← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 57

Sashe 48

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana shigowa wajen taron kowa ya fara yin ta kansa saboda ihun da ya ci gaba da yi dan duk ya taba ƙafarsa yaji wannan jinin sai ya zabura,cikin kankanin lokaci kowa ya watse hatta da ma aikatan da suka dauko sun yi ta kansu, sai yasu yasu da suke ta faman rike abby saboda yadda yake ihu kuma duk inda ya juya sai yaga dan ladi cikin jini ko kuma sule da yake ta zuwa masa cikin kamanni kala kala,take dai Abby ya zama tamkar wani mahaukaci,Garba da Kabir har yanzu basu ga komai ba shi yasa suke zaton ko dai gamo Jamil yayi,dan haka suka yanke shawarar tafiya gida cikin iyalansu ko zai dai na gani tunda ita kanta gonar daji ce,saidai me suna tunkarar kofar fita suka ci karo da wani tashin hankalin dan kuwa kofa ta rufe kanta ga wani rubutu da aka yi a jikin kofar da jini, take suma hankalinsu ya fara tashi, duk kofar da suka nufa dan barin gidan sai su ji ta a kulle ga duhun da ya mamaye ko ina na cikin gidan,Garba ne ya koma da baya yana laluben wayarsa akan kujera amma a maimakon ya dauki waya sai kawai ya ji ya damki gashin mace cikin hannunsa,take ya zabga wani uban ihu yana mai komawa da baya,da sauri Kabir shima ya fara neman yin takansa sai dai kuma ina hakan bata samu ba,ji kake tim yaci tuntube da abinda ya tabbatar da cewa gawace sai ga goshinsa na fitar da jini,cikin rawar baki abby ya ce"kun ga abinda na ke gani ko kuna gani matatun da muka kashe ne suke ta dawowa,hatta da sule fa ya dawo dan ladi ya dawo sai kuma wasu da ban san su ba amma suma inaga duk suna daga cikin wanda muka kashe sai.....tsawar da suka ji an yi ne yasa suka hade guri daya suka cure kamar wasu kudaje,jikinsu rawa kawai yake idanunsu kuwa sai walwala sule saboda karshen budewar kwayar idon,jira suke kawai ko ji daga ina tsawar take, a maimakon haka sai kuka da suka ji ya biyo baya daga haka kuma sai dariya,wayyo fans zan so kuga yadda jarumai marasa imani suka koma cikin lokaci kankani, gaba daya sun fita daga kamanninsu,Kabir ne ya fara sakin fitsarin da ya rike masa mara kafin na abby ya biyo baya,wata siririyar murya suka ji daga can saman benen tana cewa, "sannunku da kokari aikin ku yayi kyau sai dai sakamakonsa ba me kyau ba ne ku a naku jahilcin kun dauka idan kuka kwace duk wata shaidar zama a kotu kun tsira kenan?"wata irin dariya Muryar ta kuma shekewa da ita kana ta ce"muje zuwa dan iska ka fasa muddin baku tonawa kanku asiri ba ba zaku taba daina ganin tashin hankali kala kala ba,daga haka suka ji dif tare da kawowar haske a lokaci daya.

Da mugun gudu suka nufi kofa suna ture junansu kamar wasu akuyoyi,ga mamaki su suna zuwa suka ga kofar ta bude gaba ɗaya,ai take suka ranta a na kare, duk cikinsu babu wanda ya nufi hanya daidai saboda tsananin tashin hankali.

Aminatu da mus ab kuwa tun bayan fitowar su daga wanka ya bata abinci ta ci sannan ya kwantar da ita kamar jariryya haka ya dinga jijjigata har ta samu ta yi bacci, cikin dare ya ji aminatu ta farka, sai da ta leka fuskarsa ta taɓa idonsa ta tabbatar bacci yake sannan ta zaro wayar ta ta sauka daga kan gadon tare da ficewa daga dakin cikin sanda,bude idonsa yayi kafin ya gyara kwanciyarsa ba tare da zuciyarsa ta raya masa bin bayanta ba.

Zama ta yi a kan kujera kafin ta fara magana kasa kasa tana cewa "Allah kuwa aunty zainab ban taba tunanin shirin zai kawatar irin haka ba,yanzu dai dukkansu sun fara karbar zunubinsu na duniya a hannu, ai yanzu ma aka fara wasan fata na dai su yi abinda muke son su yi, tunda dai bafulata ta tabbatar mana ba zata cutar da su ba kawai dai za a jijjga su ta yadda zasu tonawa kansu asiri da kansu wa duniya"dan jim ta yi da alama tana sauraren dayan bangaren ne, kana ta fesar da numfashi ta ce wallahi aunty zainab bana don ganin daddy cikin damuwa tausayinsa nake ji saboda halin da ya shiga na jin yadda komai ya faru na bangaren rayuwarsa"daga can bangaren anita ta ce,ai yanzu ke ce abin tausayi sminstu saboda ke duka uwa da uba babu kinga kuwa kece marainiya"aminatu ta ɗan turbude fuska kamar yana ganinta sannan ta ce"aunty ni ba marauniya ba ce saboda ina da daddy shine komai na a yanzu kumanna tabbata idan ina tare dashi ba zai taba barina cikin damuwa ba sai dai abinda ya fi karfin iyawarsa da kuma kaddarar da bai isa kawar da ita ba "murmushi anita ya yi sannan ta ce kije ki kwanta kar yarinman naki ya juya yaga bakya kusa dashi"daga haka ta katse wayar ta bar aminatu da sakin murmushi,ko da ta koma yana na a kwance idanunsa a rufe, bacci ya ke son komawa amma bai koma ba sai da ya jita ta rungumesa ta baya sannan ya saki boyayyiyar ajiyar zuciya tare da kuma janta cikin jikinsa.

*********
Har wayewar gari su Abby basu fahimci inda suke jefa kafafunsu ba, dan haka basu suka koma gidajensu ba sai wajen karfe tara na safiya,yadda yake abirkice haka ya je ya samu zahida abirkice saboda jiya itama vata yi bacci ba kwana ta yi iface iface saboda duk sanda ta rufe idanunta bata ganin komai a cikin su face ƙananan yara wanda ta dinga fedewa tana cire kodar ko zuciyarsu suna yi mata kuka a kunne,dan haka lokaci daya ta yi wani irin baki ta fige idanun nan sun firfito waje kana ganinta kasan cewa a tsira e take cikin ko wane lokaci,tana ganin abby ta nufosa sai dai kafin ta karasa inda yake yayi wata irin zabura ya janye saman bene yana cewa karki zo kusa dani dan Allah ki gafarce ni ki yi min rai kinga dai bani na kashe ki ba"mamaki ne ya kama zahida to ko dai shima ya fara ganin abinda take ganin?"zahida fa ba dayawa ta yi ba tsananin tsira ta ne yasa Abby ya ga zahida ta juye masa anita,da wannan sautan ya fada dakinsa.

Suma dai su Garba cikin tashin hankalin suka koma gida sai, shima Garba yana zuwa ya ci karo da dan ladi a bakin kofar dakinsa tsaye cikin fararen kaya,take Daddy Garba ya saki gudawa tare da kokarin komawa baya,sai dai kuma yana juyawa yaci karo da wani tashin hankalin dan kuwa Abba sule ya gani cikin irin shigar dan ladi wanda hakan yasa daddy Garba faduwa kasa sumamme bayan karar da ya saki.cikin sauri zubaids ta zo tana kokarin daga shi da zuba masa ruwa amma babu alamar zai farfaɗo dan haka suka ciccibesa suka yi cikin mota dashi,

Shi ma dai Abba Kabir ba a barda a baya ba dan bafulata ce ta dinga sauya kamannin su Abba sule da dan ladi tana firgita shi tare da sanar dashi cewa lallai fa idan basu tunawa kansu asiri ba, basu fara ganin komai ba,wanda hakan yasa shi fitowa da mugun gudu kamar mahaukaci sabon kamu, yaransa biyu da matarsa su ne suka rikesa amma kokarin kwacewa kawai yake yi.

A can bangaren asibiti kuwa, ganin halin da zahida ta shiga yasa kowa ya tattara inasa inasa suka bar asibitin hatta da ma aikata ba abarsu a baya ba,masu gadi ne kawai suka tsaya sai wasu likitoci biyu da suma suka tsaya dan gadin asibitin.dan haka koda su Hajiya zubaida suka kai daddy babu wanda suka samu da zai tsaya a kansa, dakyar dai suka lallaba wannan likitoci guda biyu suka shiga bashi taimakon gaggawa.

A cikin kwana biyu kawai su abby suka zare ko ina ganinsu za aka yi suna gudun ceton rai shida kabir ,shi kuwa dadin zahida duk sanda ya farfaɗo ko mintina biyar ba a yi zasu ga ya koma suma shi kadai yasan abinda yake gani,bzahida kuwa gaba daya kunnen ta ya daina jin komai idan ba kukan mutane da na jarirai ba,abin na su Abby ya fara tsoratar da mutane dan gaskiya ba iya abinda aminatu suka shirya akansu ne yake faruwa da su ba, akwai ikon Ubangiji da ya fara tabbatuwa akansu tun a duniya, sai ya zamana basu da wani wajen zama su ji dadi kan kace me an fara haskasu a gidan talabijin da takardun jaridai da gidan rediyo,akan cewa gjk sun haukace rana tsaka.

Nana tana can tana kallon duk abinda yake faruwa hankalinta kwance, dan tun a ranar da suka yi shagalin ganin fatalwu mus ab ya dauke ta daga gidan ya maida su babban gidansa da ya yi da guminsa dan zama tare da iyalinsa, gidan kamar etatet yake dan unguwa ce guda ya gineta saboda baya son yin nisa da ahlinsa so yake su gade waje guda gaba dayansu,musamman da yake binciken inda abbansa yake, a yanzu haka inna wuro da Nana da kuma Hajara da ƴaƴanta duka suna cikin gidan su ne kaɗai suka rage basu dawo ba, wato shi da aminatu da kuma abbansa.

******
Chapter 48 · 0% Book details