← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 57

Sashe 40

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A falo daddyn zahida ya samesu zaune,Hajiya zubaida tana ta lallashin zahida da bata baki, duk da cewa bata san me yake damun zahidar ba,dan ko da ta tambayeta shiru ta yi mata,to amma ita mom zubaida ta dauka duk akan mus ab ne dan tasan matsalar zahiri ta zahiri bata wuce mus ab, shigowar Garba ne yasa zahida tashi zaune tana kallonsa dan a yanzu babu abinda take bukata irin taji ci gaba a kan harkokinsu da kuma batu akan mus ab dinta,duk da cewa tana ji a ranta idan taga zata rasa mus ab din zata iya hakura da komai ta zauna dashi,zahida bata taɓa sanin son da take yiwa mus ab ya kai inda ya kai ba sai yanzu da take ganin zai kufce mata,kai tsaye daddy ya wuce can wajen hutawarsa yana cewa da zahida ta biyosa,tashi ta yi ta bisa mom zubaida ta bisu da kallo.

Suna shiga wajen zahida ta fashe masa da kuka tana cewa daddy me kuke yi ne haka kun tsaya kuna ji kuna gani zan rasa mus ab?wallahi dad idan har na rasa mus ab to nima zaku rasani"kama hannunta yayi ya zaunar da ita kan kujerar hutu ta wajen, sannan shima ya zauna, kafin cikin rarrashi da tausasawa ya fara sanar da ita duk shirinsu,a fusace ta kwace hannunta da yake cikin nasa tana cewa "dad wannan shirin da kuke ba nawa ba ne bana dawo min da farin ciki na ba ne,ko hanya ma basu hada ba dan haka ni zan yi duk yadda zan yi na tsira da soyayyar mus ab,ko da kuwa naku shirin zai War gaje"hana zahida me yasa kike abu kamar wadda kika fita daga hankalinki? shin kun manta tonan asirinmu naki ne?shin kin manta cewa idan mus ab ya haɗa hujjojin maka mu a koto ke zaki tsira ne bare a kai batun auren ki da shi?ki maida hankalinki jikinki ki nutsu mu hada kai mu kwace hujjar da take hannunsa idan har mu kayi haka ke zamu iya fitar dake akan cewa baki san komai ba kema a rufe muke baki komai ba tare da kin san abinda muke yi ba"ajiyar zuciya ta dan sauke sannan ta ce na fahimceka dad, Amma ko a cikin hujja babu anita da abinda yake hannunta a ciki dan tun a ranar na turata garin da ba a dawowa,shi kuma ɗan ladi da camararsa yana hannunsu ka ga kenan mune da mafi rinjayen hujja bamu da matsala idan har ya maka mu a kotu zaku fita akan rashin hujja nima zan fita akan ban san komai ba"da kyau shi yasa nake sonki yata,bari ma na kira ɗanturqui na gaya masa suƙara tsaro akan Yaron nan kafin mu zo mu karbi camarar wajensa sannan shima mu turashi ya tafi inda yayarsa ta ta tafi"ya fada yana latsa wayar , wayar bata shiga kin san wajen da akwai matsalar network,gibe na sake kira saboda a yanzu komawa wajen ba zai yiwu ba saboda idanun mus ab gaba daya yana kan duk wani motsinmu wata kila ma har da yan sanda kinga dole ne mu yi kaffa kaffa".

A can bangaren Abba Kabir shima ba a barshi a baya ba,daya daga cikin yayaransa me suna Kashim ya kira suka zauna,Kashim ya jima tare da Kabir kuma duk wasu aiki da ya gagari ɗanturqui shi yake sawa yayi musu,dubansa ya yi tare da yin gyaran murya sannan ya ce"Kashim aiki nake son sa ka amma bana bukatar kuskure komai kankantarsa"kai tsaye kashim ya ce ina jinka oga kar ka samu damuwa"jinjina kai Kabir yayi sannan ya mikawa Kashim din taswirar gidan mus ab kana ya dora da cewa "duk yadda za kayi ka shiga gidan nan ban ce ka taba kowa ba,kaga abinda nake so ka dauko min"ya fada yana nuna masa zanen littafin, sannan ya ce littafin kawai nake bukata zaka iya bari ma sai sun fito daga gidan sai ka shiga sabida bana son ka taba yarinyar nan domin tabata zai iya kawo mana matsala wajen dauke littafin, iya abinda na saka shi kawai za kayi"daga nan ya mika masa wasu mukullai ya ce idan ka je ka bude gidan da su,amma fa ka yi hattara gidan da zaka shiga da mutanen da suke ciki ba gama garin mutane ba ne shi yasa nake jaddada maka da ka kiyaye"karba yayi yana cewa an gama oga zan zo maka da littafin kamar yadda ka buƙata"daga haka ya sallame shi ya tafi.

******

Wankan mus ab da aminatu dai ya juye ya koma wani irin wanka na musamman,inda daga karshe ya dauke ta cak daga cikin ruwan suka fito daga bathroom din,a hankali ya shimfideta saman tattausan gadon da ya ji lafiyyyar shimfida ta alfarma tare da bin duk jikinta yana mata wata irin massage da lokaci daya ta rikita tunanin aminatu, babu shiri ta shiga kakkame jikinta tana fidda wani dan makirin numfashin da yake sauka a kan fatar kunnen mus ab yana zaga jini da kwakwarsa yana saculatin bargonsa tare da tafiya da duk wata jarumtarsa da kwarin gwiwarsa da yake jin zai iya hakura da aminatu,a hankali yake bin jikinta da wasu irin zafafan kisses masu ɗauke hankalin wanda ya yi zurfi cikin shaƙin ƙaunar da bai tantance ta ba,dukkansu farin shiga ne sabbin yan koyo ne sai dai zuciyoyinsu tsaffine feelings dinsu ma tsoho ne gangar jikinsu ne kawai sabbi, hakan yasa tsohuwar kauna da feeling dinsu ya rinjaye gangar jikinsu da take sabuwa akan baƙon al'amarin da ya ziyarceta.........

Zahra✍️

8064537048
0pay Fatima yusha u Adam

Amount 500
[5/11, 2:51 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page54``*

Jin inda ya kama yasa Aminatu sakin wani dan jinjirin kuka wanda bata san shine ya karawa mus ab karfin gwiwar ci gaba da abinda yake yi ba,babu inda mus ab bai bi ya aikace ajikinta ba,cikin salon da bashi yake yinsa ba zuciyarsa da ta yi zurfi da kuma feelings din da yake gangar jikinsa da kuma zuciyarsa sune suke fidda tsohon mikin da baisan dadewarsa a tare dashi ba,ji yake kawai zuciyarsa na sarrafa gangar jikinsa wani irin mayen romance mai tsayawa a kwanya yake yiwa Aminatun da karamar ƙwaƙwalwarta take neman juyewa, sai dai itama ana ta bangaren bata san cewa zuciyarta na sarrafa gangar jikinta ba,saboda yadda hannunta da jikinta yake kai komo a duk inda ya ci karo da shi a tare da mus ab ɗin, wani baƙon al'amari da ta fara ji shi ya yi kokarin dawo da ita cikin hayyacinta,a take ta fara kokarin ture mus ab da yayi nisa ba ya jin kira,a hankali ya dinga karanto addu'ar kasancewa da iyali yana yi yana kokarin daidaita jikinsa a jikin aminatu, duk da yadda mus ab ya ke jin kansa kamar ba shi ba hakan bai hanashi janyowa kansa natsuwa ba ko dan gudun cutar da aminatu,kukan da ta fara yi ne yasa shi saurin haɗe bakinsa da nata yana masa shan daga ke ba kari,duka da yakushi babu irin wanda mus ab baisha ba,yana samun natsuwa ya kankameta ajikinsa tamkar zai karya mata kasusuwan jiki,sai a lokacin ya saki bakinta ta samu damar fasa kukanta ta yi sa yadda ranta keso tana yi tana mintsinansa da ture shi amma dan gidan nana ko gezau bai yi ba,(yo ke ko aminatu wa ya gaya miki ana fada da jarumi kamar Mus ab)ɗan sassauta riƙon da yayi mata yayi tare da ɗago fuskarta da ta yi share share da hawaye da majina yana kallonta,lumshe idanunsa yayi tare da ɗan kai mata kiss a goshi hannunsa guda yana gyara mata dogon gashinta da ya burkice kamar na mahaukata sai azabar ƙamshi kamar wadda ta yi barin turaren gashi,"am sorry ya faɗa yana kai kansa cikin wuyanta yana sunsuna, "me kikeso na a wajena faɗa min ko meye shi ina ji"banza ta masa tana faman jan ajiyar zuciya.

Shi kansa wani irin zazzaɓi ne ya rufe sa amma duk da haka sai da ya tashi ya shiga bathroom ya haɗa mata ruwa me zafi, sannan y adawo ji tayi kawai ya sunkuceta kamar wata jaririya,bai direta a ko ina ba sai cikin ruwan ,tare ta sanya kuka me karfi tare da sin rashi , sai dai ina karfin ba daya ba dan mus,ab sosai.ya danneta yadda ba zata iya tashi ba,haka takaraci kukanta da dukansa har ta dawo tana jan ajiyar zuciya har da su gyanggadi,cireta yayi ya sauya wani ruwan shima sai da ya barta ta ɗan yi mintuna sannan ya tsaya akanta ya ce ta yi wankan tsarki, dai da yaga ta fara sannan ya juya ya fita,wankan ta yi tana faman lumshe ido saboda baccin da take ji,tana gamawa ta langaɓe kanta a jikin bahon sai bacci,yana shigowa yaga tana bacci hankalinta kwance ,hancinta ya ɗan ja sannan ya dauke ta bayan ya naɗeta cikin towel,akan gadon da ya gyara ya canja bedsheet ya sauketa tare da lullbeta sannan ya koma yayi nasa wankan,yana fitowa ya kwanta kusa da ita yana kallon fuskarta da take ta sheƙi.
Wani abu me sanyi ya ke ji yana kwaranya a ransa, sannan nauyin da yake ji a kirjinsa ya ragu,hannu yasa yana shafa fuskarta da tayi masa wani irin kyau,"AMINATU"ya ambata a saman labbansa kafin ya lumshe idanunsa yana jin damuwarsa na raguwa, Allah ka dai yasan irin farin cikin da aminatu ta bashi a wannan dare tun daga kan bangaren sauya rayuwarsa ta hanyar bayyana masa wani haske, yasan shi waye ta bangaren nasaba, sannan y San shi waye ta bangaren auratayya, bai taba sanin dadin aure ba bai nisan yaya yake ba,amma yau aminatu ta dandana masa zumar alfarmar da suke cikin aure ta mai dashi mutum cikakke ko yanzu zai iya bugar ƙirjinsa ya ambaci kansa da magidanci,aminatu ta inganta rayuwarsa, ji yake yi da ana maida mutum cikin zuciya da tabbas ya maida aminatu ya huta da nauyin sonta da yake neman tafiya da nunfashinsa.

*******
Chapter 40 · 0% Book details