← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 57

Sashe 55

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wata kyakkyawar bafulatanar matashiyar yarinya ce,gefenta wani dangayun kyakkyawan bafulatanin da ya juye ya koma helf case ne,sanye suke cikin kayan sanyi da huluna irin na turawa masu taushi,tana gefen jikinsa suna saukowa daga matakalar jirgi, cikin kankanin lokaci idanun suka koma kansu,take fuskar mus ab ta koma ta ainihin mus ab mara dariya wanda hakan da yayi ne yasa na gane su,boyeta yayi cikin rigar sanyinsa me girma sai ya zamar mata dan jagora dan bata ganin gabanta sai inda ya sanya kafafunsa, a haka suka karasa gaba motar da aka zo daukar su da ita, wannan abin ba karamin burge mutane yayi ba,har wanda suke tare da mazajensu suka shiga wani kumbure kumbure wai ala dole suna so a yi musu irin na aminatu matar dan birni😃
[5/18, 8:52 PM] yushauadamfatima: Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page62``*

Da gudu motocin suka bar harabar filin jirgin, aminatu dakyar ta iya ciro kanta daga cikin rigar mus ab,tana samun kanta ta tura baki cikin shagwabar da sake sabuwa tun bayan samun juna biyunta,ta ce"daddy yanzu tsakani da Allah kana sane zaka kashe yar so?"Ni kuma yayi saurin magantuwa dan idan bai yi maganar ba wani sabon tashin hankalin ne,hawaye ta saki tana kuma cewa su tambayata ma kake yi bayan ka kulle mana fuska yar so na so ta kalli mutanen najeriya amma ka hana tsakani da Allah wannan aldaci ne?yadda fa kake jinka cikakken mutum haka itama yar so take jin kanta ato wallahi ama daina raina mata hankali?hannunsa ya dora kan cikin da ya ɗan fara tasawa kana ya ce "to yar so ku yi hakuri keda matar so"hannunta ta dora akan nasa ta janye tana cewa "haba daddy ya zaka dora Mata nauyin hannunka gashi nan kasa ta kuka"duk sai Mus ab ya rikice dan shi duk ya dauka gaske ne abinda aminatu take fada dan bai taba zama da me ciki ba ko cikin Khalid duk yadda yaso ya bawa Dauda kulawa sai ya hakura dan bai ga fuska ba,am sorry babyn so"ya fada yana dan shafa kan aminatu cikin kulawa da taka tsantsan,a haka suka karaso estate din, m jauro dai guguwa yayi kamar yana jin tutu ya tafi baya yana sheka wariyar da da baiyita ba tabbas sai ta zamar masa allura ashe dai har yanzu aminatun ce dai MATAR DAN BIRNI bata sauya ba.

Gaba daya mutanen gidan na waje kowa na cike da dokin ganin aminatu da kuma yar so din da kullum ba a da wani batu sai nata hatta da Khalid idan suna waya maganar yar so kawai ake yi,rungumeta Nana ta yi tana mata Barka da zuwa haka innawuro har zuwa kan su Hajara da anita da tazo itama da nata katon cikin dan tarbar aminatu,mus ab dai yana ta kallonsu har dai da suka gama da matarso sannan suka juyo kansa, ɗan karyar da kai wa Nana yayi lokacin da ta rungumosa gefenta, dariya ta yi tana cewa "kai fa ka girma dole sai kayi hakuri da ganin banbanci "alhaji babba da fitowarsa kenan shima dafa kan aminatu yayi yana mata barka daga nan ya rike hannunta suka karaso gun nana da innawuro,shima rungume mus ab yayi yana cewa "yaro na dai ya kusa zama baba in Sha ALLAH"wannan miskilin murmushin gefen bakin nasa yayi idanunsa akan aminatu da ta wani sunne kai kamar gasken kunyar take ji,gaba daya suka juya dan shiga cikin gidan,anan ne mus ab da aminatu suka yi ido hudu da zahida dake zaune kan kujerar guragu tana kallonsu idanunta cike taf da kwallar tausayin kanta,take aminatu ta turbude fuska tana kallon Mus ab da ya dauke kansa kamar bai ganta ba,ganin hakan yasa aminatun ta ɗan murmusawa zahida tare da cewa "adda zahida ya karfin jikin?"d sauki aminatu" zahida ta bata amsa cikin maganar ta da har yanzu bata daidaita ba,daga nan ta bi bayan mus ab,tana ji Nana na ce mata"me yasa kika fito ke da ba wadatarciyar lafiya gareki ba?"daga haka Nana ta turata suka shigo falon a tare,take wasu zafafan kwalla suka zubowa zahida,da ace bata kasance me son zuciya ba da yanzu ita ma tana gefen MUS AB a matsayin matarsa, ina ma zata samu alfarmar zama matar mus ab a Karo na biyu da ta fi kowa farin ciki a duniya kuwa.

*****

Lokacin da aka hadu a dinning room Dan cin abincin da aka yi musamman dan aminatu da mus Ab,kuwa zahida kasa sakewa ta yi dan duk sai taji ta mozanta,isma kuwa shima tunda suka gaisa ya wuce bangarensa dan shima kunyar hada ido da mus ab din yake.

Kowa ya fara cin abin da yake bukata sai dai aminatu bata taɓa komai ba,duk da cewa ba ita yake kallo ba amma hankalinsa kaf yana kanta kuma yasan abinda ya hanata cin abincin,to rayuwar da suka yi kaf aminatu bata cin abinci da hannunta tun kafin su bar gida ma,shi yasa yanzu ta koma kalar marayun da suka rasa me tallafinsu,Nana ce ta ajiye spoon dinta tana kallon aminatu da cewa,boddo yaya dai naga kin kasa cin komai,ko da wani abu da kike bukata wanda babu shi anan?"girgiza kai aminatu ta yi ba tare da ta ce komai ba,take kuma kowa sai ya bar abinda yake hankalinsu ya koma kan shalele matar so,alhaji babba ya ce aa diyata akwai damuwa dai ko?"da fadar haka aminatu ta rushe da kuka tana fadin Ni yunwa nake?"anne ta ce ki ji min wani sakarci duk abincin dake gabanki ko dai saboda da shakiyanci?"harara aminatu ta watsawa Anne tare da cewa Wallahi ki min shiru ko yau ki kwana da bera a dakin ki"ai ko take Anne ta yi gum da bakinta, dariya su anita da Hajara suka saka saboda dramar Anne da aminatu sababbiya ce da ba zasu iya dena wa ba, duk da cewa yanzu anne bata kallon aminatu da fuskar baya,kallon masoyiyar jika take mata, shi yasa fadansu ya koma na jika da kaka.

Nana ce ta dubi mus ab tana cewa"ka yi shiru kabarmu da shagwababbiyar matarka bayan nasan sarai kasan abinda ya hanata cin abincin?"kallon Aminatun yayi yayinda da ta kashe masa ido ɗaya tare da keɓe baki tana masa nuni da yar so fa yunwa take ji,kawar da kansa yayi yana kasa cewa komai,Muryar aminatu ya ji tana cewa "Abba ya sani fa yar so bata iya jure yunwa kuma ya sani dole sai ya bata a baki zata ci amma shine yayi shuru yana fiki fiƙi da idanu kamar bai san komai ba"da sauri Hajara ta miƙe ta shiga tattara duk abinda zasu bukata tana zubawa a cikin basken,sai da ta haɗa musu kayan abincin sannan ta kalli aminatu ta ce "taso matar so kuje dakinki na bangaren Nana ya baki abincin kar yar so ta samu matsala dan yunwa zata iya jigatata"kamar walkiya haka suka ga Mus ab ya bar wajen saboda maganar matsala da hajara ta yi,take suka sanya dariya, zahida kuwa wani irin kuka ta ji ya taho mata wanda hakan yasa ta Gara kujerar ta da hannunta da yafi lafiya ta bar wajen,gaba daya da kallo suka bita sai dai babu wanda ya tanka suka ci gaba da cin abincin su.

Hajara na ajiye basket din ta fita tana dariyar mus ab da duk ya wani birkice akan aminatun,shigewa jikinsa ta yi tana tura fuskarta cikin kirjinsa tana shaƙo ƙamshinsa da cikin ya kuma saka mata nacinsa,hannu yasa ya zagaye ta a hankali cikin takatdatdan dan yanzu sai ta ce ya matse yar so na kuka,amma idan ita ta so babu dabdalar da bata yi a jikinsa ba tare da ta yi korafin yarso ba,dago kanta yayi yana mata kallon cikin ido kafin a hankali ya motsa bakinsa yana cewa muje ki ci abincin ko?"girgiza kai ta yi tana wani shigar da idanunta cikin nasa,kawar da kansa yayi tare da janta suka zauna bakin gadon,shafa fuskarta yayi kana ya zura hannunsa cikin rugarta yana shafa cikinta zuwa samanta,kana ya hade bakinsu waje daya,ganin abinda yake kokarin yi yasa ta a kwacewa tana cewa daddy in gaya maka tsakani da Allah "?gyada mata kai yayi yana dan ajiye numfashi, ta ci gaba da cewa "wallahi daddy tsoro nake ji kar wasu ya'yan so din su karu akan yar so kaga zasu danneta amma wallahi ko Ni ina son jinka a tare da Ni wannan tunanin ne Yasa kaga ina ki"dafe kansa yayi yana jin takaicin sakarcin aminatu wani lokacin, wai a nufinta wani cikin zai kuma shigar ta ne bayan wanda take dashi,ta shi yayi zaune tare da janyo abinda yasa zata iya ci ya shiga bata, bai kyale ta ba har sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya fice daga dakin,duk sai kuma taji damuwa dan tunda taga ya yi mata haka fushi yayi,to ita da baya mata fushi ko dan yaga zahida ne? Saurin da wannan tunanin ta yi tare da shigewa bathroom ta yi wanka da ruwa masu kamshi, tana fitowa ta shafa humras da sauran turarukanta sannan ta zura doguwar riga me santsi wadda ta bi jikinta ta kwanta, daga nan ta ɗora abaya baka akai ta lulluba dan kwalinta aka ta fito fuskanta ta yi wani fes kana kallonta kaga me juna biyu.
Chapter 55 · 0% Book details