← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 57

Sashe 32

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aminatu na zaune saman gado ta zubawa littafin ido, budewa take son yi amma zuciyarta na fargabar abinda zata ci karo da shi,ita dai ana bangaren bata ga abin tashin hankali akan littafi ba,to amma yadda masu littafin suka daga hankalinsu akansa shine yake bata kwarin gwiwa akan son bude LITTAFIN, a hankali ya kai hannu ta bude littafin take jikinta ya fara rawa,hannu ta kuma kaiwa zata bude shafin littafin inda take hango shatin rubutu amma sai taji hannunta na wani irin rawa kafin shima dakin ya fara girgiza, cikin kankanin lokaci kayan dakin suka fara barewa shi kansa dakin ya shiga juyawa kamar katantanwa,amma duk da haka aminatu na kankame da littafin nan,haka kuma zuciyarta cike take da dakiya da jin cewa duk runtsi fa yau sai ta bude littafin,to wai shi littafin nan wace irin masifa ce a cikinsa da haka take faruwa a duk lokacin da ta zo budesa,juyi aka ci gaba da yi da ita acikin dakin tare da Neman kifar da dakin da ita kanta da take kwaƙume da littafin,tun qminatu na dauriya har dai ta nemi gazawa saboda yadda ake wulwulata tamkar fanka,daga can kuma ta fara jin muryoyi suna magana tamkar a cikin kunnenta,ta wani bangaren kuma tana jin hayaniya da karar fashe tashen abubuwa kamar dai kokuwa ake yi,hakan ya kuma ruɗar da ita da saka ta cikin firgici.

A can kuma ɓangaren su Abby suna biye da duk inda turakarsu ta tsafi take nuna musu, fatansu daya shine su samu shiga gidan kafin mus ab ya koma gidan ,dan duk cikinsu babu wanda yake da kwarin gwiwar tunkarar mus ab din,dafe kai Abby yayi cike da takaici ya ce"ashsha batun mus ab ya mantar damu bamu karɓi camarar hannun dan ladi ba"Abba Kabir ya ce"kar ka damu bamu da matsala ta wannan bangaren tunda shi yana hannunmu da haka suka bar batun dan lardi suka koma kan ci gaba da tunkarar gidan.

Mus ab yana kan hanyarsa ta dawowa wayarsa ta yi haske alamun kira, kamar ba zai dauka ba sai kuma ya ɗan yi tsaki gami da kai hannunsa kan wayar ya daga,ba tare da ya yi magana ba,"shike nan ki dakata daga inda kike saboda fitowarki a kwai hadari ki tabbatar dai kin adana Flash din shi kuma Ahmad babu abinda zai sameshi zan karbo shi daga hannunsu insha Allah"shike nan amma dan Allah yallabai ka yi sauri gani nake kafin kazo ka karɓa wani abu zai iya faruwa"ya ce kar ki damu mama na tabbata yanzu hankalinsu baya kanki duk da cewa sun san kin tsira"ajiyar zuciya Hajara ta yi sannan ta kashe wayar tana kallon Flash din da dan ladi yasa ta daukowa daga gun da aka sace shi.

Yana tunkarar gidan yana jin wani irin bugun zuciya da har idan kai matukar kusantarsa zaka iya jin sautin da kuma yadda take harbawa da ƙarfi,so yayi ya fara zuwa wajen Hajara to amma ba zai iya ba saboda yana ji ajikinsa cewa aminatu tana bukatarsa a daidai wannan lokaci, hakan yasa ya karawa motar gudu sosai ta yadda zai iya zuwa cikin kankanin lokaci.

*******

Tunda suka tafi suka bar ɗan ladi da masu gadinsa yake kuka da hawayensa, ba kukan kome yake ba sai kukan farin ciki dan ya tabbata i yanzu Hajara ta bawa mus ab sakon da ya bar mata,(abinda ya faru shine lokacin da dan ladi yake waya tuni ya fuskanci cewa wannan me wayar ya biyo shi saboda yaji takunsa ta bayan sa,haka ne ya sa shi tsarguwa the cewa da wata a kasa,sauri yayi ya fara danna nomber hajara wadda itama ya riketa akansa, ya tura mata sako tare da saurin gogewa Sannan ya ci gaba da yin wayar ,ko mai yayi shi cikin kwarewa da dabara ne shi yasa har yayi ya gama mutumin bai fahimta ba,lokacin da ya mika masa wayarsa a lokacin ne yayi saurin dukawa ya ajiye camarar cikin ciyayin wajen tare da yin shedar da ya fadawa Hajara zata gane wajen,daga nan ne suka cafke sa suka dawo dashi nan)hakan yasa yake ji a ransa koda bai kubuta ba in sha Allah mus ab ba zai kyale mutanen nan ba duk da cewa da mahaifinsa a cikinsu,yana tsaka da tunanin ne kuma yaga alamun cewa babu kowa a kusa da inda yake,kasancewar sun manta basu kullesa ba yasa yayi saurin miƙewa tare da leƙawa wajen,sai kawai ya gansu kwance tamkar gawarwaki ga kwalaben giya nan a baje a kusa dasu ko wanne da zamankansa yake zaune,bai tsaya wani tunani ba ya tsallake su ya bi hanya ya fice da gudu duk da cewa babu kwari a tare da shi saboda uban dukan da ya ci kamar wani jaki,amma a haka ya lallaɓa ya fito daga gidan bayan ya dauke key din gidan daga cikin aljihun daya daga cikin masu gadin.

Duk Irin gudun da mus ab yake amma gani yake kamar ana dawo dashi baya abin ba karamin mamaki ya bashi ba,to gidan ne ya kara nisa ko me hakan yake nufi,take motar yayi ya kara mana gudu amma dai again sai ya kuma ganinsa a baya,take ya shiga tsananin damuwar da har ta bayyana akan fuskarsa abinda bai saba faruwa da shi ba,a nan ya kuma tabbatar da cewa akwai wani abu me kama da sihir da yake gudana a cikin lamarin gidansu.

Su Abby kuwa a dai-dai lokacin da suke tunkaro gidan zuciyarsu tuni ta cika da doki da hanzarin karasawa gidan dan sun tabbatar da nan ne inda sunduƙi ya nuna musu,sai dai suna gab da karasawa jikin karamin gate din gidan suka ga wata irin guguwa ta taso ta rufe gidan tamkar wanda aka sakaye shi cikin yana.

At tha sametime Kuma aminatu ce ta yi wata irin kabbara tana mai jan la ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minaxxalimin tare da bude shafin littafin wanda bude shafin yazo da wasu abubuwa masu tarin yawa na ban al'ajabi daga ciki kuma har da hoton mahaukacin mutumin da bazata manta fuskarsa ba da ta yi tozali da ita a cikin bangon littafin an rubuta ( SULAIMAN JA'AFAR LAMIƊO)da manyan baƙi......

Zahra...✍🏽

Na kudi ne

8064537048

Opay Fatima yusha'u Adam
[5/5, 5:03 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page49``*

Take jikin AMINATU ya shiga wani irin bari hannunta kuwa tamkar wanda ake girgizashi saboda tsananin rawar da yake yi,fuskar mutumin kuwa tamkar zata yi magana a cikin bangon littafin,cikin kankanin lokaci komai da yake faruwa a dakin ya tsaya cak komai kuma.ya koma mazauninsa tamkar ba anan aka yi yakin ba,shafa fuskar mutumin tayi da hannunta tana kokarin bude wani shafin inda ta hangi rubutu kananu kamar ba hannu ne ya rubuta ba,zaman sa kawai ta ji a gefanta yana mai sanya hannunsa ya janyota jikinsa ya rungume yana sauke boyayyar ajiyar zuciya tare da yiwa Allah godiya da ya bashi ikon karasowa gidan da kuma ganin aminatu lafiya,a hankali ta dora hannunta kan nasa hannun da yake kan cikinta kafin cikin rawar murya ta ce"daddy kasan wannan?" ta faɗa tana maida kallonta kan littafin,zubawa fuskar mutumin ido yayi yana jin wani irin nauyin zuciya, tsawon sakonni kana ya kauda fuskarsa yana jan numfashinsa zuwa cikinsa sannan ya furta cewa "ban san shi ba,ke kin sanshi ne kuma meye a cikin littafin ne da duk wannan abun suke faruwa saboda kawai kin dauko littafin?"da sauri ta amsa masa da cewa Ni ma ban sani ba shi yasa nake so na karanta littafin, wannan mutumin nasan shi shine mutumin da nace maka yana zuwa min a mafarki wai na temaka masa, duk sanda yake kokarin fada min inda zan samesa sai wani abu ya gifta na farka bana samun bayanansa"Nima ina son karanta littafin" ya fada yana taya ta bude shafin gaba na littafin.

A bangaren su Abby kuwa tunda suka ga gidan ya rufe da wata irin bakar yana shike nan suka gigice, gashi sun kasa ci gaba da tunkarar gidan,bude shafin littafin da karanta sunan da yake kai tare da hoto shine farkon wargatsewar lissafinsu, dan kuwa take motar da suke ciki ta fara wata irin haniniya tana juyi da daga hancinta kai kace wata muguwar dabba ce,cikin gigita suka rike junansu cikinsu na wani irin hargitsawa,Abby ne ya toshe kunnensa saboda wata irin kara da ta cika motar karar mutanen da akalla zasu kai hamsin,ko wanne da kalar tasa karar, su din ma abinda suke ji kenan, da sauri daddyn zahida ya bude idanunsa da suke rufe saboda tashin hankali da tsoron da ya kamasu wanda basu taba zaton zasu tsinci kansu cikinsa ba,kokarin fita daga motar suka fara yi amma hakan ya gagara dan ko motsi ta ki yi bare su saran zara budu,da wani irin gudu motar ta kwashesu suka bar wajen, babu abinda suke sai ihu babu wanda ya iya jan addu'a ko salati a cikinsu sai ihu da neman ɗauki a wajen bokansu,
Chapter 32 · 0% Book details