← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 57

Sashe 6

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamar ance aminatu ta farka,tana buɗe idanunta ta yi zunbur ta mike tare da fitowa daga dakinta,kai tsaye dakin Anne ta nufa cikin sanda,tana zuwa bakin kofar kuwa ta ji surutan Anne kamar wadda bata cikin hayyacinta,dariya aminatu ta yi tare da sa key din ta bude kofar a hankali wanda motsin kofar yayi daidai da wani irin tsalle da beran yayi kamar an danna remote yayi kan Anne,sai ga Anne ta jika jikinta da fitsari kafin ta ci gaba da Jan gwiwowinta a ƙasan dakin tana rarrafe kamar yarinya, bakinta kuwa tun tana iya karanta karatunsu irin na tsaffin da suka zauna a cikin kauye da duhun jahilci har ta zo tana kasa bude idanunta da ko gani sosai ba sa yi,jin motsin kofar ne ya kuma razana ta ta saki wani mugun ihu tare da sakin ragowar abinda take da tabbacin cewa zawo ne.

Isma da yake daf da shigowa falon ne ya ƙara sauri wajen faɗowa falon tare da nufar hanyar dakin Anne, sai kuma mus ab da ihun ya samesa lokacin yana sujjadar karshe ta nafifilunsa, dan haka shima kai tsaye kasan yayo cikin nutsuwarsa da kamewar da suke kuma bayyanar da kwarjininsa, itama aminatu tuni ta karasa fadawa dakin tare da kiran sunan Anne tana yi tana toshe hancinta tare da yatsine fuska kamar zata yi amai,isma yana shigowa kan aminatu yayi cike da fusata yana cewa dan ubanki me kika yi mata?"ya.fada yana ƙoƙarin kai hannunsa jikin aminatu zai bigeta,caraf ya ji an riƙe hannun nasa tare da saukar da shi a hankali,da sauri aminatu ta koma bayan mus' ab Wanda hakan ne ya bawa isma damar fahimtar waye ya dakatar dashi daga samun kyakkyawar damar cin uban aminatu,"haba hamma mus' ab da Ka barni na faffalla mata mari dan na tabbatar maka da cewa ita ce ta yiwa anne wani abun tunda iya su ka daine a wannan sashen" ko kallonsa mus' ab bai yi ba ya nufi wajen anne da take ta son tashi amma ta kasa ya tsuguna gabanta duk da warin da ya cika masa hanci amma hakan baisa ya kasa nutsuwa wajen yi mata magana ba,"me ya faru Anne?"cikin kuka anne ta ce wallahi babban mutum beraye ne a dakin nan fal ganin idona kai ba ma iya su ba ina tunanin har da aljanu yau sun yi nasarar shigowa gidan nan dan wallahi ni naga abinda na gani"isma ne ya shiga duba dakin yana cewa "to uban me ya kawo bera gidan nan wallahi sai dai in shigo da su a kayi dan kuwa babu abinda zai shigo da bera daki"aminatu da ke rabe daga can inda koda isma ya zaburo zata iya buya wajen mus ab,ta ce,"shi bera ina ruwansa duk in da ya gadama ai shiga zai yi koda kuwa gidan shugaban kasa ne"a fusa ce isma ya juyo zai antaya mata ashariya amma sai yayi wani ɗif kamar an dauke nefa,jin yadda yayi shurun kamar ba da shiri ba yasa mus ab kallonsa sai kuma a hankali ya maida idanunsa kan abinda isma din ya zubawa ido baki sake tamkar wani dolo,da karfi mus ab ya rufe idanunsa yana mai kokuwar hadiye katon abinda ya tsaye masa a makoshi,lokaci ɗaya idanunsa suka wani birkice,cike da zafin nama ya mike daga durkuson da yayi a gaban Anne ya nufi aminatu da hankalinta sam ba ya kansu,wata irin rumfa mus' ab yayiwa aminatu ta yadda ko da ƙafafunta ba a hangowa, bakinsa kuwa ya kasa furta komai bare ya samu damar bawa isma umarnin fita ko dauke idanunsa daga kan abinda yake halalinsa mallakinsa duniya da lahira.

Wannan abin da mus' ab yayi shi ya dawo da isma hankalinsa sai dai kuma zuciyarsa cike take da kwadayin sake maimaita irin farin ganin da idanunsa su kayi masa,tabbas kira ko ya ce surar aminatu ta tafi dashi, zai iya cewa duk irin yawa ce yawacensa a fadin duniya da mu amalarsa da mata bai taba ganin sura makamanciyar ta Aminatu ba bare wadda ta kaita,ashe ƙadara ce ko ya ce Gara a lulluɓe cikin huhun goro a gidansu bai sani ba,kai anya kuwa ya taba kallon aminatu acikin hayyacinsa kuwa in ba yau ba? tabbas bai taba ba dan da ya taba da tuni ya gano sirrin da yake boye,to shi kuma wannan da yayi baka bakan ya hanashi ganinta me hakan yake nufi, duba fa rungumeta yayi da sunan ya kareta, to idan har shi bai halatta yaga aminatu a wannan yanayin ba shima mus' ab din ai Bai kamata ba dan haka ba zai bar dakin nan ba har sai aminatu ta fita dan hakanne kadai zai bashi damar ganin sauran abinda bai gani ba.

Kukan Anne da tsallen da ta yi ta fada kan isma shi ya dawo dashi hayyacinsa,da sauri isma ya angije Anne Yana cewa haba Anne ya za a yi ki taba Ni da wannan zawon a jikinki gaskiya Ni ba ki kyauta min ba,akan bera kawai duk kinzo kin ɗagawa mutane hankali"dan uwanka Ni ka ture to ka tabbata da cewa yau a dakinka zan kwana dan muddin beran nan suna cikin dakin nan to ba Ni babu shi,shi kuma wancan tabararran me yake yiwa yar mutane?"ta faɗa tana jefa idanunta kan mus ab da har yanzu ya kasa motsawa daga rumfar da yayiwa aminatu. ita kuwa aminatu a tunaninta kare ta yayi daga dukan da isma yake shirin kawo mata shi yasa ta yi luf tana zare idon rashin gaskiya ...

Fyadam✍🏾
[4/15, 3:25 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page34``*

Isma dai ba dan yaso ba sai dan warin zawon Anne da yake shirin kumbura masa ciki,yasa ya tattagi annen ya kaita bayi ya zubar yana toshe hancinsa,da wannan damar mus' ab yayi amfani ya janye aminatu daga dakin, duk da yadda aminatu taso ganin karshen wasan sai dai kuma ta ji dadi da ba a yi batun cire beran ba ko ba komai Film din bai kare ba,isma kuwa duk saurin da yake dan ya fito ya samu aminatu hakan bai samu ba,dan dole ya fita daga dakin yana mugun saka a zuciyarsa,ba tare da ya nemo beran dakin Anne ya fitar dasu ba,Anne kuwa koda ta gama gyara jikinta hankali kwance ta fito dan a tunaninta tuni isma ya dauke berayen da take da tabbacin shigo da su akayi, hakan yasa ta sake shirin bacci ta haye gadon tana la antar wanda ya kawo mata bera dakinta.

Kai tsaye mus' ab bangarensa ya wuce da aminatu wadda ke ta zumbure baki tana gunguni akan me zai kaita dakinsa ya barta ta koma dakinsu mana kalan kawai duk ya lallasheta mutum sai kace maye, yana jin duk abinda take fada amma bai kulata ba kuma bai saketa ba har sai da suka dangana ga bakinsa,iska ta shaka tare da yin wani dan karamin juyi wanda hakan yayi sanadiyar dagewar yar rigar bacci me zubin umbrella sama tamkar ana wulwula umbrella shafaffen cikinta ne ya bayyana da dan ramin cibinta, rufe idanunsa yayi yana kokarin saita numfashinsa da ya haɗe guri daya da wani irin yanayi tare da zafin isma da ita kanta aminatu da har yanzu bata yi hankali ba,tsawa ya daka mata wanda hakan yasa lokaci ɗaya ta nutsu tana rarraba manyan idanunta da har sun fara cika da ƙwallar tsoro dan bata taba cin karo da tsawar mus ab ba bare ta san ya kalar kwarjininta yake, sosai shakkarsa ya kuma nunkuwa a ranta dan haka ta samu guri ta maƙure jikinta babu abinda yake sai rawa tamkar wadda aka shekawa ruwan sanyi lokacin hunturu.

Ganin yadda ta tsorata sosai ne yasa shi dan sassauta fuskarsa duk da cewa ba wai ya saka mata murmushi ba ne . kana ya tako zuwa gabanta ya tsaya tare da zuba mata ido,yana kallon yadda shigar jikinta ta fidda wani irin sirrin kyawunta. ta bangare guda kuma idanun isma ne suke shawagi a jikin aminatu suke gilma masa,take fuskarsa ta kuma murtukewa makwallonta sakawai da aminatu ta kalla sai da ta kusa shiɗewa saboda yadda taga suna wani irin sama da kasa cikin karfin gudu,wanda ta nan ne kawai makusnacinsa yake gane yanayinsa na tsananin ɓacin rai.
Chapter 6 · 0% Book details