← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 57

Sashe 20

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Fada sosai ake da wani dattijon bafulatani wajen bin layin ganin likita,acewarsa ya riga wanda aka kira ya shiga dan haka dole shi ne zai shiga idan ba haka ba kuwa babu uban wanda zai kara wucewa ta gabansa ba tare da ya sauke masa sandar dake hannunsa ba,ganin abu ya ki ci yaƙi cinyewa yasa dole security ɗin gurin suka yi kokarin fitar da wannan dattijon,ganin abinda suke kokarin yi masa yasa ya shammacrsu ya fada dakin ganin likita da gudu yana cewa, "aradun Allah yau sai naga likita ya duba yaga abinda yake damuna acikina ko da zaku kasheni kuwa"har securitys din sun sa hannu zasu daukesa sai likitan ya dakatar dasu tare da basu umarnin fita daga office ɗin.

Suna fita likitan ya nunawa dattijon waje ya zauna,zama yayi yana cewa na gode likita"ya sunanka?likitan ya tambayesa yana karbar Katin dake hannunsa,sunana baffa wuro?me yake damunka?likita ya kuma tambayar mutumin da sai yanzu na gane shi saboda tsomalewa da ramar da yayi kamar ba tsoka a jikinsa,baffa wuro ya gyara zamansa yana cewa,"likita yau tsawon shekaru ina fama da lalurar da na kasa gane kanta,duk abinda na mallaka,ya kare akan neman lafiya a wajen likitocin gargajiya,sai da komai ya kare sannan na yi tunanin zuwa asibiti,asibitin da naje na farko ban yadda da abinda suka fada min ba shi yasa na taho wannan saboda tabbacin da na samu akansa kuma nasan zaku fada min tsakani da Allah tunda ku ba dan kudi kuke aikinku ba"jinjina kai likitan yayi tare da cewa "asibitin da kaje na farko me suka ce maka?takardar scanning din da aka bashi ya zato yana cewa "cewa su kayi wai ƙodar da aka cire min ce ban tsaya an yi treatment din wajen ba shi yasa ciwon da yake wajen ya harbi daya ƙodar"kai me yasa baka yarda ba?likitan ya kuma jefa masa tambaya,baffa wuro ya ce,saboda Ni ban san akan me suke magana ba,Ni ban taba kwanciya a asibiti ba ma balle har a cire min koda,ko koda zata yi tsalle ne ta fita ba tare da na sani ba?"girgiza kai likitan yayi tare da yin rubutu a jikin katin baffa wuron sannan ya muka masa yana cewa kaje lab a sake maka wani scanning din Dan mu tabbatar da abinda yake damunka"karba baffan wuri yayi ya fita yana surutu da tsinwa wancan asibitin wai har da cewa sai anyi masa aiki gagarumi idan ba ayi nasara ba sai dai a sake masa wata ƙodar,kaji shegu ku gani a kanku".

"Anita so nake ki raka ni gun boko me maganin idonka idona"cewar zahida tana kallon Anita wadda jin abinda zahidar ta faɗa yasa ta yi wata irin zabura har da dage kirjinta,cikin mamaki zahidar ta ce"meye hakan meye damuwarki da zuwana wajen ko da kwai wata matsala ne?"girgiza kai Anitan ta yi tana ɗan share gumin da ya you a kan goshinta,kafin dakyar ta samu ta daidai ta kanta tana cewa"ba haka ba ne zahida gani nai ga abinda ya faru wancan zuwan bai zama alheri ba kuma ban taba zaton zaki ce mu kuma komawa ba ,shi yasa kika ga na zabura"to idan kin dauka ki ajiye dan kuwa zan koma kuma a yau cikin wannan rana kuma tare da ke" zahida ta fada tana komawa cikin kujerar da kwanciya fuskar nan Tata tamkar an yaba kashi saboda cushewa da rashin fara a,cikin rashin kuzari Anita ta ce"to yanzu akan me zaki je?"kai tsaye zahida ta bata amsa da cewa "akan musu ab zanje, dan ba zan taba bari mus ab ya gano wani abu akaina ba tare da na samu gurbin da ba zai taba iya rabuwa dani ba a zuciyarsa,Anita dole ne na mallake musu ab kafin ya san sirrina dan ina da tabbacin idan ya san ko Ni wacece bayan sakina da zai yi har kasheni zai iya yi".

"Saboda me kike fadar haka?meye dake da har kike wannan tunanin?Anita ta tambayeta cike da zumudin samun damar jin wani abu daga cikin sirrin zahidar,sai dai kuma bata samu amsar zahida yadda take so ba,dan kuwa mikewa zahidar ta yi tana cewa muke kar dare yayi mana saboda bani da lokaci "hankalin Anita ne ya dawo jikinta cikin sauri ta dauki wayarta jikinta na rawa ta ce muje waje gani nan zuwa bari na dan yi fresh up"daga haka ta fada bathroom hannunta rike da wayarta,fita waje zahidar ta yi tana cewa ki yi sauri karki ɓata min lokaci bana cikin mood din da zan iya daukar wata damuwar yanzu wadda nake ciki ma ta isheni".

Anita na shiga bathroom ta danna kiran wata nomber,jim kadan aka daga,bata tsaya sauraron abinda yake fada ba,ta dora da cewa "yallabai na shiga Uku zahida na shirin gano komai akaina,yanzu ya zamu yi a ina zamu sake nemo bokan karya"shuru ta yi tana sauraronsa kafin ta kuma cewa,"ok shike nan na nutsu oga,yanzu zamu tafi wajen dan haka kayi kokarin ganin ya riga mu zuwa ayi duk shirin da ya kamata Ni kuma zan dinga jan lokaci tunda Ni zan yi driving ɗinta"cikin tsawa ta ji zahida na kwala mata kira tana masifarta cikin isgili da nuna cewa anitar ce a kasanta,cikin sauri Anita ta kashe wayar tare da boyeta sannan ta wanke fuskarta ta fito tana cewa sorry cikina ne ya ɗan murda kinga bai kamata mu fita a haka ba tunda doguwar tafiya zamu yi"bata ce komai ba zahidar sai harara da tabi anitar da ita, a haka dai Anita ta lallaba zahidar ta gama shiryawa sannan suka tafi.

******

Abinda aka fadawa baffa wuro a wancan asibitin da yake ta zaginsu shine ya kuma fitowa a wannan asibitin na ABM,Wanda mutane suka shaida nagartarsa da ingancin likitocin cikinsa.

Kuka baffa wuro yasa yana fadin,"yaushe aka cire min koda ban sani ba?Ni wane irin mutum ne da za a taba cikina ba tare da danina ba?"likita ya ce tabbas an cire maka koda ka dai je kayi nazari sosai ka tuna inda hakannta faru" daga haka ya sallame shi akan cewa zai je ya dawo dan ayi shirin yi masa aiki.

*****

Isma il bai san cewa Nana ta dawo ba,saboda tun ranar da ya fito daga dakin Anne Bai Kuma shiga gidan ba,saboda gari yana wayewa ya bar gidan, sai yau ya dawo da mummunan shirinsa akan aminatu.

Mus ab yana fitowa daga mittin dinsu na kai da kai,kai tsaye hanyar komawa gida ya dauka,tun fitowar sa da ga Company ya lura da wata bakar mota tana binsa a baya, da bai yi tunanin shi take bi ba har sai da ya tsaya sai yaga motar ta yi slow daga baya kuma yaga an finciketa da gudu an wuceshi,bai zurfafawa kansa tunani ba ya wuce gida.

Tun karfe tara aminatu ta kulle kanta a daki da shirin karanta littafin da ta dauko a dakin abby,duk da cewa tana son ganin daddy a Karo na farko a matsayinsa na ƊAN BIRNIn ta,amma haka ta hakura, sai dai kuma ta wani bangaren zuciyarta cike take da tsoron bude littafin da tunanin abinda zata ci karo dashi a ciki.

A can bangaren isma kuma ya gama shirinsa tsaf na kaiwa aminatu ziyara,domin saida yasha yayi tatul ta shiga fada masa karya,sai dai bai fita daga hankalinsa ba saboda me aji da tsada yake sha,
[4/28, 7:18 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page42``*

Tunda mus ab ya shigo yake zuba idanun ganinta inda aminatu zata bullo amma shuru kake ji,har ya ɗan ci wani abu yayi wasu ayyukansa na cikinsa sannan yayi shirin bacci amma har lokacin bai ganta ba,haka nan yaji abun ya taba shi, dan yasan ya barta cikin damuwa duk da cewa yanar mata abinda zai ɗebe mata kewa,yasan aminatu zata so ganinsa sai dai ina bata karanta sakon da ya bar mata ba,sai da yayi Sallah misalin sha biyu sannan ya zura silifas ɗinsa ya fita kasan, dan sam ya kasa samun nutsuwar kwanciyar ba tare da yaga halin da aminatu take ciki ba.

A can bangaren su zahida kuwa sai da tafiya ta miƙa sai mota ta tsaya cak a tsakiyar daji,wanda duk cikin shirin Anita ne,hankalin zahida ya fara tashi ganin dare yayi sosai bata son ta kwana daji ga azalzala da zuciyarta take ciki,burita kawai ta ganta gaban boka domin kuwa tana da tabbacin zai bata maganin damuwarta saboda wancan aikin ma na idonka ina da yayi mata yaci kuskure kawai a kayi ta hadu da ɗan ladi abin ya Wada kansa,shi yasa yanzun take jin kwadaituwar komawar,Anita kuwa bata tayar da motar nan ba har sai da ta tabbatar sun gama saita komai , sannan ta yi 'yantabe tabenta a cikinmotar azuwan cewa itata gyara motar sannan ta tashe ta ,tana jin ajiyar zuciyar da zahida tasauke har da sakin dan karamin murmushin da ba a cika ganinsa akan fuskarta ba in dai ba a cikin tagwar manyan mutanen da suke da kudi da fawer ba.

*****
Chapter 20 · 0% Book details