne yayi aiki ya cire zuciyar baffa Yusuf ya kawo musu,sun sha wahala ta jiki da zuciya amma duk da haka basu karaya ba suka ci gaba da gadinta amatsayin kadararsu,amma su kansu sun shaida akwai wani abu a acikin rayuwar Yusuf da iyalansa ko kuma dai su din yan baiwane.

******

Kuka sosai Aminatu take yi, mus ab kuwa tunda ya dauke kansa daga kan rubutun ya maida kansa jikin kujerar da yake jikinta tare da rufe su yana jin sautin kukan aminatu da yake diga a ransa kamar ana diga dalma...

Jin kukannata yawa yake kuma yi yasa shi dora hannunsa akan ta yana yamutsa gashin kanta me santsi,kafin cikin taushin murya ya ce "sorry nurr"lafazin da yayi amfani da shi wajen bata kalma daya ta rarrashi shine ya ja hankalinta har kukanta ya tsaya ɗif,saidai jan ajiyar zuciya da take yi,sai da ta dauki minti ɗaya kafin cikin Muryar ta da ta yi kasa sosai ta ce"daddy nima su suka kashe iyayena kuma da sa hannun amintaccen mahaifina mutumin da bashi da na biyunsa,baffa wuro ya ci amanar baffa na da baffa zai dawo duniya yau da ban san wane irin tashin hankali zai shiga na jin cewa baffa wuro ne sanadi tare da shi aka kashe rayukan mutane da basu ji ba basu gani ba, akan kuɗi abin banza da zaka mutu kabarsu,shi yasa nai bana don asibitinsu ashe abinda ake aikatawa me karshen muni ne"kukane ya kuma kwace mata saboda tuna baffanta da ta ke yi dan tafi sha kuwa dashi fiye da innarta kuma lokacin da ta mutu mata da wayo shi kuwa baffa ko yanzu tana tuno lokacin mutuwarsa.

Dago kanta yayi a hankali yana mai haɗe bakinsa da nata, ai ko take ta hadiye kukanta,yadda yake sumbatar bakinta da zafi ,zafi yasa ta tuna halin da take ciki, tsoro ne ya kamata, hakan yasa ta shiga kokarin kwacewa, sai dai ina yan mazan Nana sun yi ram da Nijar innawuro,dole ta hakura sai dai kanfanin hawaye da take yi tana jin ciwo a duk inda ya kai hannunsa musamman kirjinta da har yanzu bata ji ya dawo daidai ba,a hankali ya zame rigar da ya daka mata ta yi kasa, rike da ta yi sosai tana juya kanta hawaye duk ya bata mata fuska saboda babu damar kwallawa dan ya rike bakin kam kamar ba zai rabu da shi ba,ganin ba sarki sai Allah yasa ta ɗan sassauta tare da bude bakinta sosai tana taya sa cikin enjoying,Wanda hakan yasa shi sakin jikinsa,ita kuma hakan ya bata damar kwacewa ,da gudu ta mike tana yi masa Gwalo,wai ita fa tayi masa wayo,lumshe idanunsa yayi tare da yin balance a wajen dan a hakika nin gaskiya aminatu ta yi masa dabaibayi ta sarkakfe shi tare da mugun kullin da fitarsa daga ciki abu ne da ba zai taba yiwuwa ba.

A hankali cikin rashin kuzarin da ta haifar masa ya daga hannunsa yana yi mata alama da ta dawo gareshi,makale kafada ta yi tana kuma turo masa harshe har da kada masa dararan idanunta masu maiko......

Zahra✍️
[5/13, 6:32 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page56``*

Numfashi yaja me nauyi tare da shafa kansa,daya daga cikin wayoyinsa ne ta yi haske alamun kira ya shigo,zubawa wayar ido yayi saboda nomber da ya gani tana yawo akan screen dinta,bako wace nomber ba ce sai ta abby,ji yayi hannunsa yayi nauyi ya kasa ko motsa shi bare ya daga wayar,dan shi yanzu ko Muryar abby baya son ji,ji yayi kawai Aminatu ta daga kiran, ba tare kuma da anjira cewarsa ba, aka fara tun tsira dariya, dariya irin ta naci dubu se ceto, saida yayi me isarsa sannan ya fara magana da cewa,"mus ab ina fata dai ka ga ne babanka ne a kan layi ko?bai jira amsarsa ba ya ci gaba da cewa,"i zuwa wannan lokaci na san wannan tsinanniyar yarinyar da take tare da kai ta bude maka abinda yake cikin littafin nan ka gani,dan haka ba bukatar na kuma yi maka dogon bayani,yanzu dai kasan ko ni waye a gare ka da matsayina da komai nawa,dan haka zan tafi kai tsaye zuwa kan dalilin kiranka"wayar ya kai saitin bakin Nana sannan ya daddage ya tsinka mata marin da yasa ta yin baya tare da sakin kukan dole,dan sam bata yi niyar yin magana ba saboda kar ta daga musu hankali musamman aminatu, aiko tunaninta yayi daidai dan Muryar aminatu ta ji yo tana cewa "daddy kukan Nana ne fa wannan,wayyo Nana kina ina me ya same ki ke da waye"?cikin dauriya Nana ta ce"boddo ki kwantar da hankalinki ina lafiya baki ji Ni da Abby ku ba ne?"

"Cikin tsawa Abby ya katseta da cewa "ƙarya kike baki isa ki kwantar musu da hankali da sunan kina lafiya ba,kai bari ma na fito na bayyana maka abinda nake nufi,na dauke uwarka yanzu haka tana hannuna kuma azaba zan ta gana mata, kullum da kalar wuyar da zan bata,dan haka idan har kana son mahaifiyarka a raye to duk wani abu da kasan shaida ne tun daga kan mutanen da ka haɗa har zuwa kan wasu takardu da camarory duk ka haɗa ka bani, sannan da uwa uba littafin sirrina,dan wannan da Kabir yasa aka dauko ba shi ba ne,kai Ni fa duk yadda kuke zatona na wuce saninku wallahi,shegiyar yarinya ba ke kina takama da aljana ba,to nima aljanin kaina ne,ai tun wancan na farkon da kika sa aljanarki ta ajiye min a daki to tun daga kansa na gane irin naku na aljanu,dan haka ku bani ko mai nima na baku uwarku, kuma duk abinda na duba naga fake ne to wallahi sai na kashe ta idan yaso nima a kashe Ni"daga haka ya ajiye wayar yana dariyar mugunta dan ya tabbatar da cewa tarkonsa ya danu daidai da yadda ya saitashi.
Chapter 43 · 0% Book details