← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 57

Sashe 5

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su uku ne a dakin kamar yadda kowa ya sani ba su taba yadda da wani ba bayan junansu dan haka basu bawa Kowa damar shiga cikin kasuwancin sirrinsu ba baya ga abokan cinikayyarsu,wanda wannan kuma sune duniyarsu,Alhaji Kabir ne ya juya musu laptop din dake gabansa dan su kalli abinda ke ciki,zubawa fuskar ido su kayi duk cikinsu babu wanda yake tunanin ya taba ganin fuskar a rayuwarsa, dan haka su ka maida dubansu kan Alhaji Kabir din sunan masa kallon tambaya,shima bai ja da nisa ba ya shiga yi musu bayani kamar yadda bincikensu ya bayar,ya fara da cewa "wannan da kuke gani shine lauyan da muke nema ido rufe,kamar yadda kuka sani yana amfani da adereshin bogi wanda ta hanyarsa ne duk wasu Click dinsa suke bibiyarsa kuma ta hanyar adresoshinsa na bogi ne yake binciken duk mara sa ar da Allah ya kai hannunsa, to mu dai mun yi nasarar binciko sa ta hanyoyin da baza su misaltu ba kuma mun sha wahala kafin yin wannan nasarar,a yanzu haka na tura masa sakayayyiyar wasika me dauke da sakayayyun ma anoni wanda kafin ya fahimce su sai ya dangana ga cikakken bahaushe,mu kuma ta wannan hanyar ne zamu cimmasa dan zuwa gare mu kamar dai yadda muka tsara"bayan yin shurunsa ne Abby ya kuma kallon hoton kana ya ce"kuna da tabbacin cewa shine wannan?",dukkansu shiru su ka danyi suna mai zubawa hoton ido tamkar dai suna jiran amsar ne daga bakin hoton,can Alhaji Garba ya numfasa tare da cewa ba mu da wannan tabbacin,ci gaba da binciken mu shi zai bamu tabbacin shine ko ba shi ba ne,kuma zata iya kasancewa shine za kuma ta iya kasancewa ba shi ba ne,abinda dai yafi mu kuma maida kai wajen binciken, sannan ya batun wancan asibitin an samu wasu bayanai akansa?"ya tambaya yana duban Alhaji Kabir saboda shine yake da ilmi akan wannan har kar shi yasa komai suke barinsa a hannunsa in dai abinda ya shafi na ura ne,girgiza kai yayi kafin ya ce,a wannan binciken ne dai Gaskiya muke da rauni domin. Kuwa na kasa gano komai ta bangaren binciken na ura sai dai ban hakura ba kullum ina samo sabbin hanyoyin da zasu kara min haske wajen binciken, sai maganar tsohuwar can ita ma mun yi nasara wajen samo videon da yake dauke da matar da muke zargi"macece?" Suka hada baki wajen tambayarsa.

Numfashi Alhaji Kabir ya dan ja sannan ya ce,Nima ban san ta ba sai dai ga dukkan alamu mus ab ya San wani abu dan shi mu kaga ta bawa sako, sai dai bamu san sakon meye ba"cike da mamaki da wani irin yanayi na girgiza Abby ya mike tsaye ya dawo kusa da Alh Kabir kana ya ce,nuna min video na gani",girgiza kai Alh Kabir yayi yana cewa ai basu fitar da video ba, dole sai idan mun koma zaku iya gani a can wajensu,sai dai kuma iya daukar wajen kawai ya dauka gaba daya ragowar basu fita ba babu su ma kwata kwata a cikin fotej ɗin ",to me yasa haka cewar Alhaji Garba da shima ya shiga cikin wasiwasi akan mus' ab,bincike ne zai nuna masa komai duk da cewa Ni bana tunanin mus' ab ya san wani abu akan batan innawuro kawai dai ana son yin amfani da shi ne dan a kawar da tunaninmu, kun ga idan muka yi zarginsa to hankalinmu ba zai je kan ainahin wanda yake da alhakin abin ba"wata kakakafar ajiyar zuciya Abby ya sauke har da share wata yar zufa da ta tsatstsafo masa saman goshinsa,dan kuwa ba kara min girgiza yayi da batun sako mus' ab cikin lamarin nan ba,baya taba Fatan abinda zai sa mus ab ya San wani abu daga cikin sirrinsu saboda sanin nasa kan iya jawo sabuwar fitina ta tonewar asirin da dukkansu zai iya sanadin numfashinsu, Alhaji Garba ne ya dubi yadda Abby ya ke ta goge zufa kana ya sheƙe da dariya har da kwanciya shi kansa Alhaji Kabir dariyar yake yi,nunasa Alh Kabir yayi da hannu yana cewa" wai kai me yasa har yanzu kake tado abinda ya jima da faruwa,me yasa tun tasowar mus' ab Baka da kwanciyar hankali akan waccan bannar da muka aikata bayan kuma babu wani mahaluki da yasan abinda ya faru bayan mu ukun nan, dan Allah Alh jamilu ka dinga kyautata mana zaton alkhairi idan kana saka tsoro a ranka tamkar kana tunanin wata rana asirinmu zai tonu ne",numfashi Abby ya ja wanda kafin nan sai da ya dauki sakanni kafin yayi magana.

"Ni kaina na rasa me yasa duk na tuna wancan al'amarin sai hankalina ya tashi ban sani ba ko dan nine jagora, shi yasa abin yafi damuna,ko kuma dan saboda tasowar mus' ab ne hakan yake karuwa a raina,tsaki Alhaji Garba yayi tare da cewa wlh ban taba ganin uban da yake tsoron dansa irin kai ba,ace ka haifi da a cikinka amma ya zama dodo a wajenka kullum cikin firgita ka yake"Alh Kabir ya ce a'a fa Garba ka tuna dukan mu nan babu wanda baya shakkar idanun mus' ab,saboda shi wani irin yaro ne da Allah ya bashi kwarjinin da duk mahaluki da ya dubesa sai ya ji hantarsa ta kada musamman mara gaskiya,dan haka kar kaga lefin jamilu,"Abby ya ce "ashe ka fahimceni Kabir idan ba ku manta ba da kaina na hanasa zabinsa na fake da cewa dan yaki zabinna ne na karantar likita shi yasa na hanasa zabinsa na yin lauya, wanda kuma mu ba haka ba ne ta wajenmu,kawai tsananin tsoron yadda yaron ya taso ne yasa naji a raina idan ban canja masa tunani ba to tabbas zai iya zama silar kare rayuwarmu a kurkuku,dan da'a ce dana ya kulle ni gara ace wani ne can a duniya yayi min hakan kamar dai wannan"ya fada yana nuna hoton boyayyan lauya me gaskiya dake kan screen din laptop din Alhaji Kabir har yanzu,"hakan ma bazata faru ba domin tun farko mun riga da mun yi maganin duk wata shaida ko damuwar da zata iya zama mana matsala a cikin duniyar kasuwancinmu"dan haka ku tashi mu koma gida dan hakan ma yana da muhimmanci"ba wanda ya kuma.yin magana a cikinsu illa bin umarnin Alh Kabir da su kayi suka mike tare da ficewa daga dakin dan barin hotel din gaba daya.

Tunda Anita ta koma gida ,babu abinda take sai kaiwa da kawowa da tunanin sabuwar hanyar da zata bi domin samun yadda take so a wajen zahida,yanzu ne ta fahimci cewa zahida tana da wayo da hangen nesa akan sirrin da ya shafi rayuwarta,cizon yatsanta ta yi har sai da ta ji zafi ya ratsata sannan ta saurara,kafin cikin kaushin murya ta ce"zahida zan ci gaba da binki a hankali wallahi wallahi duk wayonki sai kin dawo a saman tafin hannuna zan jure har lokacin da haka mu zai cimma ruwa",daga haka ta haye saman gadonta tare da jan bargo ta rufe jikinta har zuwa saman fuskarta.

A bangaren isma kuwa yau da ya san cewa Nana da Abby basa nan, abokansa ya dauko su ka siyo kayan mayensu wanda babu nau in da babu a ciki suka shiga kwalbewa,duk da cewa ya fi shakkar mus ab akan iyayennasa hakan bai sa yayi tunanin bari ba,dan acewarsa mus' ab yayi nesa dashi in dai ba fada masa a kayi ba babu yadda za ayi yasan me ya aikata a gidan.

A hankali aminatu ta sauko daga kan gadon bayan ta tabbatar da ingancin baccin Khalid, sannan sai da ta tabbatar da cewa kowa iya yanzu duk nacinsa ya yi bacci, bude kofar dakin tayi ta fita, bayan ta dauko safaya key din dakin Anne wanda tun ɗazu ta sato shi a dakin Nana,berayenta ta dauko a maoyarsu, sai da ta duba su ta tabbatar suna nan da ransu sannan ta je bakin kifar Anne,ta bude a hankali cijin sanda tamkar wata ɓarauniya,tana bude kofar kadan sai ta tsuguna ta bude berayen daga cikin kejin suna ganin hanya kuwa suka arce zuwa cikin dakin Anne kamar yadda ta saita,ƙwafa ta yi tana maida kofar tare da rufewa, daukar kejin ta yi ta bar wajen cikin sauri a ranta tana fata a daren nan Anne ta ji bera saman cikinta,daki ta shiga ta fara kada kunne amma shiru tun tana sa rai har ta fidda rai ta kwanta itama bacci ya fara ɗaukarta.

Kamar daga sama Anne ta ji wani abu na bin ƙafafunta kamar zai shigeta,ai ko a miliyan ta farka tana yan dube dube da hannunta, jin bata ji komai ba sai ta yi kokarin komawa dan atinaninta ko mafarki ta yi tunda tasan dai abu ne me wuya wani abun cutarwa ya iya shigowa falonsu ma baran tana har dakinta,sai dai kuma kan ta gama gyara kwanciyarta ta kuma jin motsi a saman kanta, dan haka a maimakon ta kwanta sai ta mike zaune tana mai kunna hasken dakin inda idanunta basu sauka akan komai ba sai akan bakikirin din beran da yake ta wasan adabo akan gadon da yake jin kamar aljanna, Anne kuwa bata san sanda ta yi wata yar dungure ba sai gata a akasan gadon tana laluben mafaka bakinta tuni ya dauki kyarma ta kasa janyo wata addu'ar kirki, sai daga can ta fara jan wasu kalamai masu kama da karatun yan bori,allhumma wassikini wa maskini karatun tsoffi marasa kwari"abinda take ta maimaitawa kenan tana tafiya da rarrafe idanunta akan berayen da suke ta sabgoginsu.
Chapter 5 · 0% Book details