Sashe 8
Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
"Inna.! inna..!
"Na'am ohni fatuha wai yaushe zaki girma ne Dan Allah? mutun shekara goma shad'aya amma mutun kullun girma yake yana cin qasa"
"yi hakuri inna wallahi zanina nake nema inna, wanda baba jummai ta siyo min abirni"
"ah yau antuno da baba jummai kenan to zanin yana uwar d'aka na" Washe baki tayi ta ce, "eh inna Qur'an na matsu ta zo kwarankwatsi inna"
"ai zata zo insha Allah aikin san duk qarshan shekara ta ke zuwa, amshi kwanan ki kaima Baffan ki kinji"
"to inna.! Baffa na zaune saman tabarma ta aje masa kwanan tare da gaishe shi washe da baki ya amsa da cewa, "Fatuha yan'mata.! rufe fuskarta tayi ita ala dole kunyar Baffa take ji tana wani sunne kai ta ce, "Qur'an Baffa ni ba yan'mata ba ce su Tanine yan'mata" yar dariya Baffa yayi ya ce, "alalai d'iyar Baffan ta ke ma ai yan'mata ce, matso mu ci abincin tare nasan baki ci ba saboda baki iya cin abinci ke kad'ai, kuma inna nasan batayi kalaci ba.
"toh Baffa matsowa tayi tana cin abincin inna ta shigo washe da baki tana cewa, "Kai dai Malam baka gajiya da shagwa6a fatuha da girman ta amma har yanzu tare kuke kalaci baka bari muci tare"
"ah ke ma in zaki ci ki zo muci nasan kishi kike mun ware ki ke kad'ai" murmushi inna tayi ta zauna suka cigaba da kalacin..
****
Misalin karfe 1:00pm flight d'in su Alhaji ya sauka Kano, a hankali yake takowa ta matatakal jirgin da ka gansa kaga babba mutun sanye yake da shada blue babba riga anmata aiki da dark blue zare sosai d'inkin ya haushi yayi kyau.
sadiq na jingi ne jikin motarsa black Benz kasancewar shi ya zo d'aukar Abba, qad'an-qad'an ya duba agogo d'ago kai yayi yana kale-kale can ya hango Abba washe baki yayi ya qarasa da sauri ya rugume Abba ya ce, "I miss you.!
"Miss you more Son" tare da shafa masa gefan fuskarsa bud'e masa murfin moto yayi ya shige shima ya zagaya ya shige driver ya jasu.
Mom ce zaune a bedroom saman sofa tasha danqareran leshin ta green mai ratsin white flowers, anmata bubu da leshin mai kyau tasha d'auri ture kaga tsiya gashin ta ya leqo sai kamshi ke tashi ba qaramin kyau tayi ba.
dai-dai parking space driver yayi parking Alhaji ya fito shida sadiq yaran sadiq sai qamewa suke tare da kwasar gaisuwa wajan Alhaji, Washe da baki suka shigo gidan cikin sallamar su, Jidda da ke zaune a palour suna wasa da Jamal qanin Hanan d'an Bilkisu, da gudu Jidda ta rugo wajan grandpa ta rungum sa ita da jamal d'aukar su yayi yana cewa "Ah'ah my little grandchildren kun girma musanman angel, Angel me daddy ke baki? kin qara girma" Dariya tayi ta ce, "grandpa kullun daddy sai ya bani fresh milk da safe"
"good girl yanzu kin fara cin abinci kenan? washe baki tayi.
Mom ce ke takowa downstairs a hankali d'auke da murmushi a fuskarta, A hankali alhaji ya daga kai ya hadiya wani miyau mukut yana binta da mayen kallo (ohni salma tsohuwar zuma tatashi lol) Katse masa tunani tayi ta hanyar cewa, "Abban sadiq sannu da zuwa"
"Yauwa"
ya hanya?
"Alhamdulillah"
kun zo kun fara cika grandpa da surutu ko? Cewa aunty bilki da fitowar kenan daga bedroom washe baki su kayi su duka Anuty bilki ta ce, "oya ku wuce kuyi wasa"
Hanan ce ta zunboro baki ta ce, "Momi nafa girme su ni ai bana wasa"
"Toh yayi uwar mata"
Mom ta bushe da dariya tare da jan hannu alhaji suka wuce bedroom.
Ita da kanta ta taimaka masa ya cire kayansa ya shige wanka inda yake ta zuba mata soyayyya.
After 1hour Alhaji ne ke sakowa daga stairs shi da Mom sanye yake da jalabiya milk ya fito sak bafulatani glass na manne a fuskarsa dining area suka wuce lokacin kowa ya halara.
Mom ta jaa ma Abba kujera ya zauna itama ta zauna, Mom ta fara serving nasu lunch cuscus ne da miyar dankali taji kaji sosai aciki sai lafiyayan so6o mai sanyi ta zuba ma Abba cikin nutsuwa suke lunch inda sadiq ke feeding Jidda da Jamal.
****
Bayan sun gama kalaci fatuha ta kwashe kwani kan ta wanke, ta wuce gidan su fatsima suka wuce rafi, tafe suke suna tsokana dan har yanzu da suka fara irgandangi ba dai tsokanar su kayi ba, fatsima ce ta ce, "Fatuha kalli wancan ba d'an maigari bane da kandala"
"Qur'an shine ta6 aiko ya ja ma kanshi tona asiri taho mu qarasa"
Dan mai garine da kantala mai tallah suke aikata masha'a bayan bishiya da sauri su fatu suka qarasa cikin d'aga murya fatu ta ce, "asirrin ku ya toni bilahilazi kamar a gaban mai gari" cewar fatuha bala cikin sauri ya fara maida zariyar wandon shi yana zare ido kandala ta fara gyara riga zata d'au tulun ta .. Fatuha ta kada baki ta ce, "Qur'an ba inda zaku mun kama kwartaye ehe"
"keeee!! Ni sa'an kine zanci uban ku fa yana magana cikin borin kunya
Yar shewa fatu tayi ta ce, "bilahillazi Bala ka raina mana wayau mun Kama ku kuna iskanci shine dan baka da kunya zaka zagemu, toh Qur'an sai mun tona, dama rana nan na d'auki gyadar kandala tamin raini wayau to zan je na fad'a ma malam abinda kike in kin fito tallah..! Kwala kandala ta fara matsewa tana ba ma fatuha hakuri shima bala haka har ya masu Alqawarin zai basu murtala sannan suka hakura, suka tafi suna dariya.
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Blood sister deeja
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
17_18
After lunch sadiq ya kwashi su jidda da Hanan da Jamal zuwa shan ice cream sosai sunje yawo daga nan ya wuce dasu munjibir park, cikin jin dadi suke wasan su duk inda ka kalla a wajan yara ne da manya ke hutawa har ma turawa, resting chair ya samu ya zauna yana Kallan su Jidda yadda suke wasannin su cikin nishad'i daga nesa kuwa yan'mata sai yaba kyansa suke da tsarin shi wasu mamaki su kar dai ace duk yaranan nashi ne, dan iya kar haduwa sadiq ya hadu wasu ma sai jan su Hanan suke a jiki dan su samu damar yi ma sadiq magana ganin ba wasa a fuskarsa ya suka hakura basu suka bar munjibir park ba sai gab da magrib.
Dai-dai parking space yayi parking ya fito riqe da hannu jidda, Jamal kuma na kafadar sa yaran shi yayi ma alamar su kwaso kayan dake cikin motar su biyo shi da su, haka ko akayi suka kwaso kayan ba komai bane sai kayan zaqi kala-Kala da teddys da kayan wasa da ya saima su.
Anuty bilki na zaune a parlour saman three star Hanan ta rugo take fada jikinta ta ce, "Momi.!
"yeee yan'matan Momi sun dawo" bata ida rufe bakin ta ba sadiq ya shigo yana Cesar, "Ah sister ke kadai ce a parlour Mom fa?
"tana part din Abba"
"ok.! ina baba jummai?
"Tana kitchen"
"ok Hanan kira min rabi'a ta amshi kayanan ta kai maku su d'akin angel"
"OK uncle" rugawa tayi kitchen ta Kira rabi'a.. sanye take da farar riga mai dogwan hannu sai mini skirt da alama wannan kayan unform ne na yan'aiki.
Har qasa ta duqa ta gaishe shi tare da amsar kayan ta wuce da su bedroom d'in Jidda sadiq ya ce, "sister ni zan wuce masallaci may be sanda zan dawo kin tafi"
"Ai kwana zanyi a gida" waro ido yayi ya ce, "Gidan naki fa" yar shewa aunty bilki tayi ta ce, "ka manta mai gidan baya nan sai gobe zan koma"
"oh haka har yanzu bai dawo ba?
"eh.!
sannan sadiq ya sa kai ya fi ce zuwa masallaci.
*****
Duk wata gona dake da bishiyar mangwaro sai da suka leqa suka tsunko nunanu, daga nan suka biya wajan shafi'u mai rake suka amso bashi, acewar duk sanda bala dan mai gari ya basu murtala zasu biyasa bayan sunyi tafiya mai nisa fatsima ta ce, "Kai wallahi na gaji"
Fatu ta ce, "ai sai da nace maki mu zubar da ruwan tulun mu zuba mangwarayan mu cikin tulun, idan mun koma gida sai muce biyo mu akayi muka fasa dibar ruwan"
"kwarankwatsi ke dai fatuha wayau gare ki amma kinsan wani Abu"
"a'a saikin fada.!
"qara muje da ruwan Qur'an saboda mun dad'e"
"Haka kuma fa ga wancan Malam D'alha d'in sai sauri ya ke yaje ya fara zalinci"
"ke dai bari" ta qara gyara tsayuwar tulun ta
"kinko iya qarin jiya fatuha?
"hehe yo tun yaushe na iya shi, Ke nifa Malam D'alha ne baimun ba shiyasa bana bashi hada amma Qur'an na iya"
"toh bilahillazi yau sai kin bashi saboda yau ban shirya ma bugu ba, Ko bishiyar nan da muka hau na maqale duwawuna sai zinga yake" Fatuha ta kwashe da dariya ta ce, "Sai ki je gida kiyi gashi da ruwan d'umi Inmaki na maitafasa"
Cikin sallama ta shigo gida inna ta amsa, Inda Sabo ya kamata ta saba da wannan baqin halin na fatuha in ta je d'iban ruwa sai ta shekara bata dawo Ba.
"Inna Ina abinci na?
"yana madafi" kwanan samira ta jawo tuwo ne miya kuka yasha manshanu sai kamshi yake loma daya zuwa biyu tayi, fatsima tayi sallama cikin shirin ta na zuwa makarantar allo, tare suka zauna suka ida cin tuwo zata d'au hijabin ta kenan inna ta leko daga uwar d'aka ta ce, "yanzu saboda Allah fatuha sai na ce kiyi wanka zakiyi kome? raban ki da wanka tun shekaran jiya wuce kiyi wanka nan ku tai makarantar" baki ta turo gaba tana dire-dire "gaskiya inna ki bari sai na dawo nayi"
"Aifa baki fita sai kinyi wanka"
Da kuka da komai fatuha tayi wanka sannan ta fito suka wuce makaranatar allo.