Sashe 13
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Haba danturkyi ina ka shiga nake neman ka tamkar rai na kasa samunka?bata jira amsar sa ba ta ɗora masa da cewa,"kaje ka shiga WhatsApp ɗinka na turo maka da hoton wata mata ina so duk inda take a daren nan a nemo ta bana son ku kai safiya ba tare da matar nan a hannunku ba",angama ranki shi dade wannan farilla ne agareni cika aikin iyayen gidana ko da zaro hanjin kanin mahaifinane kuwa",ajiyar numfashi ta yi ta re da kashe wayar tana jin zuciyarta tamkar kara hargitsata ake yi, dan bata jin ta sauke koda kwayar zarrar rabin nauyin da yake cunkushe a kirjinta,dakyar ta samu ta danne kadan daga cikin yanayin damuwarta ta fita taro su abby.
Hajiya zubaida ta ce ta dinga kallonta cike da son karantar yanayinta,ita ko Nana dama kusan a haka suke rayuwa da ita a gidan babu sakewa a fuskarta a tare da su shi yasa bata kawo cewa zahidar na cikin damuwa ba ne,su kuwa ubayen gayyar kowannensu da tasa zaunanniyar tashin hankalin da suke dannewa, haka suka dauki hanyar gida,duban lokaci Abby yayi yaga karfe tara saura dan haka ya dubi zahida dake ta tsala gudu saman titi cikin yanayin fitar hayyaci, sai da yayi dan gyaran murya sannan ya ce"dougter ina ga ki kaimu babban gida gaba ɗaya zuwa safiya idan muka huta sai mu wuce gida duba da yadda bamu sanar da kowa dawowarmu ba sannan dole yanzu zamu kuma fita office Dan gabatar da gundarin abin da ya dawo damu ba tare da mun shirya hakan ba"har Nana zata yi magana sai kuma ta fasa ta maida kanta gefe tana ci gaba da tunanin ahkinta da kuma abinda ya ke ta nukurkusarta akan gaba daya tafiyar tasu,dan itama tun maganar innawuro ta yi matukar sawa dukkan motsi su ido take kuma jin bata amince da duk wani motsinnasu ba a yanzu.
Kasancewar motar babbar mota ce kamar ta family yasa duk ta ccunyesu, daddy yana gaba kusa da zahida yana duba sakonnin da suke ta shigo masa bai samu nutsuwar dubawa ba saboda halin da suke ciki,a cikin sakon har da na br fele Wanda yake sanar da daddyn cewa yazo yana gidansa yana jiran karasowarsu saboda izinin zuwan da suka bashi dan gagarumar matsalar da taso so musu yau din.
A can kuma br fele ne zaune a falon da masu aiki suka shigo dashi yana zaman dakon karasowarsu, a daidai lokacin Hajara ta yi sallama hannunta dauke da ruwa da cup kanta a sunkuye tazo ta ajiye wa br fele da har yanzu kansa yake kan wayarsa,Hajara na juyawa wayarsa ta fara ringin daga wayar yayi tare da ficewa daga falon dan amsa wayar.
Lokacin da danturkyi ya bude hoton Hajara a cake yake bai ganeta ba,sai da daya daga cikin yaransa suka shigo ya nuna masa tare da sanar musu aikin da zasu yi akanta,yaran me suna bazuka ya ɗan zabura yana murje idanunsa tare da cewa "kai oga wannan ba wannan matar da Alhaji Jamil ya bamu kwangilar bazarwa ba ce?"sai a lokacin suka lura suka kuma dubawa sosai suka ga fa ita dince,dan turƙyi ya ce "tofa an yanka ta tashi asiri dole ya tonu kuma a wannan karon ko zan rasa raina sai na bazar da matar nan ta bar numfashi na rantse da wanda ya busan rai".
Suna zuwa gidan sauke su Nana kawai su kayi ba tare da ko fita daga motar sunyi ba suka juya suka bar gidan gaba daya su hudun,hoton Hajara zahida ta kunna musu tare da haska musu ita,bayan sun hau saman kwalta tare da cewa wannan ita ce aka gani tare da AMINATU da mus ab wanda hakan ke nuna i da cewa ta san abinda suke shiryawa shi yasa na bawa su danturkyi damar su nemo mana ita a daren nan"da sauri daddy ya shiga mirza idanunsa kafin cikin tashin hankali ya ce wannan ai sabuwar yar aikin da nake gaya muku na samu ce sabon kasuwanci"wani kallo abby yayi masa kafin cikin tunzura ya ce "amma dai garba kai wawa ne yanzu dan Allah me ye a idonka da ka kasa gane hoton matar da br ya turo maka taje wajensa da hujjoji har muka sa su danturkyi su kasheta".
Cikin sauri. Zahida ta kuma duba hoton wanda sai a yanzu itama ta tuna inda ta san fuskar matar,tabbas ita ce matar da taao daga mata hankali da tona mata asiri a cikin asibiti mata me aljanu tabbas ita ce"wani wawan burki zahida ta ci tana mai dafe kanta, kafin ta dago da kanta da idanunta suka yi jawur tana cewa to me yasa bata mutu ba?"wannan tambayar su danturkyi za a yiwa ita"daddy ya fada yana mai daga wayarsa kira daya kuwa, danturkyi ya daga tashin farko da ban hakuri ya fara sannan ya dora da cin alwashin karo na biyu babu kuskure,kai tsaye daddy ya sanar dasu cewa suke tana cikin gidansa amma kar su kasheta a wannan karon dan suna da bukatar jin wani abu daga bakinta......nima a gidan zaki sauke Ni dan ba zan taba bari matar nan tasha ba"cewar daddy da yake jin zuciyarsa kamar zata yi bindiga, "Nima ki ajiye Ni a gidan in yaso sai kai Alhaji Kabir kuje gidan Garba gaba daya,ni kuma zan tsaya domin ankara da motsin AMINATU da MUS'AB"
Abby suka fara ajiye wa a kofar gidan sannan suka wuce,ko security a fusace da bindigu suka leko gate din amma ga mamakinsu sai suka ga abby ne shi kadai ba mota ba driver ba Nana,cikin sauri suka fara yi masa barka da zuwa kafin su bude masa karamar kofa ya shige gidan.
Amiantu na cikin falon abby tana canke canken dakin da ya kamata ta shiga, zuciyarta babu abinda take sai bugu, duk da cewa kuwa rana da tabbacin ba yau su abby zasu dawo ba,haka.kuma kowa.yayi bacci tunda lokacin karfe goma da sha daya ne na daren hatta da mus ab ya jima da kwanciya zahida ce dai bata tunanin ma tana gidan.ahi yasa kawai ta yi shahada ta shigo a wannan lokacin,daga karshe dai canki zankinta ya tsaya kan dakin da yake daga can lokon corridor din Dan haka cikin sanda ta nufi dakin tare da murdawa, ba tare da ta yi tunanin a bude yake ba kawai ta ji kofar ta bude tamkar wanda aka bude ta a lokacin.ba tare da ta teaya bata lokaci ba ta ahuga bude buden loka da guraren ajiya wanda ita kanta bata san ainihin abinda take nema ko take son daukar ba,idanunta ne suka tdaya kan wani katon littafi me kauri da tudu,cikin sauri ta dauki littafin tana dubawa sai kawai taji wasu takardu sun zubo daga tsakiyar littafin, ta tsugunna tana tattarawa kenan taji alamun taku yana tunkaro dakin, take cikinta yayi wata irin murdawa sai kawai ta tsaya cak tare da zubawa kofar dakin ido........✍🏽
[4/22, 3:05 PM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page38``*
A kofar gidan daddy ya samu su ɗan turƙyi da shirin su na marasa imanin yan daba, ko wannen fuskar nan a shabune suna faman muzurai, daddy Bai tanka musu ba sai da suka shige gidan gaba dayansu, sannan bayan sun fito daga motar daddy ya tsaya da su Alhaji Kabir da zahida kuma cikin falon suna shiga, a nan suka samu br fele ya fito daga falon da yake ciki saboda jin shigowar motar su daddy, "yallabai me yake faruwa ne ?ina nan tun dazu ina jiran ku duk a dame nake saboda ina da tabbacin cewa kiran nan bana lafiya ba ne"br fele yayi maganar yana kallon kofar falon da zuge su daddyn zahida na shigowa shi da su dan turƙyi, Alhaji Kabir ɗinne ya bashu amsa da cewa br kai ma kasan ba lafiya ce zata sa mu dawowa yanzu ba tare da shiri ba,da farko dai ina sin tabbatar maka da cewa wannan matar me suna hajara bata mutu ba hasali ma ta yi badda kama ta. Shigo gidan nan da sunan me aiki"what"br fele ya faɗa yana baza idanunsa a falon tamkar wanda ke neman Hajara a gurin.
Cikin ɗacin murya daddyn zahida ya ce"duk wannan bashi muke bukata ba yanzu ɗanturƙyi ku yi hanzarin kewaye gidan nan ta yadda ko kwaro bai isa fita ba sai kun gansa, sannan ku shiga ko ina na cikin gidan nan ku ɗauko min ita ku kai ta can gidan gyaran hali, kar ku kasheta saboda a yanzu rayuwarta muke bukata dan dole sai ta amsa mana tambayoyi,kafin ta tafi inda take gudun zuwa".
"An gama oga"ɗan turƙyi ya faɗa yana kallon yaransa da suke jiran umarni sa,kallon da yayi musu yasa gaba daya su ka rabu mutum bibiyu suka ba zama cikin gidan wasu kuma suka yi waje dan tsare hanya saboda kar ta samu damar guduwa.