← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 57

Sashe 18

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daddy"ta kirasa cikin wata irin raunanniyar murya da har sai da ta sa ya bude idanunsa akanta,"me yake damuna wai?wacece ni?me ye a cikin rayuwata?me yasa girmana ya fara da haka?me yasa nake jin na samu sauyin rayuwa tun daga jiya?me ya sa nake jin cewa farincikina da walwalata ba zasu dawo ba?me yasa nake jin kamar an rataya min igiya me dauke da girman dala da gauran dutse, ji nake tamkar ina dauke da wani babban nauyin da in ban sauke saba zan iya mutuwa"ta karasa maganar wasu hawaye na gudu saman kumatunta.hannunta ya janyo tare da mannata a jikinsa yana jin yanayin yadda tempuriture dinta ke sauyawa kamar wadda zazzaɓi zai rufe,dago fuskarta yayi yana kallon idonta da suke ta hawaye kafin a hankali ya sanya harshensa da yayi sanyi ga wani kamshin da bakinsa ke fitarwa ya shiga lashe hawayen da suke kwanciya a tattausan kumatunta, sai da ya shanye su tas sannan ya hade fuskarsa da tata yana kallon cikin idanuna da ta kasa bude su ta kalli nasa idanun,magana ya fara yi cikin tsinkakkun kalamansa da basa fita dai-dai, ya ce"ba ko wani irin nauyi ne kike ji ba sai nauyin igiyar aure"yadda yake maganar labbansa na taba nata labban haka furicin nasa yake dukan zuciyarta,ci gaba yayi da cewa "AMINATU MATAR ƊAN BIRNI Aminatun baffanta Yusuf Aminatun innawuro Aminatu kawar bintalo da halimatu Aminatu rigimammiyar dadda ,Aminatu me leƙen dan birni a cikin bukka duk da taurkun nata kuma gashi har ya tafi bata taɓa ganinsa ba"shuru yayi da alama dai yayi abinda bai saba da yi ba,hakan yasa ya yi shiru yana maida numfashi tare da ci gaba da lalubo abinda ya kamata ya fada mata dan samar mata da nutsuwa wanda kuma zai sa ta fahimci abinda yake son fahimtar da ita....zai yi magana kenan wayarsa ta fara kawo haske da wani silet kida me taken momyna wanda hakan dole yasa ya yi shuru tare da daga wayar Nana.

Aminatu kuwa babu abinda zuciyarta take yi sai bugu,duk ina daddy ya San mutanen nan ko dai innawuro ce ta fada masa?anya kuwa daddy zai zauna innawuro ta bashi wannan labarin wanda duk yawancinsu shirmenta ne da ta tafka na kuruciya,zuba masa ido ta ci gaba da yi yana waya da Nana da take sanar dashi ta dawo gidan,"Nana ta dawo" ya fada mata yana kashe wayar,ganin yana kokarin janyeta daga jikinsa ya muke yasa ta yi saurin kanƙamesa tana girgiza kanta a kirjinsa sai dai ta kasa cewa komai,duk da cewa tambayoyine makil a bakinta wanda take son yi masa,ya gane dimuwar da ta shiga dan haka bai saurareta ba ya mike gaba daya da ita a jikinsa, sai da taga sun nufi hanyar fita ta dawo.hayyacinta tare da saurin sauka daga jikinsa tana mai girgiza masa kai alamun dai bazata fita ba,zuba mata ido yayi yana kallon tsoro karara a cikin idanunta,wato ke nan akwai abinda ya hanata zuwa wajen Khalid tun tashinta?ey no wonder yaga Aminatu taki sauka ashe da abinda take tsoro,cikin nutsuwa da komawa ainihin mus abb dinsa ya kama hannunta tare da kallon tsakiyar idanunta fuskarsa babu wasa kana cikin deep voice dinsa ya ce"gaya min wa ye kike tsoro?me ya same ki jiya?ko zahida ce?da sauri ta girgiza kanta fuskarta tuni ta koma kalar tausayi,to gaya min Anne ce?nan ma girgiza masa kai tayi,cikin yanayin fushi da yar tsawa yace "to waye ne kike tsoro fada min ko na saba miki anan".

Ganin kamar zai kai mata duka ne yasa ta dora hannunta saman kanta tana kare fuskarta tare da kokarin shanye kukan da yake son kwace mata fuskarta tana bayyana firgici da tsoron da take ciki,ganin yadda ta tsorata yasa ya ɗan sassauta, ba tare da ya ce komai ba kuma ya juya ya fice, tsugunawa ta yi a gun tare da sakin kuka me dauke da ma'anonin da ita kanta bazata iya fassarasu ko fahimtarsu ba,sai da ta yi me isarta sannan ta miƙe ta koma ɗakinsa dan bata jin zata iya sauka kasa ta haɗa ido da abby,saboda gani take kamar yana kallonta zai gane ita ce ta shigar masa daki,fadawa ta yi saman gadon tana yamutsa shimfidar dake kai tamkar ita ce ta yi mata laifi,wani ɗan ƙaramin littafi ta ji ta kama da hannunta, shuru ta yi tana rike da littafin ba tare da ta dago ta ga wane iri ba ne.

A hankali ta dago kanta da ke cikin shimfidar gadon da ta cusashi tare da dawo da hannunta dake dauke da dan littafin saitin fuskarta ta yadda zata iya ganinsa sosai,zubawa littafin ido wanda yake dauke da kwalliyar zaiba, kamar zata ajiye sai kuma ta fasa tana daga kwancen rugingine ta bude littafin tare da fara karanta shafin Farko da aka rubuta da manyan baƙi.

KOMAI YANA DA SANADI KUMA DUK ABINDA UBANGIJI YAYI YANA DA MANUFARSA, ALLAH YA KADDARA ZAN AURI AMINATU YUSUF SHI YASA YAYI SANADIN ZUWA NA RUGAR MALAM YUSUF...........

MAFARIN AL AMARIN......Tafiya ce ta samesa zuwa rugagen Fulani dan yin wani obxabation da ya danganci aikinsa,Nana kawai ya sanarwa inda ya tafi amma daga zahida har abby basu san ina mus ab ya je ba,dake su ma harkar neman kudinsu ita ce a gabansu shi yasa sam basu damu da sanin ba,shi kadai ya ɗauki hanyar rugagen cikin hilux dinsa bayan ya tanadi duk abinda ya san zai bukata duk da cewa ba wani jimawa zai yi ba.

Sai da ya ziyarci rugage uku kafin ya isa rigar malam YUSUF wadda ita kuma ta karshe daga nan gida zai juya,tabbas musu ab zai iya cewa duk rugagen da yaje babu rigar da ya samu karɓuwa aka gwada masa karamci sama da rigar malam YUSUF,sosai yayi mamakin karancin mutumin duk da cewa kuwa akwance yake magashiyan cikin cutar da kullum ba a sa ran zai farka da rai,amma a haka bawan Allah nan ya dinga nan nan da mus ab yasa aka kaisa bukka ta musamman wadda mus ab yayi mamakinta saboda babu abinda babu a ciki na zamani har da fanka da sauran abubuwa na bukatun yau da kullum,shi yasa mus ab yaji dadin zama a garin fiye da duk wata riga da ya zauna,sun yi sabo da malam YUSUF sosai duk da cewa mus ab ba ma abocin hira ba ne amma haka nan yake zama da malam YUSUF sabida ya fahimci Malam Yusuf din yana jin dadin hakan dan har dan zama ya kanyi sabanin kafin zuwan mus ab din da ko ruwa sai an tayar dashi an bashi.

Yawancin hirarsu da malam Yusuf din hirar tilon yarshi ce me suna AMINATU,ta haka ne mus ab ya fahimci tsananin son da malam YUSUF ke yiwa Aminatu,bayan sin kuma har da tausayi wanda a lokacin mus ab yana tunanin ko dan malam YUSUF din yaga yana gargarar mutuwa ne,sai daga baya kuma ya fahimci cewa ba haka bane akwai wani boyayyan dalilinsa,mus ab bai tana ganin Aminatu ba amma kaf halin Aminatu ya gama saninsa a bakin baffanta a lokacin yana tunanin Aminatu bazata wuce shekara shida zuwa bakwai ba,kaf rashin jin Aminatu sai da ya sanshi a bakin baffanta.

Wata ranar Alhamis ne ya kammala abinda ya kawo shi, dan haka yake sanarwa da baffan cewa zai koma gida washe gari juma kenan,baffan ya danyi tari sannan ya ce "idan ka tashi tafiya zamu yi wata magana da kai"daga haka baffan bai kuma cewa komai ba ,to shi din ma ba gwanin magana ba ne dan haka ya tafi nakwancinsa ba tare da zuciyarsa ta raya masa abinda baffan ke shirin aikatawa ba.

Washe gari mus ab bai fito da wuri ba sai wajen karfe sha biyu na rana,dan haka a dan gaggauce ya karasa bukkar malam YUSUF,inda ya samesa tare da mahaifiyarsa me suna innawuro,ganin suna magana da innawuro yasa mus ab ya fasa shiga bukkar ya koma da baya ba tare da ya bari sun Gandhi ba,shi din na bai ga fuskar innawuro ba,bai. Koma bukkar ba har sai da ya tabbatar sun kammala maganar da suke saboda ya fahimci maganar tana da muhimmanci tunda har yazo bakin bukkar amma basu ankara dashi ba,yana shiga baffa Yusuf ya saki dan murmushin dake nuni da jin dadin ganin mus ab da yayi,dan da farko jin shuru mus ab din bai zo ba har ya karaya a tunaninsa ko ya yi tafiyarsa ne ba tare da yazo sun yi sallama ba,

Abinda ya biyo bayan gaisuwar da mus ab yayiwa baffa ne ya matukar girgiza shi da dimuwar da tunda yake bai taba shigar makamanciyar ta ba,duk yadda mus ab ya kai ga iya boye labarin fuskarsa a cikin zuciyarsa a wannan ranar abun faskara yayi ,domin malam YUSUF yazo masa da bukatar da bai taba zaton zaizo masa da ita ba sannan ya kuma haɗawa da dora masa nauyin da baya jin zai samu salama a rayuwarsa sai ranar da ya sauke shi idan ma ya karba din ke nan,matukar karamci da kauna da yadda da Malam Yusuf yayiwa mus ab yasa yaji ba zai iya sarayar da bujatarsa ba, mu a ab ji ya di ga yi jamar mahaufinsa ne a gabansa yake rokinsa akan ya taimakeshi ya amsa bujatrsa domin ta hakanne kadai zai kubutar da aminatu da ga sharrin azzaluman mutanan can.
Chapter 18 · 0% Book details