← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 57

Sashe 36

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu yarda sun kai sule gida ba sai bayan sallar asuba sannan suka taho dashi, cikin yanayin tashin hankali da alhini,Abby ne ya ce a barshi da kansa zai fadawa Nana halin da ake ciki,babu wanda ya Musa masa, dan haka kai tsaye dakin Nana ya nufa inda ya tarar da ita saman dadduma tana ta shararo addu'a wa mijinta,kallonsa take cike da mamaki da kuma takaici na yadda ya shigo har dakin mijinta kai tsaye,Abby Sarai ya fahimci mugun kallon da Nana take masa amma sai ya basar tare da, sanar da ita abinda ya kawo shi kai tsaye babu lallashi babu kwana kwana ko kame kame,wani irin duhu ne ya mamaye ganin Nana,wanda a take annan ta zube babu alamun numfashi,cikin sauri Abby ya zaro tsumman tsafin da sunduƙi ya bashi ya sanya mata akan fuskarta,daga haka ya daga karkashin gadonta ya saka wata karamar kwalba ya mayar ya rufe,dariya ya sanya yana cewa shike nan na gama da babinki har abada ke da kara tuna wani sule a matsayin mijinki na baya a ranar da kika kammala takarbarki a ranar zaki zama matar Jamil burina ya cika saura kuma na bi na tattara kadarorin mijinki da duk wani abu da ya mallaka ya zama nawa"dag haka ya bar dakin yana sauya yanayinsa har da matsar kwalla,karo suka ci da mus ab da yake kokarin shiga dakin Nana,cikin sauri Abby ya kama hannunsa tare da shafa masa wani turare a saman kansa, cikin sauri mus ab ya rufe idanunsa saboda yadda warin turaren ya bugi kansa har ya shiga juyawa kamar wata fanka,a lokaci daya kuma ya bude idon, tozalin da ya fara yi da Abby shine yasa har rana irin ta yau yake kallon Abby a matsayin babansa sule kamar yadda nana take yi masa kallon mijinta sule.

Kwana bakwai aka share makoki daga nan Abby ya nufi inda yake da tabbacin cewa kadarorin sule suna nan,sai dai me wayam yaga gurin ko biro bai samu ba bare wata takarda da zata nuna masa shaidar kadara,sosai hankalinsa ya tashi, to shin ina sule ya kai arzikinsa ko dai sun kare garin yiwa talakawa hidima,ya jima cikin zuzzurfan tunani,kafin ya bar wajen yana cewa in dai matarka ka bawa ko yaronka ai babu wata matsala tunda Dukansu a karkashina suke",wasa wasa fa abu yana nema zama gaske dan duk inda suke zaton sule ya wuce nan,kuma sun tabbatar da cewa sule boye kadarorinsa yayi,to a ina kuma yaushe?"kwafa su kayi tare da samun kwarin gwiwar cewa matar da dan duka yanzu suna karkashin ikon mus ab.

******

Suna zuwa nan a karatun suka dakata tare da dago kansu suna kallon juna, fuskar aminatu jiƙe da hawaye,mus'ab kuwa makwallatonsa zaku gani kawai ku gane yanayin da yake ciki,idan tunaninsu yayi daidai kenan Abby ba shine mahaifinsa ba?"aminatu ta ce ta kuma maida hankalinta kan littafin inda ta dawo kan shafin da hoton sule yake,zuba masa ido ta yi sai kuma ta yi saurin kallon mus ab tana cewa'daddy wallahi bai mutu ba shine yake kirana nazo na taimaka masa yana nan a raye shine babanka ba wannan azzalumin ba"ta karasa fada tana fadawa jikinsa tare da kankamesa kamar za a kwace mata shi,shi kansa mus ab jikinsa ne ya yi murus idanun babu abinda suke sai yaji tamkar an zuba barkono a cikinsu,zuciyarsa wani irin gudu take tana bugawa da ƙarfi.

""""Zunbur Nana ta farka da ga dan baccin da ya fara saceta,ji ta yi tamkar ta tashi daga wani mummunan mafarki,tashi tsaye ta yi tana gyara daurin kallabinta da sauri ta dafe kanta da yake matukar sara mata,kafin cikin wani irin sauti me karfi ta fara ambaton sunan sule, dakin ta fara zagayawa cikin fitar hayyaci,ko mai ya dawo mata sabo amma dai tana da tabbacin mafarki ne ba gaske ba,da gudu ta fito daga bangarenta ta nufi dakin Anne tana shiga ta rike Anne tana cewa,"Anne da gaske sule na ya mutu, da gaske yayi hadari ya mutu ko gane fuskarsa ba ayi?"cikin tsananin mamaki Anne take duban nana, ganin dai nanan bata hayyacinta yasa ta rikota ta zaunar da ita a kusa da ita tana cewa,"haba nana me zai sa ki birkice akan mutuwar sule yanzu bayan sule tuni ya manta da zama turbaya saboda shekarun da a ka yi da mutuwarsa,tun fa mus ab yana shekara biyu a duniya sule ya mutu,to me zai sa ki dawo da hannun a gigi baya a lokacin da ake kan jimami ma kika hakura kika dangana dake da danki bare kuma yanzu da aka dau kusan shekara talatin da biyar"tunda Anne ta fara magana Nana ta zuba wa bakinta ido, a take kuma komai ya dinga dawo mata tun daga kan abinda Jamil ya shaka mata har zuwa aurenta da ya sake yi da rayuwar da suka yi da ya'yan da suka haifa dashi,to me yasa a lokacin ta ke kallon abby a matsayin sule?tabbas akwai wani abu da ba daidai ba, tabbas akwai wani biyayyan al'amari game da kome da ya shafi rayuwarsu ita da danta, sannan mutuwar mijinta ma lallai akwai sa hannu a ciki,kallon da Anne take mata ne yasa ta miƙewa cikin sanyin jiki tare da cewa,ki yi hakuri Anne wani mafarki nayi mara daɗi shi yasa kika ga duk na birkice"daga haka ta fice daga dakin tana share hawayen da suka kasa tsayawa.

Ganin kukan aminatu yawa yake kuma yi dan har ya fara saukar mata zazzaɓi yasa mus ab ya nuna jarumtar nan tasa da dakiya na kokarin ɓoye firgicinsa ko tashin hankalinsa,ya juyo da ita tana fuskantarsa,hade fuskar sa yayi da tata, sannan cikin muryarsa da a yau ta bayyana halin da yake ciki ya ce"princess me yasa kike kuka haka da yawa?"bata san sanda ta antaya masa wata irin harara tamkar idanunta zasu fado ba, kana ta tura karamin bakinta tare da kokarin kawar da fuskarta daga kallonsa,amma sai ya sanya hannunsa ya rike fuskar yadda bata isa juyawa ba,a hankali ya sanya harshensa ya ɗan lashi labbanta da ya ga alamun bushewa a tare da su,lumshe idanunta ta yi tana jin wani irin yam a jikinta kafin ta yi saurin shigewa cikin jikinsa ta naɗe sai kace wata yar mage,hannunta ta dora a kan fuskarsa tana shafawa a hankali,rike hannun yayi yana cewa"ke eee so kike karatun ya tashi daga nan wata matsalar da zata hanamu karasawa ta bullo"?kallonsa ta yi idanunta suna wani shigewa ciki kamar wadda ta sha abin maye,wanda hakan ya kuma birkita lissafin mus ab,jikinsa har wani tsuma yake wajen kokarinsa na haɗe bakinsa da nata,sai dai bata bashi damar hakan ba saboda sautin zamewa da tayi daga jikinsa tana wani rangwadar da kai tare da cunno jajayen lips ɗinta gaba tana wani kif_ƙifta ido cikin kallonsa,sumarsa ya ɗan shafa yana lumshe idanunsa alokaci daya kuma yana cewa,kin tada wutar da kasheta cikin sauki ba mai yuwuwa ba ne,kuma kin gudu?"shafa cikinta ya yi ba tare da ta tankawa maganarsa ba ta ce"daddy yunwa nake ji abinci zanci,amma bana so ka.sake fita ka barni Ni daya ba zan iya ba kashe Ni za suyi, Dan kaine baka sani ba yau a dakin nan yaƙin duniya na farko a ka yi a ciki?"yanayin da fuskarsa ta nuna kadai zaka fahimci cewa murmushin ciki yayi wanda bai bayyana akan fuskarsa ba.

Matsawa ta yi da dashi tare da sanya hannunta akan fuskarsa ta ce, daddy me yasa baka son yin dariya ko murmushi nasan zai yi maka kyau tunda kai me kyau ne,WLh daddy Ina son murmushinka Ina son muryarka bare kuma ƙamshinka da yake sani cikin wani yanayi, dan Allah daddy ka fada min meye ne abinda nake ji a raina game da kai,uhm ji nake fa kamar zan mutu idan....sai kuma ta yi shuru tare da kwanciya a kan kafafunsa, sannan ta janyo littafin zata bude,yayi saurin rkiewa ya dakatar da ita,kana cikin rarraba kalmar da zai fada ya ce"me zaki fada kika fasa?"maimakon ta bashi amsa sai kawai ta yi wani irin juyi a jikinsa take mus ab ya ɗauke numfashi saboda juyin da aminatu ta yi sai da ya tabo masa sirrinsa,ita ko bata san hakin da ta jefa ɗan gidan nana ba, dan haka cikin kwanciyar hankali ta bude shafun gaba ta dora daga inda suka tsaya,shima din zubawa shafin da ta bude idanun yayi.

***********
Tunda abby ya juyar da hankalin Nana da mus ab,shike nan ya ci gaba da cin kare masa babu babbaka harkoki kuwa sabbi aka buɗe, ko da yaushe da irin sabon kasuwancin da zai bullo musu,duk da irin manyan kudaden da suke samu amma hakan bai wadatar da su ba,dan sun ce har yanzu burin su na yin kafada kafada da manya kuma kusoshin gwamnati da masu mulki bai cika ba,dan haka suka kara bude kofar zaluncinsu,lokaci daya suka.gina wasu irin manyan gidaje masu kyawun tashin hankali,a cikin anguwar da ta kasance ta talakawa masu karamin ƙarfi,wanda sun yi haka ne da manufar su ta kara samun abinda yake kawo musu Kudi,cikin boyayyiyar fuskarsu su ka fara janyo talakawan da suke kewaye da su jikinsu,inda suka samu galaba suke yi musu dauki dai-dai.

A haka har aka ja shekaru Nana ta samu karuwar yara har uku bayan mus' ab,isma shine me bin mus' ab,sai suleman wanda aka sanya masa sunan marigayi sule, sai suhaima autarsu,matar Kabir ma ta kuma haifar da namiji,tunda ga sannan kuma babu wadda ta kuma yin ko batan wata,zubaida dama tuni ta cire rai da haihuwa shima Garba be sa abin akansa ba,a haka rayuwa ta dinga tafiya da abubuwa masu tarin yawa.

Duka yaransu su suka zaba musu abinda suke son su karanta, dama ita zahida burinsu da ya shi yasa basu sha wahala akanta ba,akan musu ab ne suka dan sha wuya kafin ya hakura ya bar burinsa ya karbi nasu ya je ya karanci kasuwanci.

Har zuwa yau din nan su Abby ba su daina tunani da binciken neman inda suke ya kai kadarorinsa ya biye ba, kullum kansu da da kullewa yake akan dukiyar sule,sai dai sun kasa karaya da hakan .
Chapter 36 · 0% Book details