← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 57

Sashe 44

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ya kashe wayar aminatu ta ke kuka tana cewa"dan Allah daddy mu bashi komai ya bamu Nana, Daddy muna fa da babbar shaida wato Allah dan haka ba zai sa mu ji kunya ba"tana zuwa nan a maganar ta ta saki hannunsa da ta rike ta dauko littafin tana cewa kawai ka tashi mu kai masa ai mun gama karanta duk abinda muke da bukata ba wani abu ba ne dan mun bashi kaji daddy"rikota yayi jikinsa yana sauke numfashi a hankali,shiru ta yi tana jin yadda bugun zuciyarsa ke tafiya wanda anan kawai zaka gane r8kitaccen yanayin da mus ab din take ciki,take aminatu ta yi wani tunani, hakan yasa ta dago kanta daga kan saitin zuciyarsa tare da maida hannunta ta cikin rigarsa tana shafa kirjinsa a hankali,sai kuma ta yi saurin balle botiran rigar ta cusa kanta a kan kirjin tana sumbatar ko ina da ta ci karo dashi,cikin ikon Allah taji yanayin bugun zuciyarsa na sauyawa yana dawowa daidai, hannu ta sa ta zagaye shi duk da cewa bata rutsa shi ba,bakinta ta sanya ta sunbaci idanunsa wanda shima take ya marmarasu suka dawo aiki daga suman quick gadin da suka tafi,sosai aminatu ta yi kokarin fitar da mus ab daga cikin shock din da ta fahimci ya shiga,amma in dai ba mutum me tsananin kusanci ko fahimtarsa ba babu me gane hakan, wannan dalilinne yasa mus ab ya tabbatar da cewa ya samu mace mace ma zai iya bata suna da tafisu,yanzu kuma kallon mamaki yake mata, gata dai yarinya ba wata babba ba amma ta iya cire mijinta daga cikin bad condition,hannu ta kai kamar zata tsokal3 masa ido, wani dan guntun murmushi ya saki yana ji a ransa cewa da babu aminatu a tare da shi ya riski kansa cikin wannan tashin hankulan da tabbas duk karfin imaninsa sai ya shiga mummunan yanayin da sakamakonsa ba zai yi kyauba,tabbas mace ta gari i ta ce rabin addini karshen nutsuwa, ita kadai ta isa samar da i gantacciyar rayuwa me dauke da farincikin da yake tattare da sanin Allah wato yarda da jarabawa da kuma karfin imani,duk halin da ya shiga tun daga kan sanin waye shi har zuwa yau da mahaifiyarsa ta ke hannun da yasan tabbas zai aikata mata duk abinda ya faɗa,bai taba rikicewa ko shiga yanayi irin na raunin imani ba,idan har ilminsa ya bashi kwarin gwiwa to tabbas kadancewar aminatu a tare da shi ma ya bashi kwarin gwiwa.

Jin da yayi ana jansa ana nishi shi ya dawo dashi duniyar da aminatu da azzalumai irin su Abby suke,ware manyan idanunsa yayi a kanta, sannan ya kalli dogon hannunsa da take ja duk a kokarinta na son daga shi ya tashi,murmushine me taushi ya kuma subce masa a bazata,dan kuwa aminatun ta bashi dariya saboda ganin yadda ta hakikance bilhakki tana don dagashi,tana kuma jansa ya rinjaye ta ta dawo jikinsa gaba daya. take towel din da ta daura yayi takansa,da sauri ta sanya hannu ta kare kirjinta tana tura lips dinta da suka sha tsotsa wajen mus ab,janye hannun yayi yana kafe ta da lumsassun idanunsa a ransa yana fatan ko mai ya shige domin ya samu nutsuwar rayuwa da aminatu, rayuwa me inganci wadda take ciki da farin ciki da shauki da kuma mutunta juna, yana son yayi koyi da ma aiki wajen shimfida rayuwar aurensa bisa tsari da koyarwar ma aiki,"Muryar ta da ta kuma yin sanyi ya ji tana cewa " dan Allah daddy ka kirasa ka gaya masa zamu bashi kome duk abinda yake so amma kar ya taba Nana dan Allah"wayar kawai ya dauka tare da danna kiran Abby, wayar bata shiga ba, dan haka sai suka yi masa test suka tura masa, take kuwa ya dawo musu da adireshin wajen da zasu kai kayan sannan ya tabbatar musu da cewa sai ya duba ya samu komai lafiya Sannan zai saki Nana,sun amince da hakan.dan haka aminatu da kanta ta tattara duk wata shaida daga wajen mus ab sannan ta haɗa da littafin, tana gamawa ta kallesa ta ce"ka tashi mu je yanzu kar dare yayi"mus ab ya zama kamar wani soko duk abinda aminatu ta ce yayi yi kawai yake dan yana ji a ransa akwai wani abu da take boye masa shi yasa lokaci daya ta amince da sharadin Abby da kuma karfafa masa gwuiwa akan cewa in sha Allah sune da nasara.

A ranar sai da suka tabbatar duk abinda Abby ya nema sun bashi,abinda ya kuma bawa mus ab mamaki da aminatu shine,kai tsaye ta sanarwa da Abby cewa sun janye kara tunda yanzu babu wani amfaninta ba tare da shaidu ba,mus ab, ba ma abocin magana ba ne hakan yasa ya yi shiru sai dai yana cike da dokin ganin abinda da aminatu take shirya wa su Abby dan yasan ba zata taba kyale su ba,ko lefinsu bai kai wannan ba aminatu sai ta hukunta su, dan yasanta fiye da sanin da yayiwa kansa.

*****

Su Abby fa duniya ta dawo sabuwa,a yanzu jin kansu suke yi kamar wasu waliyay saboda tsananin sa a da da yadda kwallon duniya ya dawo hannunsu suke garashi duk inda suka so.

A bangaren dan ladi kuwa, Film kawai yake kallo a wannan gida,Gashi dai suna daure shida su ɗanturqui amma duk lokacin da su abby zasu bugo musu waya ko video Call dan su tabbatar dan ladi yana nan,sai abin ya juya, duk lokacin da hakan zata faru to zai ga su danturqui akan matsayinsu na baya,abin yana matukar bashi mamaki sai dai bashi da bakin tambaya.

Anita ma tunda suka bar garin suka dawo Kano, basu kuma waiwayar Gombe ba.

Zahida hankalinta fa har yanzu bai dawo jikintaba,saboda bata samu mus ab dinta ba,gashi dan nata ma anrab ta dashi ,saboda ita ko inda yake ma bata sani ba bare kuma gidan suhaima da yake can yana rayuwarsa cikin kwanciyar hankali, dan babu wanda baya waya dashi tun daga kan Nana har zuwa kan innawuro,daddyn sa ne ma da aminatu suke daukar lokaci basu yi magana ba.

Zahida ta bar batun Mus ab ne har zuwa lokacin da zata hadu da me ABM,ta tabbata idan kome nata ya dawo to mus ab ma dole ya dawo gare ta,dan kudi da power sune komai a wannan zamanin shi yasa bazata yi wasa da nemansu ba, kullum cikin irga kwanakin haduwar tasu take saboda yadda take jin labarin su ta tabbatar da cewa ita din me sa a ce.

...duk da cewa mus ab da aminatu sun tattarawa su Abby komai amma sai yaki sakin Nana , acewarsa ai nana matarsa ce dan haka yana da iko akanta,a karo na hudu aminatu ta kuma nemansa a waya,yana dagawa ya dura wani uban ashar yana cewa"wai ku yaran nan wane irin Mayu ne?karfa ku manta matar nan ina da yara da ita dan haka na fiku bukatarta, lamuni daya zan yi muku shine duk sanda kuke son magana da ita ku kirani ni kuma zan hadaku sannan duk abinda zaku fada a gabana zaku fadeshi idan ma so kuke ku ganta sai na baku dama, amma fa ku sani baku isa gano inda nake ba duk iskancinku da dabarunku wallahi nawa ya ci uwar naku,dan karku dauka bani da wayo na barku da nombata muna waya ku dauka cewa ban yi wani shiri akan hakan ba"dariya ya yi sannan ya dage girarsa daya tare da yi musu irin kiss din nan me sauti, runtse ido aminatu ta yi maganganun na dukan ranta,shi yasa duk sanda zata kirashi sai ta bari mus ab ya fita daga gidan dan tasan shi ba zai jure wannan iskacin na Abby ba, gyaran murya ta yi bayan ta yatsine fuska da dakin wani uban tsaki,kana ta ce"wai kai tsohon dan iska nan ka dauka duk abinda mu kayi maka tsironka ne ya sa mu kayi?ta wani girgiza kai tare da cewa lala lala,kawai dai akwai wani abu Nana kuma ka ci gaba da rike ta har nan da lokacin da zaka bayyana wa duniya kankan, wallahi Abby na dauki alkawarin sai ka tonawa kanku asiri da kanku tsofaffin banza da wofi kawai"daga haka ta katse wayar tana jiyar da kiranta ka wata nonber da ita da kanta ta tafa ta sannan ya fara magana cikin fillanci, to ango gun Ni dai kunsan ba iyawa nayi ba,dan haka ba san da waye aminatu ta yi waya ba,dan bata bamu wannan damar ba.

Kasancewar mus ab ya yi alkawarin ba zai kuma neman aminatu ba har sai bayan da suka samu nutsuwa, duk da bai san yaushe ba ne wane lokaci ne,a kusa ne ko a nesa ne? duka bai sani ba,abinda ya sani shine ba zai iya rayuwar aure da aminatu cikin rashin kwanciyar hankali ba,dan haka yasawa kansa hakuri dan ita kanta aminatun ya fuskancin wani abu a tare da ita,shi dai ya zuba mata ido ya kuma sakar mata da wuka da nama.

Sosai su Abby suke shirye shirye wajen hada kan costomominsu don harka zasu koma ka in da na in,yayin da a ta gefe kuma suke shirin kashe mus ab da aminatu ba tare da zahida ta sani ba,don sun tabbata sune kadai matsalarsu,baran ma da suka fara tunanin isma yana hannun mus ab din ,amma dai basu tabbatar ba,suna dai kan bincike ne kawai.

*****
Chapter 44 · 0% Book details