Sashe 1
Matar Dan Birni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
[4/12, 7:00 PM] yushauadamfatima: *Typing*
💕
*MATAR ƊAN BIRNI ** 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
``` *Page31``*
Har misalin ƙarfe ɗaya Anne ta kasa runtsawa saboda yunwa ga kuma bakar zuciya ta ki yiwa kowa magana, har fitowa tayi lokacin basu jima da cin abinci ba ta yi shawagi wai ko Nana zata ganta ta tuna bata kawo mata abinci,ba amma shiru kake ji, dan ita Nana bata ma kawo wannan tunanin a ranta ba sam,aminatu kuwa dauke kai take tana dariya a a fakaice dan sarai ta fahimci shawagin Anne ba akan komai ba ne sai akan adda'am,a ranta cewa take ai tsohuwa tunda kika sake na gane kaunarki da abinci to kuwa kin shiga tara tsohuwar kawai.
Haka ta gama shawaginta ta koma daki tana faman zuba ƙwafa cikinta kuwa banda kugin yunwa babu abinda yake, duban agogo Nana ta yi kafin ta dawo da dubanta kan Khalid dake kwance kan cinyar aminatu, sannan ta ce,"aminatu ku je ku kwanta kunga dare yayi kar ki kasa tashin dare",shafa tattausar sumar khalid aminatu ta yi tana cewa ,nana wane dare kuma?ai dare ya riga ya gama yi shi yasa ba zan kwanta ba sai nayi sallolina dan kar na kasa tashi karfe biyu"mikewa Nana tayi tana cewa "to hakan yayi Nima bari na yi amfani da dabarar ki na fara yin sallar kafin na kwanta"to Nana Allah ya tashe mu lafiya yau tare da Khalid zamu kwanta kwana biyu na yi kewarsa saboda tafiyar da yayi gidan adda suhaima",to shike nan Amin"nana ta fad tana taka matakalar step biyar da zai kaita bangaren dakinta.
Sai da aminatu ta tabbatar da cewa Nana ta yi balance a dakinta, sannan ta kwantar da Khalid a hankali, tashi ta yi ta nufi kiching, tana shiga ta dauki kayan abincin Anne ta fita da shi ta baya ko tsoro ba ta ji ba ta kaiwa security da yake gadin main kofar da zata sadaka da cikin gidan baki daya,tana dawowa ta kwanta a kujera tana ci gaba da kallon tashar aljazira da suke karanta Alkur'ani me girma,a hankali take bi cikin daddan sautinta tana yi tana kallon gefen hanyar dakin Anne, Dan ta tabbatar sai ta fito neman abinci a yadda dai ta fahimci zaryar da take.
Hasashen aminatu ya tabbata dan kuwa Anne ta hango cikin sanda kamar wata ɓarauniya,ta fito daga dakinta,da sauri aminatu ta rufe idonta kamar me bacci,sai dai tana kallon Annen.
Hanyar kiching Anne ta yi cikin sanda kamar ɓarauniya dan yasa a ranta ko da zata ci abincin nan to bata son wani ya sani bare idan ta ce bata ci ba a ƙaryata ko kuma idan ta kwanta jinya,sai da aminatu ta tabbatar da shigar anne kiching ɗin sannan ta yi sauri ta miƙe tare da nufar kiching ɗin,bata bari ta yi takun da Anne zata Ankara da shigar ta ba, shi yasa ganin aminatun ya matukar razana ta dan bayan kunyar da ta ke gudu har da tsananin tsoro, take ta diririce, cikin in ina take cewa,"en dama bera ne na gani nake son neman madoki na bigesa dan kin san Ni fa a rayuwata bana son bera, da na ga bera gwara na ga maciji ina matukar jin tsoron bera, shi yasa idan naji motsinsa bana iya zama a wajen"rike kugu aminatu ta yi kafin cikin son boye dariyarta ta ce,"duk tsoron da kike masa shine kuma zaki iya kasheshi?to ma wai ta ina bera ya shigo gidan nan ne?gaskiya dai anne kin iya zubota sai dai idan da abinda ya kawo ki daban amma ba dai batun bera ba",kallonta anne ta yi cike da tsarguwa da masifa taf baki ta ce,"to dan ubanki me nazo nema? idan ma wani abun na zo nema ai gidan dana ne ba na ubanki ba ko?" Tura baki aminatu ta yi cikin gunguni take cewa "uban aminatu bawan Allah ne dan haka a daina zagar munshi",har Anne zata daga murya sai kuma ta tuna hakan yana nufin fallasa halin da take ciki ne,dan haka ta rufe bakinta tare da barin kiching ɗin a fusace cikinta kuma na karar yunwa fadin rai kuma ya hanata ta tambaya.
A wannan dare dai haka Anne ta kwana da yunwa,ba dan taso ba karshe akan aminatu ta huce duk da cewa bata san cewa ita ce me shiryawa da bada umarni ba,haka ta kwana tana tsinewa aminatu da ahlinta.
Kafin safiya tuni Anne ta jigata,Nana bata tashi sanin halin da ake ciki ba sai da ta je gaida annen ta ganta kwance tamkar wadda ta yi jinyar wata biyu,numfashi kawai take iyawa dan ko sallah asuba a zaune ta yi ta,da sauri Nana ta karasa gaban gadon saitin kanta tana cewa "subhanallahi "anne baki da lafiya ne kuma baki fada ba?"Anne da take jin cikinta kamar zai hade da bayanta ta yi saurin kawar da kanta gefe cike da fushin da yake Kuma taso mata tana danne zuciyarta,jin ta yi shuru karshe ma ta rufe idonta yasa Nana shiga tashin hankali duk a tunaninta zafin ciwon ne,dan haka ta yi saurin juyawa tana cewa bari na kira Abbyn su a kira likita tunda Zahida bata nan",jin haka yasa anne saurin riko hannunta sannan cikin muryar da ke nuna bacin rai ta ce"kar ki kira min kowa tunda ba damuwa yayi dani ba bare ke da bani na haifeki ba,bai san ya na ci ba bai san ya nasha ba,shi dai kawai tunda ya ajiye a dafa a bani gani yake ya fita HAKKINA"matse kwalla ta shiga yi tana ci gaba da cewa, "shi yasa kullum sai nayi kewar ya mace, tabbas na yarda da yan magana da su ke cewa da ka haifi gwamna gwara ka haifi matar gwamna sannan yaya mata rahma ne, duk wanda bai samu rabon mace ba zan iya cewa bai gama more haihuwa ba", zama nana ta yi a gefan gadon tana cewa "dan Allah anne ki yi hakuri ki daina fadin haka Ni ma ai yarki ce,dan haka ki fada min damuwarki?"
Matse kwalla Anne ta kuma yi sannan ta ce,"yanzu kamar ni ace an manta da bani abinci a cikin gidan nan sai haka na kwana ciki fayau, ko bacci kasawa nayi saboda azabar yunwa"salati Nana ta sa tana tafa hannuwanta kafin cikin mamaki da damuwar da ta bayyana a kan fuskarta, ta ce,"yanzu Anne kina nufin AMINATU bata kawo miki abincin da na ce ta kawo miki ba"? Cike da fusata Anne ta ce "yo ta kawo min zance banci ba ne ki ji wata banzar tambaya"ganin ta harzuƙa yasa nana ta fara rarrashinta tare da sanar mata yadda sukayi da aminatu akan kawo mata abincin,daga karshe da kanta ta je ta haɗo mata lafiyayyan karin kumallo ta kawo mata, sannan ta sata a gaba kamar karamar yarinya, sai da ta tabbatar ta ci ta koshi sannan ta fita daga dakin dan zuwa ta samu aminatu ta ji dalilin wannan masifa da ta kusan Kunno mata.
AMINATU yau ko fita karin kumallo basu yi ba, kiching ɗin sama wanda ke bangaren mus ab ta shiga tana haɗa musu breakfast,hirarsu suke cike da na nishaɗi ita da Khalid, "Khalid wai dama haka Anne take tsoron bera da yawa?"aminatu ta yiwa Khalid tambayar tana juye ruwan shayi a flax,dariya Khalid yasa dan duk sanda ya tuna karon Anne da bera sai yasha dariya,sai da yayi me isarsa sannan ya bawa aminatu amsa da cewa,"wallahi adda aminatu Anne tana tsoron bera kamar ya kashe ta, ita kuma momyna mage take tsoro kamar me dan idan ta ga mage kamar zata shide haka take yi"jinjina kai aminatu ta yi sannan ta ce"shi kuma uncle isma me yake tsoro wanda idan ya gansa zai iya fitsari a wando"?kai tsaye Khalid ya bata amsa da cewa,"kyankyaso"daga nan aminatu bata kuma cewa komai ba sai saka abinda zata fanshe rashin mutuncin waɗannan mutane Uku da take a ranta,Khalid ne ya dinga kai musu kayan ƙaramin falo yana jerewa, daga karshe aminatu ta fito ta dauko kunun kabewa da madara da ayaba da zuma da dabino, da ya zama abincinta, dan tun da ta fara tasawa Nana ta sabar mata dashi har ma da wasu abubuwan da har yanzu aminatun bata fahimci dalilin bata su da Nana take yi ba,tana sha ne kawai dan azabar dadinsu da take ji hatta da ruwayen da take sha daban suke da na gidan watsu tsimi ne na musamman da Nana take yi mata masu dan karen dadi, daukar kofin da ta cika shi da hadin kabewar nan ta yi ta juya zata fita sai hannunta ya bigi cabet din kusa da ita take kunun kabewar yayi tsalle ya fallatsu a fuskarta har zuwa kirjinta kasancewar wata yar bulawus ce me faɗin wuya a jikinta kuma ba bra a jikinta, shi yasa kai tsaye kunun ya tafi zuwa cikin wuyanta ya bata kirjinta sosai,