← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 57

Sashe 19

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Yusuf ya ci gaba da cewa mus abu ka daure ka yi min wannan alfarmar ka auri Aminatu saboda aurenka da Aminatu shi kadai ne hanyar kariya gareta, wallahi mus abu na yarda muddin ka zama kariya ga Aminatu na amince ka sake ta ka zama uba a gareta, amma dai yanzu aurenta nake so kayi dan Allah yarona,amana ce zan baka kan amana ga yata nan aminatu marainiyar Allah bata uwa sannan uban bashi da tabbas din kasancewa da ita, amana ta biyu kuma mahaifiyata innawuro sai kuma nauyin dukiyar aminatu da girmanta da zan rataya a wuyanka, sai dai ina rokon yafiyarka domin na dora maka nauyin da muddin wasu mutane suka gane hakan to rayuwarka na cikin hatsari,shin musu abu ka yarda wannan nauyin da nake shirin dora maka?"kai tsaye mus ab ya samu aknsa da amsawa domin sai yanzu ya san cewa AMINATU marainiya ce sai yanzu ne kuma ya gaskata hasashen da yake na cewa akwai dalilin da yasa baffanta yake mata wannan tsananin son da tausayin.

Mus abu yaga tsananin farin ciki a tare da baffa wanda har sai da mus ab ya dinga jin wani iri a ransa da yadda yake sa masa albarka tana masa godiya da addu'a masu matukar dadi,

Ana idar da sallar juma a aka daura auren mus ab da aminatu baffa sani Kani ga innawuro shine wakilin aminatu baffa Yusuf kuwa shine ya zama wakilin mus ab,mus ab da kansa ya bada sadakin aminatu, daga nan baffa Yusuf ya nemi da a kira aminatu su tafi, sai anan mus ba ya kuma yin magana ya nemi da baffa yayi hakuri yaje gida ya sanar da iyayensa idan yaso sai su taho baki daya su tafi da aminatun,baffa ya amince da wannan sai dai kuma kullin silallan gold din da ya haɗe su da wasu takardu na kadarori ya ce mus ab din ya fara tafiya dasu domin zamansu anan kusa dashi hadari ne, babu yadda muka AB ya iya bai so ba amma ba zai iya musu da baffa ba dan haka ya tattara ya tafi dasu ba tare da sun hadu ko sau daya da aminatu ba,

Baffa wuro ma sai da mus ab ya tafi. Sannan ya dawo shi yasa bai sanshi ba a fuska.

****

Ɗora littafin ta yi a saman fuskarta hawayen tuni suka jika littafin sharkaf,take ta ji komai ya na dawo mata tamkar wanda aka saita memoriin kanta.......
[4/26, 6:13 PM] yushauadamfatima: Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page41``*

Sosai abubuwan da suka faru a dai-dai wannan lokacin suka dinga dawo mata.

Duk lokacin da ta shiga wajen baffa sai taji wani irin kamshi wanda yawan shakarsa da take yi yasa har ta haddace kamshin a hancinta,a iya tunaninta a lokacin babu irin wannan kamshin a duniya dan haka ta sa masa ƙamshin ƴan aljanna,haka kuma so daya ta taɓa jin takunsa lokacin da take shanya a bayan bukkar baffa, shi yasa ta rike sautin takunsa wanda take ganin sun isheta makami wajen nemansa da ganesa.kamar yadda baffan bashi da abun fada a wajen mus ab sai ita,haka a wajenta bashi da abun fada sai ɗan birni dan alokacin baya fadin sunansa shine yasa masa dan birni,baffanta ne ya sa mata soyayyar dan birni da sha'awar zuwa birni amma ba tare da kowa ba sai ɗan birni.

Bayan an daura aurenta da mus ab ne kenan baffan yake kiranta da matar dan birni, runtse idanunta ta yi tana kallon lokacin a cikin idanunta tamkar a talabijin,

Tana kallon lokacin da baffanta ya kirasu ita da innawuro yana gargarar mutuwa babu abinda yake nanata musu illa su ci gaba da zama a nan saboda yasan tabbas wata rana dan birni zaizo nemansu, a cikin dare baffa Yusuf ya ce ga garinku nan, duk da kuruciya dale samun aminatu amma taji zafi da ciwon mutuwar baffanta dan har sai da innawuro ta fara hada mata da tofi sannan ta dangana.

Tun daga lokacin ne kuma rayuwarsu ta fara yawo basa wannan ruga basa wannan ruga basa wannan ruga,saboda hari da ake kawo musu a duk RUGAR da suka zauna, baffa wuro shine ya zama komai nasu, daga karshe dai zamansu ya mika a rigar ardon gari, daga nan ne kuma ya tattara su ya kawo nan.

Kenan mus ab yasan ita ce AMINATUnsa?No wonder yake mata abubuwa irin na mata da miji,ashe shi yasa itama bata iya dakatar dashi akan wasu abubuwa da yake mata?me yasa bai koma nemansu ba kamar yadda baffanta ya fada musu?ta yaya akai ya ganeta? Ko dai shine yasa baffa wuro ya kawo su nan?to amma ai lokacin da suka zo alamu sun nuna cewa mus ab bai san komai akan zuwansu gidan ba,wai me yake faruwa ne ? Wannan wace irin hargitsatstsiyar rayuwace mara kai meye baffanta yake boye mata?me ye asalinta ? Su waye suka kashe baffanta ? Menene baffanta yake so ta gano?

Zunbur ta mike tsaye tana yan dube dube,bafa a nan kika ajiye littafin ba"zuciyarta ta fada mata,domin ta ji a ranta duk abinda take son sani yana cikin wannan littafin,da wani irin sauri ta fita daga dakin kai tsaye ta sauko kasan, ko mai yinsa take a.hanzarce kamar wata zauntacciya,kacibus suka yi da Nana wanda hakan yasa ta mugun razana tare da hade jikinta waje daya,zuba mata ido Nana ta yi cike da mamakin sauyin da ta gani a tare da aminatun dan kuwa koda aminatu bata nuna mata ba kallo daya ya isheta fahimtar cewa wannan aminatun dake gabanta ba aminatun ta ce ta kwanakin baya ba.

"AMINATU lafiyarki kuwa?me ya same ki?Nana ta fada tana janyo ta jikinta,ajiyar zuciya aminatu ta sauke tana jinta tamkar ajikin mus ab,kasa cewa Nana komai ta yi, dan ita kanta bata san me yasa take boye abinda yake faruwa da ita ba,haka nan take ji a ranta ya zama tamkar sirrin da ya kamata ta boyesa a yanzu,kama hannunta Nana ta yi suka zauna a kan kujera, sannan ta dago da kan aminatun tana kallon idanunta da su ka yi haske alamun dai sunci kuka, "aminatu baki bani amsar tambayata ba,shin wani abu ya same ki ne ko wani ya miki wani abu?girgiza kai aminatu tayi tare da cewa Nana innawuro nake son gani dan Allah ki kaini gunta na ganta"shine abinda ya saki kuka da damuwa?"nana ta tambayeta zuciyarta cike ds wani wasi akan aminatun,jinjina kai kawai aminatun tayi tana mai kawar da fuskarta dan gujewa kallon rashin gamsuwar amsar da ta bawa nanan a idanunta,ba dan nanan ta gamsu ba ta rabu da ita sai dai ta gaya mata dole ganin innawuro sai ta bari mus'ab ya dawo, saboda ita bata da ikon kira mata innawuro dan itama shi da kansa yake kira mata ita, saboda baya son ana yawan kiran innawuro saboda dalilin da ya barwa kansa sani, aminatu bata ce komai ba tunda dama ba wai damuwar rashin innawuron ce ke damunta ba, tunda tasan innawuro tana cikin aminci da kulawa ta musamman.

Duk a ranar aminatu ta kasa sakewa duk taji motsin fita ko shiga sai hankalinta ya tashi,saboda ji tayi bata da wani abu da take gudun gani a yanzu sama da Abby.

A bangaren Nana kuwa ita ma din hakuri take da juriya na danne damuwarta a matsayinta Na uwa ,amma rashin jin wayar abby da rashin sanin ina suka je me suke ciki?ya hanata sukuni,saboda wayar da suka yi da hajiya zubaida ya tabbatar mata da cewa suma yadda abby bai waiwayeta ba suma gare su haka ne,ita damuwarta ba ta kome ba ce sai ta fahimtar da ta yi cewa su abby din akwai abinda suke boyewa ko suke aikatawa,baran ma idan ta haɗa da batun abinda suka so yiwa innawuro da abinda ya faru daga jiya zuwa yau ,duk sai ta ji ta cikin shakka da zargin su abby din da aikata wani mummunan abu, ga kuma rashin zahida wanda hakan yake nufin suna tare da iyayennata kenan, dan haka p cikin rashin sukuni ta wuni a gidan.

Ko da aka tashi su Khalid daga makaranta kai tsaye suhaimance ta zo ta daukesa kamar yadda mus ab ya bata umarni,dan baya son yaran ya fahimci damuwar da aminatu take ciki,yasan dole shima zai damu daga karshe ya cikata da tambayoyi, wanda a ransa.yake.jin cewa tsaf aminatun zata iya sanarwa da Khalid abinda su bazata iya sanar dasu ba, dan haka ya zabi nesanta su da juna na wasu yan kwanaki.

******

Ba tare da sallama ba zahida ta fada dakin Anita wadda take kwance tunda ciki tana duba wasu takardu ga kuma waya a kunnenta tana yi,cikin sauri Anita ta tashi zaune tare da saurin tura wasu daga cikin takardun da take dubawa can bayan gadon, jikinta.da yanayinta yana nuna rashin gaskiya da kuma tashin hankalin da zuwan bazatan zahidar ya haifar mata,tsayawa zahida ta yi tana kallonta na yan sakonni kafin kuma ta nufi kujerar hutu ta dakin ta kwanta tana maida numfashi ba tare da ta kuma kallon anitar ba,dan taga alamun anitar ta tsorata da shigowarta,sai da ta samu wasu yan mintuna kafin ta kauda shirin nasu da cewa,Anita meye haka kike yi nazo wajenki dan ki taimakawa zuciyata ta samu salama amma kin wani firgita kina kallo na,da kin san kina jin tsoron kike zaune a gida ke daya?wata boyayyar ajiyar zuciya Anita ta sauke tana mai kokarin dawo da hayyacinta, cikin dabara kuma tana hade kan takardun da ta baza dama tuni wayar da take yi ta mutu.

*******
Chapter 19 · 0% Book details