Sashe 54
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Isma kuwa rasa inda zasu nufa yayi dan duk gidan da yasan na abby ne idan suka je sai suka ga ansa masa kwado ko da da yan haya a ciki kuwa,saboda dukiyarsu gaba daya ta zama ta Baitul Mali dan gaba dayanta sun sameta ne ta hanyar kwace da fashin gidajen talakawa da gonayen Fulani da shanyen su da dabbobinsu,hakan yasa isma ya damu wani mutum ya a ra masa waya ya kira daya daga cikin abokansa amma yana jin Muryar isma ya kashe wayar baki daya,haka ya dinga bin abokansa yana kira suna kin taimaka masa, duk da irin bushashar da yayi musu lokacin yana isma dinsa,tun yanzu ya fara nadamar biyewa abokan banza da ya tsaya yayi karatunsa yadda ya kamata da yanzu shima yana rike da wani muƙamin cikin rufin asirin Allah kuma, amma Gashi yanzu sun gujesa haram din da yake takama da ita itama ta gujesa lafiyar da yake takama da ita babu,kai duniya zan can banza ce wallahi idan ba mu yiwa kanmu fada ba zamu yi asarar rayuwa,hannu yasa yana goge tawayen da suke zuba kan fuskarsa, kallon anne yayi sai yaji wani irin tausayinta barin yadda yaga tana takawa dakyar kafafunta har sun kumbura,dare yayi sosai dan haka bai san wa zai kuma kira ya saurareshi ba,dan haka ya nemi gefen hanya ya zaunar da anne da ta har yanzu ta kasa yin magana daboda yadda zuciyarta k3 ci da wutar bakinciki duk ta tuna halayyar jamil sai ta ji hawaye cikin idanunsa3da kunar zuciyar da bata san yaushe ne zata daina ba, mota suka gani a gabansu har sun tsorata sai kuma su kaji Muryar malam jauro driver yana cewa anne tun dazu Alhaji babba da Hajiya Nana suka ce na koma gidan can na daukoki,amma banganki ba,gashi bana son komawa gida dan ban san me zance dasu ba,sai yanzu Allah ya sa na ganki ku tashi mu tafi "cikin farin ciki da godiyar Allah isma ya kama hannun Anne suka saka ta amota shi kuma ya shuga gefen m jauro suka tafi.
Lokacin da suka isa gidan larai da Hajara suka samu suna dakon jiransu kamar yadda masu gidan suka roke su da su yi,daki Hajara ta kai anne tare da shiga bathroom ta hada mata ruwa me zafi, kana ta fito ta kamata ta ta kaita banɗakin,tana fitowa ta samu larai ta shirya mata abincin da take so wato dan wake,ko da anne ta fito kasa cin komai ta yi har sai da larai ta ce zata sanrwa da Alhaji babba saboda wannan umarninsa ne akan cewa kar su bari anne ta kwana da yunwa bare wata damuwa, wannan kalamin shi ya sanya Anne jin wasu hawaye suna gangaro mata, bata taɓa tsammanin cewa bayan abinda Jamil yayi sule zai kuma kallon ta a matsayin uwa ba,sai gashi ya fara da bata gatan da ko a baya bai bata shi ba.
A bangaren isma shima ya samu kulawa daga wajen m jauro,shima m jauro yana gidan saboda tun mutuwar matarsa bai kuma wani auren ba,,kuma dama bashi da ya'ya.
A bangaren zaunab (Anita)ma sun koma ainihin gidansu na nan ita da mijinta da kaninta.
********BAYAN KWANA UKU......
hankula sun kwanta, mus ab tuni y adauke matarsa suka wuce kasa me tsarki yayi da sai daga baya su Nana gaba daya dai gidan zasu bi bayansu su je gaban ka a ba dan kara yiwa Allah godiya daga nan su kaiwa suhaima da sule karami ziyara,isma kuwa yana asibitin aminatu yana karbar magani bayan an yi masa dori me kyau dan a kwana biyun ya fara tafiya de de sabanin da da yake dingisawa.
A cikin kwanaki ukunne dai gwamnati ta shiga binciken asibitoci ka in da na in Dan tsafatace su daga baragurbi, dan yanzu mutanen Gombe sun kiyaya da sauran asibitoci,yayin da kuma mus ab ya kuma sanya hannu wajen bada tallafi ga talakawa da wanda suke daga cikin wanda aka taba kwacewa wata kadara,
Baffa wuro takanas ya je har estate Dan ganin innawuro ya bata hakuri da neman gafararta,itama dai bata ja da nisa ba tunda wanda suka yi abin ma gamsu nan suna karbar hukunci tun a duniya, to shi kuma wanda ya gane gaskiya ai ba lefi ba ne dan an yafe masa.
Gaba daya abokan kasuwancin su Abby sun razana da abinda ya faru dasu,dan hak da yawansu suka.dinga ajiye wannan mummunan dabi ar suna komawa ga Allah yayin da suke ta fito da dukiyarsu suna yin sadaka da nema Allah ya yafe musu,dan babu wanda zai so rayuwarsa ta yi karshe irin na su Abby.
Matar Alhaji Kabir tuni ta tattara ƴaƴanta maza suka bar kasar dan dama ita ba yar kasar Najeriya ba ce,acewarta gwara ta yi nisa da in da suke ko Allah yasa rayuwar ƴaƴanta ta inganta,
Itama Hajiya Zubaida garinsu ta gudu gidan iyayenta da fatan bude sabuwar rayuwa me inganci dan so take ta yi aure ko Allah yasa rabon yana tare da wani.
Garba da Kabir dai da alama ba zasu kai ba, dan treating din da aka yi musu na konar da su kayi ba wata me inganci ba ce,shi yasa ta dinga cin jikinsu ga kuma tururi da suka shaka,daga karshe dai a cikin wannan ranar suka amsa kiran Ubangijinsu a tare sai dai banbancin lokaci,shi Kabir da safe shi kuma Garba da sha biyun rana, Allah ya sa hutunsu kenan Allah ya sassauta musu alfar shugaba da kuma tuban da suka yi har ransu.
Zahida kuwa gaba daya sai yadda a kayi da ita,idanunsa ne kawai a bude babu abinda kake gani a cikinsu sai hawaye saboda babu wanda yake lekota, dan ba ta samu tana karkashin kulawar jami'ai ai da ko kashi ta yi babu me wanke mata,shi kuwa Abby gaba daya idan ba da allura ba baya barin mutane su ji gari dan har an fara tunanin da ya ɗan warware za a mikasa asibitin mahaukata.
*****
Yau satin su aminatu daya a saudiya,tun da suka je ibada kawai suke, har zuwa yau da su Nana suka karaso,hatta da kaka da larai masu aiki sai da aka taho da su,m jauro Hajara da su zainab Anita da Ahmad Anne da isma, securities kawai aka bari a gidan,zuciyar kowa cike take da farin ciki, sai kuma ga suhaima da sule karami suma sun iso,kai wannan ahli fa ya cika da farin ciki, ririta juna kawai suke ,yayin da suka a dukufa wajen yiwa Ubangiji godiya tare da mika masa bukatun al ummar Annabi Muhammad s.a.w da nema musu sauki da shiriya,sai da suka yi sati biyu sannan suka rankaya suka tafi Dubai wajen Khalid.
*****
Khalid yana karasowa cikin gestroom dinsu sai kawai ya tsaya yana karewa kowa kallo, zuciyarsa cike da farinciki duk fuskar da ya kalla sai yaga murmushi akanta,tsaida kallonsa yayi akan fuskar Abba sule wanda a cikin mutanen da suke zagaye da shi shi kadai ne bai sani ba,Muryar aminatu ce ta bashi amsar tambayar da yake yiwa kansa da cewa,he is grand father ur name is Alhaji sulaiman Ja'afar"kafun6ta rufe bakinta ya nufo waje ta da gudu ya rungumeta,dama tunanin wajen wanda zai fara zuwa yake yi, kunnensa ta yi masa rada, hakan yasa ya sake ta ya nufi Abba sule da gudu ya rungume sa yana cewa idan kaine baban daddy na shi kuma Abby daddyn waye?"kai tsaye aminatu ta yi poiting yatsanta kan isma tana cewa daddyn uncle isma ne sannan grand fa dinka again"daga nan bai kuma yin wata tambayarba ya dinga binsu yana basu hug har yazo kan daddynsa, inda ya shige jikinsa yana cewa "daddy I miss You kai da adda aminatu"Nana ta ce mu da ba ayi missing namu ba sai a koremu,gaba daya suka sa dariya,sun jima tare da Khalid inda ya dinga karbar kyaututtuka daga ɓangaren iyayen sa zuwa kan kakanninsa,sai da suka zo yin sallama ne ya dubi daddynsa ya ce "daddy ina mommy ita bata zo ba har yanzu bata sona ko?"tale jikin kowa yayi sanyi babu wanda ya iya magana sai aminatu ta data ja shi gefe ta yi masa wasu maganganun da babu wamda yasan me ta ce masa,sun dai ga ya ware sun yi sallama cikin dadin rai, sai kewa da ta cika kowanensu.
Daga nan kuma su amintu suka wuce Faransa tare da suhaima da mijinta suke karami ya wuce gidansa tunda shi dama a Dubai din yake,amma yanzu ganin ahkinsa yasa shi jin kwadayin komawa gida,yayin da su kuma su abba sule suka.rankayo sai gida Najeriya.
Sun dawowa Abba sule ya karbi dukiyarsa da ya barwa Nana ita kuma ta dankata a hannun lauyansa,dan haka cikin aminci ya bude Companys dinsa da gidajen gona sai gidajen mai da aka dena amfani da su,isma ya jawo da shi da Ahmad ya danka musu wasu abubuwa da fatan zasu rike amana dan duniya yanzu ba tasa ba ce ta mus ab,yayi wannan ne kafin ya gama hutunsa ya dawo su ci gaba da tsare tsaren da ya kamata.to isma dai yayi hankali da karatun ta nutsu shi yasa ya sawa ransa rike amana ba zai taba yadda yayi rayuwa irin ta mahaifinsa ba,Abba sule da kansa ya je asibiti yasa hannu aka bashi zahida dan tuni aka gama shirye shiryen fita da ita US dan yi mata magani akan lalurarta,shi kuwa Abby hauka ta tabbata dan yana samu aka yi masa aiki ya fara tafiya shike nan ya ɓalle suka nemesa suka rasa,dan yadda ya fita babu kyan gani kusan tsirara yake dan duk ya yage fiye da rabin kayan jikinsa,surutansa na haukan duka ne da rashin imani, Allah yasa mu yi kyakkyawan karshe Amin.
*****BAYAN WATA BIYAR....