Sashe 34
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sannu sannu kwanaki na shuɗewa su zama watanni watanni na shuɗewa su zama shekaru ,gashi yau matasan samarin har sun cika shekara sha biyar biyar, ko wanne kuma burinsa bai sauya ba,sai abinda yayi gaba,ta bangaren sule yanayin rayuwarsa na rashin girman kai da neman hakan da rashin raina samu duk kankantarsa ya fara kaisa matakin nasara,bai damu da irin hantarar da su Jamil suke masa da gori ba dan duk abinda ya samu sai ya basu nasu kason kuma su sa hannu su karbe ba godiya sai dai su bishi da harara da gorin rashin iyaye da takaicin almajiranci duk da cewa su din ma talakawa ne bambancin su dashi shine su suna gaban iyayensu ne,kamar yau ne sule ya dawo daga kasuwa wajen da yake yan buga bugarsa ya samu, ya kuma samo me albarka har yayi musu guzurin hatsi, Jamil na gefe da wayarsa da ya samu ta hanyar kwace yana faman latsata,duk albarkar da iyayensa suke sakawa sule yana ji sai dai bai tanka ba, da abin ya ishesa ne ya mike yana buga uban tsaki tare da fucwa daga gidan,baby abinda zyciyartsa take aiyanawa sai kudi karfi mulki duk inda ya kamata ya samesu sai ya samesu, acewarsa karamin samu ma an martaba mutum bare kuma akaiga babban samu.
A kofar gida ya tarar da Garba da Kabir suna lido,zama yayi yana huci wanda hakan yasa suka bar abinda suke suka fuskanceshi tare da tambayarsa abinda yake damunsa,a.maimakon ya basu amsa sai shine ya juya musu da tambay,abokaina kuma son muyi kudi cikin kankanin lokaci?"gaba daya suka daga masa kai kamar wasu kaɗangaru,hannunsa ya dora akasa su kuma suka dora nasu a bayan nasa,daga haka ya ce da su ,"daga yanzu duk wani abu da muka san zai kawo mana kudi kawai zamu yi shi babu tunanin abinda zai je ya zo"dariya suka sa tare da daga hannun su sama da yake a hade.......
Zahra..✍🏽
8064537048
Opay
Fatima yusha'u Adam
500 only
[5/6, 11:21 AM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page50``*
Tun daga wannan lokaci su jamilu suka sauya dama can suna da dabi arsu ta kwacen waya kudi da yan abubuwan da ba a rasa ba,amma a wannan lokacin da zuciyarsu ta kuma tsunduma akan lallai sai sunyi kudi ta ko wane hali sai abin nasu ya fara yawa,har ta kai da sun fara haurawa gidajen mutane,abun nasu dai babu imani ko kadan,ana cikin haka zance ya fara baza anguwa, har magana ta dawo kunnen mahaifin Jamil,a lokacin Garba da Kabir su iyayensu maza sun rasu a hannun iyayensu mata suke,su kuma tun da ya zamana zasu nemo musu suci shike nan suka daina fada musu gaskiya sai albarka da take biyowa baya,shi ko mahaifin Jamil faduwa yayi tun da yaji labarin, da kyar aka samu kansa, ko da ya tashi nan ma gorin mutane ya sashi a gaba wanda dole yasa ya fara hada kan iyalansa dan su bar garin DAMATURU.
Alokacin shi kuma SULAIMAN ya jima da komawa garinsu Gombe ,inda ya tarar da baffansa ba lafiya anan ya shiga jinyarsa da yi masa hidima ta kudi, har Allah ya karbi abinsa,SULAIMAN bai karaya da rashin dangi ba sai ya sawa zuciyarsa hakuri ya kuma tabbatarwa da mutane cewa babu Maraya sai rago,dan cikin ikon Allah neman na kai da jajaircewa ya fara kai SULAIMAN wasu matakan nasara inda ya tashi gonarsa ta gado ya habbakata tare da yi mata yan uwa,a gefe daya kuma yana ci gaba da neman ilminsa na boko da na addini,
Kai tsaye malam ilya maihaifin Jamil Gombe ya taho,ƙafarsa kafar Jamil dan bai yarda ya barshi a wajen abokansa da yake tunanin su suke lalata Jamil din ba,kasancewar SULAIMAN ya bashi cikakken kwatancen kauyensu da kuma gidansu yasa basu sha wahalar ganewa ba,SULAIMAN yayi farin ciki iya farin ciki da ganin iyayensa na riko mutanen da ba zai taba mantawa da su ba,a nan fa ciwon hassada ya fara motsawa Jamil saboda yadda yaga Jamil fes baya cikin wata damuwa komai nasa cikin rufin asiri da wadatar zuci,ga kyau da cikar kamala irin ta matasan da suka san kansu, dakin da yake ciki ya bawa Jamil suka ci gaba da zama a tare, yayin da ya fara son jawo Jamil din a jiki yana nuna masa wasu kananun harkokinnasa da kawai ya cire masa tunanin wancan banzar dabi ar da ta sasu suka baro garinsu.
To abin dai na Jamil ya yi sauki dan sosai ya kwantar da kai ya fara cin arzikin SULAIMAN duk da cewa ta ciki na ciki, to amma yanzu babu yadda zai yi saboda albarkacin sulen yake ci,duk da cewa a ransa yana jin cewa kome sule ya zama iyayensa ne suka zama sila shi yasa yake ji a ransa kamar duk abinda sule ya samu shima yana da hakki a cikinsa.
Sannu sannu har gashi sun zama cikakkun samari, arzikin sule shine abinda ya fara sanyawa zuciyar Jamil ciwo,daga nan burinsa na baya ya tashi daga baccin da yayi,hakan yasa rana tsaka ya tashi ta kanas ya tafi har DAMATURU ba tare da sanin kowa ba ya janyo abokansa,a lokacin mahaifiyar Garba ta rasu,ko da suka zo sai suka kwantar da kai suka nunawa malam ilya cewa suma fa tuni sun shiryu har da neman gafararsa,hakan yasa suka ji dadi, sule shi ya rungumesu ya ci gaba da tallafawa rayuwarsu har da ta iyayensu, dan shima Kabir har mahaifiyarsa sule yasa shi ya dauko daga damaturu, sun hadu sun zama family daya jajirtaccen cikinsu shine sule,duk wani abu da za a ci a sha a hannun dan sule ne,yadda iyayen su su Jamil suke nunawa sule so yasa suka kuma tsanarsa a ransa,a cikin haka ne suke ya kammala dgree dinsa kasancewarsa me sa a yasa bai sha wahalar samun aiki ba,damar da ya samu yasa shi wargaje gidansu ya zama na zamani, sam. Aransa bai ji yana sin komawa birni ba dan acewarsa mutanen garinsu yake gani yake jin dadi a matsayinsa na maraya wanda bai da kowa a duniya.
A yawan shige shigensu ne Jamil ya hadu da wani mutum me suna don, don karen masu kudi ne duk wani me ji da arziki yasanshi,tun da Jamil ya kula da irin kudaden da donnyake kashewa ahike nan ya zama cingim dinsa har dai daga karshe ya nuna masa hanyar da yake bi yake samun kuɗi,Jamil bai wani girgiza ba ya nuna masa ba matsala yana da abokan da zasu dinga yin aikin tare,ko da ya samu abokansa da maganar duka babu wanda yayi musu, duk da dai suna tunanin ta inda zasu fara ciro koda ko zuciyar mutum suna kaiwa iyayen gidan da don ya haɗa su da su to amma dake sun sawa zuciyarsu dakiya akan cewa zasu nemi kudi ta ko wace hanya sai basu ga wahalar abin ba,cikin kankanin lokaci suka fara wasa da kudade, daga nan likkafa ta ci gaba su ka fara kwacen gidaje da gonayen mutane a boye,kai tsaye suke sace mutum su kaishi tsakiyar daji su bashi biro yasa hannu a cikin takardun gonarsa bayan sun yi masa barazana da kisa,amma memakin idan mutum ya sa hannu su barsa sai kawai susa a farke ka a dauko musu zuciyarsa da kodarsa daga nan su tsallekeka su Barka cikin jini a mace.
A cikin sati daya kawai sai a tsinci gawa sama da biyar, gaba daya kauyen ya rikice har wasu sun fara yin balaguro daga kauyen,take malam ilya ya fara dora zarginsa a kan yaransu, wanda sanadiyar ganowar ya rasa ransa ta hanyar bugawar ZUCIYA,
Nana Asma'u kyakkyawar bafulatana ce me hankali da ilmin addini, sun dade suna soyayya da sule ba tare da kowa ya sani ba,sule yana gab da bayyana kansa wajen iyayen nana, shi kuma jamil ya hadu da Nana lokaci daya.ya nuna mata yana sonta amma sai ta nuna masa tana da wanda take so,bai yi niyar rabuwa da ita ba,ya ci gaba da bibiyarta ba tare da yasan wanda take so din ba,ana cikin haka kuma SULAIMAN ya samu karin girma wajen aikinsa tare da gida da mota,a bangare daya kuma harkar gunakinsa suna habbaka tare da companin taki da ya bude, hakan yasa kai tsaye ya tunkari mahaifin Nana da maganar son auren Nana da yake,nagartar suke da sanin halayensa na gari da kuma nutswarsa yasa a take a wajen mahaifin Nana ya bashi aurenta tare da sanar dashi juma a me zuwa za a daura auren,sun yi farin ciki da murna hatta da Anne sai da ta raba goron murna, alokacin kuma Jamil ba sanan sun yi tafiya.
Jamil da Kabir da kuma Garba, sun yi tafiya me tsayi domin haduwa da wani iblishin matsafi, wanda wani abokin harkallarsu ya haɗa su dashi, acewarsa duk mutanen da suka hada hannu da sunduƙi to basu da sauran takaici domin duk abinda suka sa a gaba sai sun cimmasa, tsarin tsafin sunduƙi ya banbanta dana sauran matsafa saboda shi tsafinsa a littafi yake,wani littafi ne wanda idan zai baka shi sai ya rubutu kundinka na duk abinda ka aikata a baya da wanda zaka yi a gaba,da kuma sunaye da tarihin duk wanda suka taba cuta ko su ka zauna tare dashi, daga haka zai tsaface littafin ya baka shi ka je ka ajiye shi a waje na musamman kana bauta masa, sai dai sharadin sa ba me sauki ba ne,dan duk ranar da wani ya samu nasarar daukarsa ko budesa har ta kaisa ga karanta shafin da yake cikin littafin to tabbas rayuwar me littafin da shi kansa tana cikin matsala, tunda sunduki yake tsafinsa har izuwa lokacinnsu jamil ba a taba samun akasi ga sauran mabiyansa ba,shi yasa yake jin kamar tsafinsane yayi karfin da har ba a taba samun wanda ya taba littafin ko ya budeshi ba,tun daga wannan lokacin suka karbo littafin suka yi masa waje a dankareren gidan da suka siya a cikin babban birnin Gombe,