← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 57

Sashe 11

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me yake faruwa a nan?" Mus ab da shigowarsa kenan yake tambayar securities din da suka cukuikuiye saurayin aminatu dan karya😃,Daya daga cikinsu ne ya sanar dashi abinda ke faruwa, sai ko saurayin ya juya tare da rike akafr mus ab yana cewa,yallabai kayi min rai wallhi tsautsayi ne ya shigo dani wajen nan dama ba abinda zan siya dan ko kudin ruwan riba bani dashi, tsautsayin zan hadu da aljana sunbuka ne ya kawo ne,dan me wannan aikin aradun Allah se aljana, ku taimaka ku raba ni da ita ku bata hakuri daga yau ba zan kara ba wlh kasuwa ma zan koma na ci gaba da dakona"kallin nan na nu dake ne mus ab yayiwa aminatu kafin ya karbi list din a hannun security ya duba,bai ce komai ba sai atm da ya mika musu, jiki na rawa suka karba suka cire kudin da suka kai kusan dubu dari biyu,daga nan ya sa kai ya fice,duk da halin fargabar hukuncin da zai yi mata sai da ta dungurewa saurayin kai sannan tabisu da gudu.

Suna shiga mota Khalid ya fara bawa mus ab labarin saurayin yana yi gana dariya yana kwatanta yadda aminatu ta yi da yadda saurayin yake,shi dai bai tanka ba amma aminatu biyewa Khalid ta yi suka ci gaba da kwatanta maganar saurayin suna sheƙa dariya abinsu, a jikin wani katon store ya tsaya, hakan yasa suka fara murna dan da sun yi tunanin daga nan sai gida,fitowa suka yi a tare kamar gaske, sai dai yanayin takunsa yasha banban da nasu dole suka haƙura ya basu tazara, daidai da zasu shiga wajen Khalid ya ɗan marairaice fuska tare da hade hannunsa waje daya yana cewa"dan Allah adda aminatu kar ki kuma yin lefin da daddy zai tattaramu ya watsa a mota ya maida mu gida"harara ta watsa masa kafin ta ce"oh me ka mai dani ne?kana tunanin zan kuma yin abinda zai batawa daddy rai ne?to ka ma daina wannan tunanin dan har muje gida ba za a kuma jin kaina ba, yau dole na saki raina na ci banza har tsaraba zan yiwa makwabta kuma sai na kwashe rabin kayana na basu tunda yau zamu yi sabbi"ta karasa maganar tana sakin wani lafiyayyan murmushin da ya kara haska fuskarta,hannu suka hada suka tafa sannan suka ƙarasa shiga ciki,wanda shi har ya samu gu ya hakimce tare da kwantar da kansa jikin kujerar idanunsa a lumshe yana sauraron shigowar danjer aminatu da dan korenta Khalid.

Kamar abin arziki suka.fara zagayawa suna daukar duk abinda zai musu amfani, daga kan suttura har zuwa kayan amfanin yau da kullum,suna tafiya wajen turaruka Khalid ya shiga diba da yawa kamar ba kudi za a sa a siya ba,zai kuma dauka ta rike hannunsa tana cewa "Khalid mu barsa haka kar mu yi almubazzaranci gwara musa daddy yayi kyauta ga mabukaci"Khalid ya ce"adda aminatu ai daddy yana da wani kudin da zai yi sadaka ba sai mun rage wani abu ba"um um Khalid nace maka babu kyau mu dauki iya abinda muka san zamu bukata daidai misali, a hakan ma idan munje gida sai mun cire zakka mu rabawa makota ko almajirai masu bukata ko?gyada kai Khalid yayi suna ci gaba da zagayawa suna daukar abu daidai da bukata kamar yadda aminatu ta umarcesa.

Da gudu aminatu ta fito daga wani bangare tana fadin,inna lillahi wa innahu sulaimanu jama ku yi ta kanku ga dodannin duniyar sama nan"aiko kan kace me jama a sun fara yin takansu har da masu jefar da siyayyar da suka yi da masu karo da juna, kan kace me jama sun taru a bakin kofa wasu ta lipter dukkansu a razane, gashi har yanzu aminatu ba ta daina ihu da kururuwa tana zagaye duk inda tasan da ragowar mutum ba, kuma an kasa samun mutum daya da zai tambaye ta meye ko abinda ta gani,sai da ta fidda kowa daga tafkeken store din nan sannan ta tsaya cak tana makyarkyatar tsoro,hada ido su kayi da mus ab da yake zaune daga can inda suka barsa ya zuba mata ido fuskarsa fayau babu wata alama da zata nuna maka yanayin da yake ciki ko ya dauki lamarin, Khalid kuwa yana gefansa dan tun sanda yaji ihun aminatu ya arta ya dawo wajen daddynsa yana makyarkyatar tsoro.

Daya daga cikin security ne ya karaso gaban aminatu yana cewa, a ina kika ga dodon muje ki nuna mana dan ga mutane can a waje duka kowa yana so ya dauki kayansa da ya zubar muje koma meye a fitar dashi"gaba ta yi tana nuna masa hanya kusfa kusfa har suka zo wajen , sannan ta ja ta tsaya, dubanta security yayi tare da cewa yana ina?"cikin rawar hannu ta nuna masa ƙatuwar tedys din da suke zube a wajen saboda bangarensu tazo,wani uban tsaki security yaja yana kallon aminatu a wani irin fusace tamkar zai kai mata duka,kafin ya juya ya koma bakin kofa yace kowa ya dawo yaga abin da take yiwa ihun kar su damu ba abin tsoro ba ne ko na cutarwa, a hankali suka dinga dawowa har sai da suka shigo gaba daya sannan ya tafi da su bangaren toys din ya nuna musu abinda aminatu ta gani ta razana,take mutane suka ayi kan aminatu suna kokarin kai mata duka mus ab ya janye ta suka fito cilli yayi da ita cikin mota Khalid ma fa kansa ya turasa sannan ya shiga ya figi motar tamkar zai tashi sama.

A wannan karon gaba ɗayansu dif su kayi suna rarraba ido,aminatu kuwa yau tasan me kwatarta babu shi a duniyar nan, tsayawa suka ji ya kuma yi, suna ji ya fita amma babu wanda yayi gangancin bin bayansa,gani su kayi wata babbar mace ta fito daga katon shagon ɗinkin da yake cike da ma aikata ta ko wane ɓangare, cikin girmamawa ta gaida MUS'AB daga nan ya bude mata but don motar tasa yaranta suka dauki katiwar jakar da take shake da sitturun da basu san lokacin da ya saye su ba,dan ko wanda suka zazzaba basu bi ta kansu ba saboda gayyar da aminatu ta tara musu a store din,sai da a aka gama shiga da kayan sannan suka ga matar ta tsaya suna magana da mus ab, sai dai lokaci lokaci tana kallon aminatu da ta zuba musu ido kamar wanda take tunanin cinikinta ake yi.

Amma fa yallabai dole sai ta shigo shago mun aunata saboda bamu taba yi mata ɗinki ba,bare mu san ko mai nata"dan jim MUS'AB ya yi kafin ya dan waiga inda su aminatu suka zura musu ido ita da Khalid sai da yayi musu kallon minti ɗaya sannan ya furzar da huci me zafi ta bakinsa yana duban gefen Hajiyar ya ce"shike nan zaku iya tafiya"karasawa ta yi gaban motar ta bude tare da kamo hannun aminatu da take binta da kallon rashin sani da tambaya,"idan kika kuskura ki ka yi wani abu anan zan hadiye ki ne da ranki kawai oya kuje a aunaki"abinda ya fada kenan ya koma jikin motar ya jingina yana mai sa idanunsa a kan duk motsin aminatun.

Burkin da aminatu taja daga bakin shagon shine ya sa Hajiyar saurin kallonta,sai dai kafin ta samu damar tambayar ta dalilin tsayawar tuni aminatu ta yi zaman dirshen a gaban shagon tare da rafka tagumi hannu bibbiyu bakinta dauke da salati da innalillahi kafin kuma ta fashe da kuka tana cewa, "wallahi fitowar nan ta yau babu sa a cikinta dan gashi nan sai cin karo nake da bala u kala kala,idan ba bala I ba me zai kawo sangamemeiyar budurwa ta kafe a waje tsirara haihuwar uwarta, aradun Allah birni ba ta yi ba,kuma ba zan shiga wajen nan ba bare mu hadu mu babbake gaba dayanmu"da sauri Hajiyar ta kalli sassaken gunkin da suke tallan ɗinki da su cike da mamaki dan tunda aminatu ta fara shirmenta ta gane da abinda take,mamaki kuma ba na komai take ba sai na ganin macr har mace yar birni kyakkyawar bugawa a jarida tana magana irinna cikakkun yankauyen da basu taba sanin hanyar birni ba,zata yi magana aminatu ta yi saurin katse ta da cewa wallahi ko zaki haukace ko ki zama irin wannan budurwar ba zan shiga shagon nan ba aradun Allah ba zaku shafa min kashin kajiba,kiri kiri a dinga sabon Allah a......da sauri ta hadiye maganar ta saboda kamshin mus ab da hancinta ya shaƙo a daf da ita, wani irin kakkauran miyau ta hadiye tana raba manyan idanunta tsakanin hajiya da yar tsanonin da suke jere reras a bakin shagon,a hankali ta lallaba ta mike tsaye idanunta sun yi raurau ta mele bakin irin na shagwababbun yara gab take da fashewa da kuka,duban matar yayi a natse ba zaka taba cewa akwai wani abu na bacin rai ko sabaninsa a ransa ba,cikin tsitstsinka maganarsa ya ce"dole sai an yi gwajin nan ne?"yes yallabai dole sai an yi idan kuna son dinki ya fita daidai"jinjina kai yayi tare da dora idanunsa akan aminatu yana watsa mata wani azababban kallon da ya sa cikinta murdawa,babu shiri ta bi bayan matar aka aunata, lokacin da ta fito tuni har an sanyawa yar tsanonin kaya sun yi tsaf kai kace a jikin mutum aka sa kayan ,to sai lokacin aminatu ta fahimci cewa ba mutane bane yar tsanane,sai kuma ta fara murmushi tare da matsawa kusa da su zata shafa su karaf ta ji an figi hannunta da karfi, sanin ko waye yasa bata yi gardama ba ta bisa, sai dai tuni cikinta ya duri ruwan tsoro har wata kara yake yi.

Yallabai mus ab a dai yi mana a hankali kar a karya mu 😃

Zahra✍🏽
[4/20, 4:07 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page37``*

Da wani irin karfi ya figi motar tamkar zasu tashi sama,sai dai a yanayinsa ba za kaga hakan ba,basu kara tsayawa a ko ina ba sai gida, ita kanta aminatu ta shiga taitayinta dan a wannan karon daga ita har Khalid babu wanda ya kuma yin kwakwkwaran motsi bare yin wani abu me kama da laifi.
Chapter 11 · 0% Book details