Sashe 26
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zahida sun yi waya da Anita ta sanar da ita cewa daga yanzu zuwa ko wane lokaci za a iya ganin dan ladi,Anita bata nuna mata maganar dan lardi ya sameta ba sai tashin hankalinta da ta nuna akan rashin lafiyar zahidar duk da ta ce mata da sauki ciwon bakin ciki da na zuciya ne kawai wanda kuma shi maganinsa samun mus ab a hannu da kuma ganin karshen Aminatu,kai tsaye Anita asibitin ta yo.
Abby da daddyn zahida da Abba sun fito daga dakin bayan sun yi waya da su danturkyi akan cewa ya saki ɗan ladi amma ya tabbatar ya rufe masa ido kafin su fito dashi,amsawa danturkyi yayi tare da cika umarnin oganninsa,sai da suka fito cikin gari sannan suka watsar da dan ladi a gefen titin, dan ladi fa yasha wahala sosai a zaman da yayi tare da wannan mutanen da bai san ko su waye ba, sai dai yana gab da sanin ko su waye din tunda idan shi sun rufe masa ido ai camararsa da ya dana ajikinsa basu isa rufe mata ido ba,cikin jin nauyin jikinsa ya shafa gefen cikinsa ya tabbatar dan dunkulen camararsa tana nan sannan ya mike dakyar yana numfarfashinn wahala, wajen wani mutum da ya gani a tsaye yayi tare da rokonsa alfarmar Aron waya,bai musa ba mutumin ya bashi, sai da ɗan ladi ya ɗan matsa daga can gefe sannan ya sanya nomber da yake bukatar kiran da ita,jim kadan aka daga wayar ba tare da an yi magana ba,cikin saurin baki da haki ɗan ladi ya ce"ina magana da yallabai Musa tanko ne?"daga can mutumin ya miƙe zaune daga kashingiden da yake saboda daukar me muryar da yayi amma dan ya kuma tabbatarwa sai ya amsa masa da cewa shune dawa nake magana?"ajiyar zuciya ɗan ladi yayi sannan ya ce"yallabai ahmad ne ke magana".
Cikin sauri mutumin da ake kira da yallabai ya miƙe tsaye yana cewa"Ahmad kana ina yanzu ina fata dai kana cikin tsaro?"ey yallaɓai Amma yanzu zan karaso jikina ne babu ɗaɗi saboda ciwon da yake na zama waje daya"Ahmad amma dai basu yi maka komai ba kuma ka tabbatar ka dauko camarar nan dan ta hanyarta ka dai ne zamu samu shaidar wanda muke zargi"dan ladi ya ce duk na yi yallabai yanzu kasanar da anita abunda ake ciki"mutumin ya ce kar ka damu Ahmad ka ƙaraso kawai a yanzu Anita itama ta tafi dauko ragowar shaidun dan ta sanar min da cewa ta samu damar yin hakan ina fatan Allah ya bamu sa a baki ɗaya"Amin Amin daga haka ya kashe wayar tare da goge nomber daga kan wayar sannan ya juyo ya dawo inda mutumin yake ya miƙa masa wayarsa yana godiya,karɓar wayar mutumin yayi yana masa wani mugun kallo har sai da ɗan ladi ya ji ya tsargu, hakan yasa ya ɗan yi dumi dumi cikin rashin yarda da mutumin,taku daya ɗan ladi yayi dan barin wajen yaji an cafke sa tare da watsawa fuskarsa wata hoda take anan ya sume, su kuma suka ciccibesa suka saka shi a mota.
Lokacin da Anita ta karaso asibitin a maimakon ta nufi dakin da aka kwantar da zahidar sai kawai ta canja ta miki hanyar office ɗin zahidar cikin nutsuwa da BASARWA dan kar wanda yayi zarginta,hakan yasa har ta shiga office din bata samu matsala ba, dama ta jima da tanadarwa kanta key din office ɗin zahida saboda zuwan irin wannan ranar,koda acikin likitocin wani ya ganta gaisar da ita kawai suke su bata hanya saboda sun santa da zahida, da haka ta samu ta faɗa office din tare da rufewa, cikin sauri kuma ta fara neman abinda ya kawota abinda yasa take bibiyar zahida kuma shine sanadin shigarta rayuwar zahida,tana gama wannan aikin shike nan ta kammala abinda ya akawota babu ita babu zahidan sai idan sun haɗu a inda zahidan bata taba zato ba.
********
Akan idanun isma mus ab ya fito daga gidan,hakan yasa shi sakin murmushi tare da daga key din da yake hannunsa yana dage girarsa daya, sannan ya ce"Abby wannan aikin ba naka ba ne nawa ne,kai temakona kayi da ka bani umarnin na biyo maka bayansu maga inda zasu je,zan jefi tsuntsaye da dutse daya wato na biya maka buƙatarka Nima na biya tawa,dan yau babu abinda zai hanani jin daɗi da yarinyar nan"dariya ya sheƙe da ita yana buga sitiyarin motar tare da cewa wai matarsa"kai amma fa bayan nan ya rainawa mutane hankali ko a yaushe ta zama matar tasa oho?"Ni dai yau sai na ji abinda kake ji ato dan wallahi ba san bari a barni a baya ba,ina kallo ayi min ta leko ta koma ga dadi a gida ba zan je dawa ina nema ba"yana karasa zansa ya fito daga motar kai tsaye ya nufi gidan kasancewar da yar tazara daga inda yake biye dashi da motarsa dan ma ba motar gidan ya dauko ba, saboda lokacin da Abby ya kira shi ya sanar dashi abinda ke faruwa da abinda yake son yayi masa baya gidan, shi yasa ya dauki motar abokinsa ya fito da ita.
Cikin sa a yana saka key din ya bude kofar, shiga cikin gidan yayi ya ɗan kalli farfajiyar gidan ya tabbatar babu me gadi sannan ya sa kai cikin falon da yake madaidaici me kyau da tsari,daga nan ya fara bin dakunan yana gwada keys din hannunsa, sai dai ko alamun budewa dakunan basu yi ba,lokacin aminatu ta yi sallar azhar da la'asar tana zaune saman sallayar ta zubawa littafin dake hannunta ido, a hankali tasa hannu zata bude sai kawai ta ji alamun bude kofa hakan yasa ta yi saurin maida littafin ta ajiye a tunaninta mus ab ne ya dawo,to amma sai ta ji kamar ya kasa bude kofar, hakan yasa ta miƙe ta nufi kofar dan bude masa.
******
Tsayawar da Abby yayi daidai wani tsohon gida da su ma su daddy basu taba sanin da shi ba yasa su dubansa,dariya suka ga yayi tare da cewa ku fito kuga wani abin mamaki"cikin hanzari suka fito suka bi bayansa, har zuwa cikin gidan da yake da dan zurfi,a nan suka ga su ɗan turqui da yaransa sai faman muzurai suke yi,dakin da suke tsaye tsaye ajikin kifar suka budewa su Abby,dakin duhu sosai sai da aka kunna haske sannan suka ga abinda ke ciki,da sauri Abba Kabir ya dubi Abby ya ce"haba jamilu ya mu kayi da kai ai na dauka tuni kasa an saki yaron nan kamar yadda mu kayi da kai?"daddyn zahida ma kallon Abby yake yana jiran amsar da zai basu dan a halin yanzu da asirin jikin dan lardi suke takama da shi ne suke jin kwarin gwiwar samun abinda suke so ta wajen mus ab da zarar zahida ta mallakeshi,kujerar da dan turqui ya ajiye musu Abby ya ja ya zauna,yana cewa lissafinku da nawa ba daya ba ne,amma bari kuga wanu abyn mamakin"ya fada yana daga wayarsa tare da sanya kiran zahida,tana dagawa ya ce"maza ji ta shi ki bi ƙawarki Anita zuwa office dinki akwai abinda zaki gani,daga karshe zan turo su danturkyi yanzu zasu taho da ita nan amma ki yi iya yin ki na ganin bata kufce miki ba"ƙit ya kashe wayar yana kallin su daddy da suka yi suman tsaye,dakyar abba ya bude baki ya ce me hakan yake nufi kenan"?.
Abby ya ce"wannan tambayar na kiraku mu hadu mu yi musu idan an kawota, abu daya na fahimta shine ɗan ladi da Anita sun shigo rayuwarmu ne da wani dalili daban,shi yazo a matsayin me wanki ita kuma taxo a matsayin kawar zahida dole da wani abu a kasa kuma a yau nake son sanin komai idan ba haka ba na kashe su na kashe banza,da fari dai ka fara bani camarar da kake maganarta a waya sannan ka kira wanda kuke wayar dashi yanzu ka sanar dashi inda zaku hadu, ba kuma tare da ka nuna masa kana hannun kowa ba idan ba haka ba na fasa kanka da bindigar nan"Abby ya fada yana zaro bindiga daga kugunsa tare da saitata akan ɗanladi wanda har yanzu fuskarsa take rufe da bakin ƙyalle.
*****
Anita gaba daya ta haɗa uban gumi saboda har yanzu bata ga abinda take nema ba,hankalinta ba karamin tashi yayi ba dan har ta fara hawaye,tare da sambatu kamar wadda zata yi hauka,gaba daya ta firgita office ɗin, ta ma kasa nutsuwar tsayawa ta duba a hankali ko ta dace,babu abinda take hangowa sai karamin kaninta nuraddin cikin jini zuciyarsa a bude babu kyan gani,babu abinda zaka hango a idanunta sai wani irin fushi da azababbiyar wutar fansa da ke ta da ɗa ruruwa,muddin bata ga fayal ɗin nan ba to ta tabbata babu wata shari a da zata iya kwatar musu hakkinsu, babu wani lauya da zai iya tsaya musu, tunda shima wanda Shari'ar tasu take hannunsa ba sanin fuskarsa su kayi ba bare har idan ya gudu su iya nemosa, tabbas idan ba su hadu sun kawo karshen su zahida ba rayuwar mutane tana cikin hadari dan barin irinsu a duniya babban zunubi ne,a nan idanunta suna hango mata wata durowa sai dai kuma da pin take amfani, duk da haka Anita bata karaya ba da sauri ta karasa jikin durowar tare da fara gwada lambobi daga cikin nombobin zahida da ta sani na sirri wanda suma din ta sansu ne ba tare da zahidar ta sani ba.
******
Da gudu zahida ta fita daga ɗakin da aka kwantar da ita,sai bayan ta fito ne ta yi kokarin saita kanta,zuciyarta kuwa babu abinda bata raya mata akan abinda zata tarar Anita ta na yi a office dinta ba,ita dama taji a jikinta cewa Anita akwai abinda take nema a wajenta,daidai lokacin ta karaso office dinta inda ta na dora hannu a jikin kofar ta ji ta bude, bata tsaya wata wata ba ta faɗa office din, cak ta tsaya tana kallon.....