← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 57

Sashe 12

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A darare suka fito daga motar ko wannensu ya kama kansa,"waye zai dauka muku kayan"ya fada muryarsa a dake fuskar nan babu a lamun wasa a cikinta,da sauri suka juyo suka fara daukar kayan da dukkan su yafi karfinsu amma haka suka dinga kinkima suna shiga dasu yana tsaye yana kallonsu, bai matsa daga gun ba har sai da suka gama kwashe gaba daya sannan ya tasasu gaba suka shige ciki,suna kokarin wucewa daki ya buga musu tsawa "ku wuce muje sama"da sauri suka hade jikinsu waje daya kana suka kama hanyar da ya nuna musu aminatu tuni ta fara ruwan hawaye dan yau tasan me kwatarta hannun daddy babu shi tunda nana bata nan duk makiyanta ne a gidan dan haka ko kasheta zai yi babu me ceton ta sai Allah..

Suna shiga falonsa yasa su nil doun yace duka su rufe idanunsu su daga hannunsu sama,tunawa da azabar da ta taɓa sha a wancan karon yasa ta fashewa da kuka,yana ji yayi wucewarsa daki dan yasan babu wanda ya isa matsawa ba da izininsa, sosai aminatu ta fara tausayawa Khalid saboda shi yaro ne sannan kuma duka babu laifinsa a cikin abinda ya faru dan haka ta kallesa taga yadda yake ta tangadi cike da gajiya idanunsa duk sun yi laushi, amma yaron dake jarumi ne bai ko yi hawaye ba,ta ce"Khalid ta shi ka tafi Ni zan hada da nawa da naka nayi duk da cewa kai ba kayi kome ba"da sauri ya girgiza mata kai cike da tsoro yana cewa "a'a daddy zai yi fada kuma zai kara miki punishment"babu komai tashi kaje kawai"sai d ya ɗan yi jim kafin ya lallaɓa ya tashi yana dingisawa da haka ya bar falon ita kuma ta ci gaba da aikin duk da yadda gwiwoyinta suka sage suke neman kasa daukarta.

Fitowa yayi tare da bata umarnin taje ta yi sallar magriba ta dawo ta ci gaba,har zai wuce sai kuma ya dakata yana kallon gefanta kafin ya dawo da dubansa kanta,kana ya ce"ina Khalid?"kayi hakuri ba laifinsa ba ne kuma shi yaro ne ba zai jure ba shi yasa nace ya tafi zan yi duka har nasa"a hankali ya lumshe idanunsa yana jin wani abu me kama da tausayi da kuma wani abu na musamman da bai gama tantance ko meye ba,daga nan kuma ya juya ya fita, a hankali ta tashi ta nufi dakinta ta shiga bathroom ta dauro alwala tazo ta tada salla bata tashi ba sai ta dora da karatunta har sai da aka yi Isha ta mike ta yi, bayan ta idar ta shafa addu'a,sai ta tattara sallayar da hijabin ta linke sannan ta fita falo ta ci gaba da aikin da ya sakata,tana yi tana gyangyadi a haka ya dawo ya sameta.

A nutsensa ya zauna yana kallonta cikin wani irin yanayin da ya kasa fassarashi, abu daya yq sani shine baya iya jin haushinta baya iya fushi da ita, sannan kuma baya jin cewa laifinta ya kai a hukuntata,nuni yayi mata da ta tashi tsaye,girgiza mai kai ta yi hawaye na gudu akan kuncinta,lumshe idanunsa ya yi tare da kuma maida kansa jikin kujerar ya kwantar yana jin wani abu me kama da zafi akan zubar hawayennata,ganin yayi hakan sai ta yi tsammanin wani laifin ta kuma yi dan haka ta mike a hankali sai dai kuma.kafin ta gama daidaituwa kan kafafunta tuni ta yi luuuu zata fadi,cikin hanzarinsa da zafin namansa ya tarota ta fado jikinsa,ajiyar zuciya ta sauke saboda tuni ta ƙaddara zata sha kasa, kokarin tashi ta fara yi amma sai hakan ya gagara saboda yadda ya shigar da ita jikinsa sosai ya hana mata kwakwkwaran motsi sai na shaƙar numfashin da yake tafiya da kamshinsa tare da bugun zuciyarsa da take harbawa a hankali tamkar wanda ya shiga comer .

Shi dinma na ta bugun zuciyar yake saurara da nasa da yake hadewa da natan, sai kuma sakon zuciyarsa da baya fahimtarsa a yanzu.

Yanayin sauyin numfashinta da bugun zuciyarta ne ya fahimtar dashi cewa ta yi bacci, hannunsa yasa ya kuma zagayeta da wani irin shaukin da ya kasa tantance dalilinsa.

Yau kwanan su abby biyu da zuwa abuja kuma tun da suka zo kullum sai sunyi sittin da sabbin customers dinsu da kusan dalilinsu ne yasa suka zo Abuja,a bangare guda kuma bincike ne zazzafa suke akan asibitin ABM da kuma barister duk da cewa sun gama da bangaren barister tunda sun san shi a fuska abinda kawai ya rage musu ya kawo musu kansa, kuma suna da tabbacin hakan zata faru ta hanyar wasikar da suka tura masa,dan haka basu da ji a wannan bangaren hankalinsu ya fara kwanciya ta bangaren barister dan sun san cewa ba zai taba gudunsu ba saboda tanadin manyan kudaden da suka yi masa idan kuma yaki yadda kai tsaye zasu maida shi ya zama manyan makudan kudade fiye da wanda yaki karba a hannunsu, wannan shine shirinsu akan br.

A can asibiti kuwa hankalin halima ya fara tashi saboda yadda taga an fara zafafa bincike akan satar innawuro har ma hoton Hajara da mus'ab ya bayyana acikin c.c camara,sosai ta fara neman hanyar haduwa da mus'ab amma hakan ya faskara, karshe ma tunaninta tsayawa yayi saboda tsoron kar a gano ta acikin case din duk da cewa ta wani bangaren tana samun kwarin gwiwa akan cewa mus ab ba zai bari ba wani abu ya sameta ba.

A can gida bangaren su aminatu kuwa,tunda ta tashi yau gaba daya babu nustuwa a tare da ita, saboda tunin da aka sake mata a daren juya akan binciken dakin abby wanda a iya saninta ko Nana bata cika gani tana shiga dakunan abby ba saboda hakan shine abu mafi muni da abby ya tsana shiga duk wani bangare da akasan yana mu'amala dashi a cikin gidan,shi yasa aminatu ta cika da fargaba gashi kuma cikin ranta kamar ana hura mata wuta akan son yin abinda baffanta yake so ta yi da wannan matar da bata san ko wacece ba,aiyanawa ta yi a ranta sai dare zata shiga tunda a lissafinta sai gobe ne zasu dawo dan haka har ta yi abinda zata yi ba tare da kowa ya sani ba.

Zahida ce zaune gaban laptop dinta, ta zuba mata ido tana kallon daukar da aka turo mata yanzu ta Hajara da mus ab,wani irin zabura ta yi tare da buga teburin gabanta har sai da takardun da suke kai suka watse, me ya kawo daddyn Khalid nan?me ye hadinsa da wannan matar?tsam ta yi da ranta tana tuna fuskar hajara kamar a ranar ta ga gilmawarta acikin asibitin.

Da sauri ta dauki kan waya ta yi wani dan danne danne kafin ta hadata da kunnenta,ba tare da ta jira komai ba ta fara magana,yanzu ina so a turo min ragowar daukar ranar na masu shiga da fita,ake wayar ta yi tana ci gaba da sunturi a cikin makeken office dinnata tana yi tana duba laptop din dake dire ian teburinta, karar shigowar sako ne yasa ta yi saurin komawa ta zauna tare da bude sakon videon da ya shigo.

"What?"zahida ta fada tana nuna aminatu da camarar ta dauka suna shigowa harabar asibitin ita da Hajara, hannu tasa ta share zufar da take keto mata,kenan MUS'AB da AMINATU sun san wani abu akan sace innawuro?"ey lallai mana dole taga damuwar AMINATU kadan, me yasa mus ab ya biyewa AMINATU?ko dai ta sanar dashi wani abu akan sirrinsu ne tunda wannan abun da ya faru ya sa ta tabbatar da cewa AMINATU tasan wani abu akansu,ji tayi kanta yana daukar zafi dan haka sai kawai ta saka kiran iyayenta, suna dauka ba tare da ta jira cewarsu ba,ta ce "lallai daddys ku yi saurin baro abuja kome kuke yi ku bari ku dawo akwai ƙurar da ta tashi take neman cinye mu baki daya dan duk lamarin da ya haɗa da mus ab ba lamari ne na wasa ba,lamari ne da ake batun zaki ya bude bakinsa yana zaga daji dan neman me karar kwana"tana zuwa nan ta kashe wayar tare da kida kanta akan teburin tana tunanin ta ina zata fara kafin iyayennata su dawo,neman matar da suke tare ya kamata kisa a fara yi tun kafin wankin hula ya kai ku dare,zuciyarta ta bata amsa hakan yasa ta mike da sauri ta fice tana lalubo wayar danturkyi.

Tunda halima taga fitowar zahida jikinta ya hau bari, dan a gabanta zahida ta yi kiran farko dakin cctv din, duk da cewa har yanzu babu video da ya nunata a ciki amma cike take da fargaba da tashin hankali,bata tunanin wannan matar da suka dau innawuro da ita dan tasan ba lallai ne su samota ba(anata tunanin fa)bata iya zama ba itama tatatraw ta yi ta bar asibitin bayan ta sanar dasu cewa bata jin dadi ne.

A can Abuja kuwa cikin kankanin lokaci suka gama kome na tahowarsu, dukkansu zuciyarsu cike take da razani na jin cewa ta tabbata da mus ab cikin lamarin,amma sun yi kokarin boyewa saboda matansu kar su fahimci cewa everything is wrong with them,Dan haka suka yi kokarin nemowa kansu nutsuwar dole,a cikin wannan yanayin suka dauko hanyar dawowa Gombe,

Zahida ta kasa samun wayar danturkyi duk hankalinta ya kuma tashi,babu abu mafi sata cikin tashin hankali irin idan ta tuna cewa duk musu ab ya gano irin kasuwancin da suke yi babu abinda zai hanasa rabuwa da ita wanda hakan yana daidai da zuwan numfashinta karshe,hakan yasa ta kuma rudewa ta shiga bulayin neman danturkyi a duk inda tasan suna zama,har wajen isha tana yawo, daidai lokacin kuma su abby suka kirata sun sauka,dan haka kai tsaye ta juya da motarta ta nufi filin jirgi dan daukosu.

Tana faka motar a harabar wayarta ta shiga kuwa, har zata yi banza da kiran sai kuma idanunta suka hango mata sunan danturkyi yana yawo kan screen din wayar, cikin sauri ta dauka dan kuwa zahida a yani daya ta manta wacece ita saboda tashin hankali akan tunanin abu guda biyu da take matukar so da burin ci gaba da mulkarsu a rayuwarta suna shirin Kubce mata, wato kudi da MUS'AB.
Chapter 12 · 0% Book details