← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 57

Sashe 7

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da ƙarfi aminatu ta runtse idanunta tare da hade hannayenta guri guda alamar roko dan bata taɓa tunanin yadda ya kusanto tan ba duka zai kai mata ba,jin shiru yasa a hankali ta bude idonta guda, sai ta gansa har yanzu tsaye gabanta yana mata kallon kurillar da har ta fara sabawa dashi, ajiyar zuciya ta dan sauke tare da dan yin dibi dibin neman hanyar da zata ratse ta gudu, sai dai babu wata hanya dan girmansa da kwarjininsa ya kankane ko ina,dan haka babu wata hanya da ta rage mata,dan haka ta bude idanunta gaba daya ta kallesa ba tare da ta yadda ta kalli cikin idanunsa ba ta ce,"dan Allah dan Allah na tuba ba zan kara ba",ta karasa maganar da zirarowar hawayen tsoronsa da har yanzu bai saketa ba.duk da cewa Kuma bata san lefin da ta yi masa ba,gira daya ya dage mata tare da cewa "me yasa ba ki ji ne amanata?" Yayi maganar tamkar ba shi ba haka kuma zuciyarsa kamar ba cikin barazanar fashewa take ba,"to to me nayi nifa ba Ni ce na kai mata bera ba"ta fada tana kebe baki zata rusa kukan da yake cin zuciyarta,cikin takaicin amsar da ta bashi ya karasa hade jikinsa da nata tare da lalubo bakinta, kana cikin zafin nama ya cafke harshenta yana masa wata irin tsotsa a ransa yana jin yana yin hakanne da sunan punishment, kuka aminatu tasa saboda yadda yake neman cinye duk wani abu da ta mallaka a cikin bakinta,a ranta cewa take shike nan aminatu ta zama bebiya hamma mus' ab ya cinye harshen yin magana,hakan da ta ƙaddara ya gama faruwa yasa ta kuma fashewa da kuka tana dukan ƙirjinsa ko zata samu ya rabu da ita,amma ina shifa dan gwagwarmaya dan Nana Asma'u tuni ya kurmance baya ji baya ganin kowa in ba Nana aminatu yar gidan baffa Yusuf jikar innawuro ba,wata irin azaba yake ji cikin ƙirjinsa wanda yake tunanin abinda yake yiwa aminatun shi zai sa ya samu Salama amma ina tamkar kara rura wutar dake babbaka cikin zuciyarsa yake,ji yake cinye aminatu ko maida ta cikinsa gaba daya ma bai isa kashe masa wannan rurarriyar wutar da bai san iya jimawarta cikin ransa ba,sai dai yayi mata kiyasi da lokacin shigowar aminatu cikin rayuwarsa.sannan bai san zafin na meye ba yanayin da yake tsintar kansa a ciki shima bai san na meye ba,bai san amsar ba, kuma bai san waye zai bashi amsar ba, dan haka dan rage raɗaɗi dole yayi abinda yake jin shi zai ragewa zuciyarsa azaba da raɗaɗin da take ji.

Dan kansa da kuma kukan aminatu da ya ji yana kuma zafafa masa zuciya ya hakura, sakinta ya yi tare da janta jikinsa suka kifa saman gadon, jin nauyinsa kanta yasa ta kuma kara karfin kukanta tare da bugun bayansa tana cewa,"aradun Allah ba zan yadda ba tunda ka cinye min harshe yanzu ko magana ba zan iya yi ba,kai mugu ne dan birni na yafi ka kirki duk da cewa shima baya magana kuma ban taba ganin fuskarsa ba,amma dai a hakan ya Fika kirki tunda shi bai taba cin....saukar tattausan lips ɗinsa da ta ji kan nata yasa ta yi shiru tare da datse bakin dan karma ya ce zai kuma cin wani abun,"yanzu da wane harshen kike MAGANA?"ya tambayeta bayan ya kwantar da fuskarsa kan tata fuskar yana dan janye nauyinsa daga gareta, jin ya dan saki jikinsa yasa ta daddage ta turesa daga kanta amma memakon ta samu sararin guduwa kamar yadda take SO sai kawai ta ji ta koma samansa ya zamana shi a kasa ita kuma a samansa wanda hakan ya bata damar jin wani irin tudun abu daga can kasansa, "wayyo hamma mus' ab me ye a jikinka me tauri kamar sand...hannunsa yasa ya rufe bakinta yana dan zare mata idanunsa da suka tuno mata da kwarjininsa, sanin cewa bata da wata hanyar kubuta yasa ta kwantar da kanta a kirjinsa tana mai jiyo bugun zuciyarsa da take harbawa a hankali,a ranta kuma ta kudurta cewa sai taga ciwon da yake jikin Hamma MUS'AB, tunda ta tabbatar da cewa babban ciwo ne dan duk sanda ya rungumeta sai ta ji girman abin ajikinsa,to da alama ma dai kullum karuwa yake dan yau abin ya bata tsoro sosai kuma taji tausayinsa ya kamata,da wannan tunanin bacci me nauyi ya dauketa, shi din ma bacci ne ya suresa ba tare da ya shirya masa ba.

Zahida kuwa duk abinda ke faruwa acikin gidan bata sani ba, dan kuwa tana can tana baccin asara baki sake da mafarkan mallakar duniya da mus ab din ta ita kadai, wannan shine kadai burin zahida kuma ga dukkan alamu ta dauko hanyar samun duniyar,mus ab ne kaɗai zai zama wahala a gareta.

Isma kuwa ya bar bangaren ne da mugun tunanin ta yadda zai ya samu aminatu ta ko wane hali wala da aure wala ba aure burinsa kawai ya mallaketa a shimfidarsa.

Cikin ikon Allah berayen nan basu kuma firgita Anne ba, dan haka tuni Anne ta shanya baki da tunanin an fitar da su ta ci gaba da baccinta hankali kwance duk da cewa da yar ragowar fargabar halin da ta shiga.

Sosai baccinsa yayin nauyin da har yaso makara sallah,cikin hanzari ya fito daga bayi, ragowar ruwan hannunsa ya yarfawa aminatu a fuska daga haka yayi fitarsa dan yasan dole zata tashi,aiko dai tashin ta yi bayan addu'ar tashi da ta karanta babu abinda ya biyo baya sai gunguni da haka ita ma ta faɗa bayin ta yi alwala tazo ta tayar da raka'atanil fijri.

Duk da baccin da ta ke ji amma haka ta daure ta zauna ta yi karatunta da laziminta lokacin shida ta wuce gari ya fara haske,dan haka ta rufe Kur'anin tayi walha tana idarwa ta maida Kurt anin majiyarsa tare da hayewa saman lafiyayyan gadon mus ab,ba tare da ko hijabin sallar ta cire ba.

Koda mus ab ya dawo bai tashe ta ba dan yaga alamun ta yi ibadarta,dan haka kai tsaye ya wuce gemroom, har ya gama ya fito aminatu bata farka ba, again bai tasheta ba ya wuce clothing daga nan ya wuce bayi, nan ma ya jima yana kalkale kalkale kafin ya fito jikinsa daure da karamin towel da karami a hannunsa yana goge bakar sumarsa me sheki, gaban mirror ya je ya fara shafa mayukansa masu ƙamshi da tsada, mikewa yayi tare da yin kasa da towel ɗin jikinsa dan ya samu ya shafa mai a guraren da bai sa ba,da sauri ya yawaiwayo tare da toshe kunnensa da karfi saboda karar aminatu da ta karaɗe ko ina na dakin, lokacin da ya juyo har ta fice daga dakin tana ci gaba da ihunta, girgiza kansa yayi yana mai ci gaba da abinda yake dan tuni ya gano abinda ya sa ta yin wannan ihun, shi bai ma san cewa ta tashi ba da ba zai yi gangancin cire towel ɗinsa ba dan yasan halin abarsa.

Dai-dai lokacin da aminatu ta fito daga dakin mus ab da gudu,lokacinne kuma zahida ta shawo kwana cikin shirinta na fita as usual tana wannan takun nata na ƙasaita tamkar ɗiyar sarki,gayu kuwa tamkar zai yi magana a jikinta, dama gashi ta karo uwar kiba, sai ta Kuma zama irin matan alhazawan nan,dan haka kai tsaye suka yi wani irin karo, sai ga zahida zube a kasa daga ita har braekcase ɗinta da jakarta, da sauri aminatu ta ja burki ba kuna dan ta damu da barin makauniyar da tayi da zahida ba ne, a'a sai dan kawai tasan ko ta sauka kasa babu wanda zata sanarwa abin tsoro da mamakin da ta gani,bugu da ƙari tasan bayan Nana zahida ce kawai wadda zata tausayawa mus ab kuma gata likita ta ko ina zata iya taimakonsa, dan haka ba tare da ta jira cewar zahidar ba ta fara magana cikin haki da nuna tashin hankalinta tana mai nuna bangaren mus ab din,"adda zahida dan Allah kije ki taimakawa hamma mus ab jela ne ta fito masa ajikinsa wallahi baki ganshi ba kato ko lankwasuwa ba ta yi, kuma fa girma take yi saboda duk sanda ya rungumeni ina jin tudunta ajikinsa ina taso in san meye sai jiya da ya ke cinye min harshe na kuma jinta, har na tambayesa ya rufe min baki da alama dai baya so hankalin yan gida ya tashi ne shi yasa yaki fada,"dan shuru ta yi tana mai da nunfashi kafin ta kuma fashewa da kuka tana cewa "dan Allah ki taimaka masa wallahi nasan yana jin ciwo sosai ".

Zahida fa ina tunanin sumewa ta yi a zaune dan tun da aminatu ta fara maganganun nan ta gano abinda aminatu take kira da jela kuma wai ciwo saboda rainin hankali,shi yasa tun da ta kame bata kuma motsi ba, kunnen ta ne kawai ya ci gaba da jiyo mata maganganun aminatu wanda ita kuma ba haka take so ba, so take in da Hali gaba daya kunnuwanta su toshe, ba gangar jikinta take so ta tsaya da aiki ba kunnenta take so ya daina aiki saboda jin wannan kalaman daidai yake da tashin hankalin jin lokacin mutuwarta.
Chapter 7 · 0% Book details