← Book details Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 57

Sashe 8

Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Adda zahida dan Allah kije ki gani wllh da gaske nake idan aka barsa nan gaba ba zai iya fitowa ba saboda girman abun da ciwon da yake masa, Kum.....bata iya karasawa ba saboda wani mugun naushi da zahida ta kaiwa bakinnata wanda take ya kumbura dan ita kanta zahida bata san lokacin da wannan karfin ya zo mata ba,jinta kawai ta yi a tsaye kan kafafunta, cikin fushi me tsanani ga wani irin bakin ciki mara misaltuwa, cikin fita hayyaci ta ci gaba da kaiwa aminatu duka da mari ta ko ina,bakinta kuwa har yanzu ya gaza furta ko kalma daya ne,aminatu kuwa Cikin kuka da son kare kanta daga dukan da zahida take ta kai mata tace "me yasa kike dukana dan kawai na taimakeki na fada miki halin da mijinki yake ciki haka kawai zaku kashe ni keda mijinki shi ya cinye min harshe ke kuma kin bugeni a labbana"wani irin ihu zahida ta Kuma sawa tana mai zubewa kasa sumammiya saboda kalaman da aminatu ta kuma yi dan kuwa gaba ɗaya abinda aminatu ta ke fada na shirme babu wanda zahida bata fassarashi ta kuma fahimceshi sa ba a matsayinta na wadda ta girmewa aminatu nesa ba kusa ba.

Larai ce ta hayo saman da gudu tana fadin "inna lillahi Hajiya zahida me kuma ya sameki?"aminatu zata yi magana kenan idanunta ya sauka akan mus ab da ya dan tokare ajikin kofar sashensa,fitowarsa kenan kuma duk abinda ke faruwa yana saurarensu dan kuwa mus ab Allah yayi masa kunnen ji sosai,fitowa ne kawai bai yi ba har sai da ya gama shirinsa tsaf cikin hadaddiyar cot dinsa Kalar sararin samaniya da nic dinsa baki fuskarsa babu abinda take sai walwali bakin kwantaccen sajensa ya kwanta tun daga gefe da gefen fuskarsa har zuwa karkashin habarsa inda ya tara dan gemun da ya kuma kawata surarsa ta cikakkun maza yan gayu da tsafta ga kuma kyawunsa na Fulani dan haka abin ya kuma hadewa ya bada wani kyawu na musamman me tsayawa a zuciyar yanmata,idanunsa tsaye akan aminatu yana mata wannan kallon nasa na kai tsaye wanda tuni ta fahimci cewa ita ka dai yake yiwa wannan kallon duk da cewa kallon nasa ba iri daya ba ne, a ko da yaushe yana mata kallo ne na daidai da yanayin da suke ciki, amma ta fi sanin ma'anar wannan kallon saboda duk sanda ta yi wani laifi shi yake mata kuma laifinta yafi zamanta lafiya yawa, daga shi kuma sai kallon da yake mata wanda take shiga cikin yanayin jin sanyi da mutuwar jiki kallon da ya fi shigar ta da tsuma ta har da taba zuciyarta,wancan kallon nasa komai yake haifarwa a tare da ita, sai dai kuma kash bata san komai akan yanayin ba kawai dai tasan cewa idan yayi mata wannan kallon to everything is wrong with you, janye idanunta ta yi daga kansa tana kallon larai da har ta ɗebo ruwa tana yayyafawa zahida,cikin natsuwa mus ab ya wuce yana zuwa saitin aminatu yayi kasa da murya sosai kana ya ce"idan kika kuma bude bakin nan kika yi magana makamancin wancan to sai na gutsure harshen gaba daya"yana maganar ya wuce abinsa tamkar bai san da mutane a wajen ba dan ita kanta aminatu badan tana kallonsa ba ba zata ce ya ma kalleta ba bare yakai ga yi mata kashedi,yana gama sauka zahida ta farfado dan haka bayansa kawai ta hango yana fita daga falon hannunsa dauke da yar karamar jakarsa ta laptop,yunkurawa ta yi cikin zafin Nama wanda hakan yasa aminatu ta kwasa da gudu ta sauka kasa tana cewa "wannan fa ina ga ta haukace aradun Allah idan na tsaya kaheni zata yi"aiko aminatu tayi gaskiya dan kuwa zahida bata bi mus ab ba, Dan tasan ba sauraren ta zai yi ba, karshe ma ya yi mata abinda zai sa mutuncinta ya zube gaban yan aiki, shi yasa kawai ta bi aminatun da mugun gudun da bata taba sanin cewa nauyin jikinta zai bari ta yi sa ba.

Da sauri aminatu ta banko kofar wanda hakan yayi daidai da zuwan zahida dan haka kofar bata sauka a ko ina ba sai akan goshinta ji kake Kum,da sauri zahida ta dafe gashinta da ta ji yana neman cirewa tare da lailayo wata muguwar ashar ta bankawa aminatu tana mai buga kofar dakin kamar zata karya dakin,goshinta kuwa tuni ya suntume tamkar me bisin kai, ta jima tana buga kofar tare da antayawa aminatun zagi kwando kwando.

Aminatu kuwa tana shiga dakin ta sa kuka tana neman maboya, cikin wardrobe ta shige tana cewa Khalid rufe dan wallahi ba zan tsaya wannan lutuwar uwar taka ta kashe Ni ba,dan haka gara na yiwa kaina kamshin mutuwa tun kafin na mutu a hannun iyayenka daga mai cinye min harshe sai mai dukana dan kawai anga ni marainiya ce,"ta karasa maganar da kuka har tana jan majina,"Khalid ya ce "adda aminatu idan fa na rufeki ba zaki shaki nunfashi ba kuma idan mutum baya shakar numfashi mutuwa yake yi"khalid rabu dani kulleni kawai idan Allah yayi zan hadu da dan birni to dole sai na rayu"Khalid bashi da wani dogon tunani dan haka ya rufe aminatu kamar yadda ta bukata ya samu waje ya zauna yana sauraron muryar maminsa da bugun da take yi.

Gajiyar da ta yi ne yasa ta hakura da bugun, larai tasa ta dauko mata jakarta da sauran tarkacenta ta fita a fusace ba tare da ta duba yanayin da take ciki ba,dan sam bata san yadda goshinta ya koma ba,ya kumbura yayi suntum fuskarta tayi tsayi gashin yayi tsayi sai kyalli yake yi,tun daga harabar gidan securities duk wanda ya kalleta sai ya sunkuyar da kai yana rike dariyarsa,tana fita kuwa suka samu aikin yi.

Kai tsaye hospital ta nufa zuciyarta na wani irin zafi da jin tsanar aminatu kamar ta kasheta tun yanzu ba tare da ta jira umarnin iyayenta ba.

Fyadam ✍🏾
[4/15, 5:42 PM] yushauadamfatima: *Typing*

💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

``` *Page35``*

Zahida na fitowa daga mota,kowa ya zuba mata ido,mutane yan jinya wanda basu san halinta ba kai tsaye suke mata dariya, wanda suka san halinta kuwa basa iya yi sai sai su sunkuyar da kansu kasa ko su kauce daga wajen suna dariya,tun zahida bata fahimta ba har dai ta fahimci cewa da ita fa suke yi,abin ya bata mamaki shin me ye abin dariya a tare da ita,dube dube ta shiga yi a jikinta sai dai bata samu ko mai ba,har ta isa office ɗinta tana ta faman duba jikinta,dan ko kallon inda masu gaisheta suke bata duba ba bare ta yi musu kallon da ta saba yi musu idan sun gaida tan,tana shiga ofishin kai tsaye ta wuce gaban madubi dan ganin abinda yake tare da ita har wasu banzaye kaskantattun mutane suke yi mata dariya,isheta wajen ke da wuya ta kurma ihu tare da zubewa kasa tana mai sakin wani kakkarfan kuka me tsananin ciwo,wai yau ita zahida mutane suke yiwa dariya akan canjin fuska kawai da ta samu,to idan har mutane za su yi mata dariya dan sauyin kamannin da ta samu to me zasu yi mata idan har ta bari kudi da suka bar hannunta, wannan alamu ne da suke nuna mata na cewa idan har ta bari kudi suka kwace mata to tabbas mutane jifanta zasu dinga yi suna dariya da nuna ta da hannu,da sauri ta share hawayenta tana cewa, zahida kar ki yi kuka, yanzu ba lokacin kuka ba ne lokacin kawo karshen aminatu ne lokacin samun kudi da pawer ne, dole ne aminatu ta biya bashin wannan abun da jininta,ko ta halin kaka sai tayi kudi da wani sashe na jikin AMINATU.

Mikewa ta ya da sauti kamar wadda ta tuna da wani abu tare da figar jakarta ta fi ce daga office din ranta a matukar bace,dole masu kallonta suna dariya suka koma sunkuyar da kansu saboda yadda suka ga fuskarta ta koma irin ta bosa bosan nan masu ban tsoro,motarta ta shiga ya kwasheta da wani matsiyacin gudu,ko masu tsaron gate ɗin sai da suka tsorata dan dan sun yi zaton tasu ta kare saboda saura ƙiris ta take su da motar Allah ya taimake su suka janye kofar cikin zafin Nama.
Chapter 8 · 0% Book details