← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 67

Sashe 24

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bedroom ta dire jidda ta shirya ta cikin uniform din ta, sannan ta raba mata gashin kanta gida biyu taja hannun ta suka wuce dining area, Mom da Abba na zaune a dining area cikin nutsuwa ta qaraso ita da jidda ta gaishe su cikin ladabi a tare suka amsa tare da yimata ya jikin, washe da baki tace da sauki jidda ta jama kujera ta zauna sannan ta fara saving nata tana cikin saving nata sadiq ya qaraso dining area gaishe da su mom yayi tare da yi masu peck, sannan ya samu kujera ya zauna masha Allah ya sha kyau har ya gaji, kallo daya fatuha ta masa ta kauda kai cikin tsanarsa amma duk da haka sai da ta yaba kyau irin na sadiq har mamaki kyan sadiq ke bata, anya akwai wanda ya fishi kyau kuwa ta jefawa kanta tanbayar, musanman yau da yake sanye da manyan kaya yayi matukar kyau da kwarjini, tunda ta zo gidan yau ce rana ta farko data fara ganin mai kyau da manyan kaya shada ce sky blue yasa tasha dinki da dark blue zare anmasa irin dinkinnan na sarauta sai hula blue mai ratsin dark blue da kafa ma kansa ta zauna d'ansa, hannu ya kai ya d'au cup ya fara hada tea dan shi mutun ne ba mai san yawan cin abinci ba, bayan ya gama hada tea ya fara sha a hankali Mom ce ta kalle sa tare da cewa, "baby karka ce min yau ma tea kadai zaka sha? lagwabe kai yayi ya ce, "eh..!
"haba baby wai me yasa baka san cin abinci ne uhm" Abba da ke gefe ya ce "Sai kace ba soja ba sojoji da aka sani da cin abinci" shagwabe fuska yayi ya cigaba da shan tea din ganin Mom nata magana yasa shi cin chips din kadan fatuha sai da tabatar jidda taci ta koshi sannan ta kyale ta bayan sun kamala cin abincin sadiq ya dau jidda fatuha na biye da su da lunch box har bakin mota, sannan jidda ta mata peck ta shige mota juyowa tayi ta shigo gida da su Abba ta ci karo Mom ta rako shi riqe da briefcase din shi wuce su tayi ta koma dining area chips ta zuba ma kanta a plate da farfesun kifi bata wani ci da yawa ba saboda har yau bakin ta ba dad'i bayan ta kamala ta fara kokarin kwashe kwanikan, Mom ce ta shigo dauke da fara'a a fuskarta ta ce "Haba fatuha ke da baki da lafiya ina ke ina aiki ki? zauna ki hutu" washe baki fatuha tayi tana qoqarin yin magana Mom ta hanata kwalawa rabi'a kira tayi cikin ladabi rabi'a ta qaraso ta d'urkusa har kasa ta gaishe da Mom Mom ta ce, "yawa rabi'a kwanikan nan zaki kwashe sannan yau ki je ki gyara part din sadiq, saboda fatuha bata jin dadi har" cikin zuciyarta rabi'a bata so Mom ta ce ta gyara part din sadiq ba saboda basa wani shan inuwa daya jiki ba qwari ta kwashe kayan dining area din fatuha kuwa daki ta koma tasha magani bata wani dadi ba bacci ya kwasheta.

A cikin school yayi parking din motar shi tare da zagayowa ya budewa jidda murfin mota, ta fito lunch box din ya miqa mata tare da yi mata peck a kumatu ta ce, "daddy am going to miss you"
"I now angel karki damu anjima idan an tashi ni zanzo daukar ki kin ji angel" murmushi tayi tare da yi masa peck ta shige class yana kallon ta har ta shige, shi kuma ya wuce wajan aiki cike da kaunar diyar tashi.

Ba ita ta tashi daga bacci ba sai karfe 11:30pm ita kanta tayi mamakin baccin da tasha, toilet ta shiga tayi wanka ta fito tare da shafe jikin ta da lotion wardrobe ta bude ta ciro atamfa brown mai ratsin black n white atamfar ta hadu riga da skirt dinkin ya mata kyau sosai y'all zauna a jikinta tamkar an aunata qarewa kanta kallo tayi ta cikin dressing mirror, murmushi ta saki tare da cewa, "gaskiya birni tayi dubin yanda na koma kamar ba fatuha inna ba.! duk wannan zancan tana yinshi ne a zuciyarta, murmushi takara yi tana qoqarin kama gashin kanta bud'e kofar da akayi ne yasa ta saurin waigowa a tunanin ta Jidda ce sai taga Hanan washe baki tayi tare da cewa, "Hanan..! cikin fara'a Hanan ta qaraso dakin sanye take da lace sky green mai ratsin black sai veil dinta white ba qaramin kyau tayi ba ta fito yan'matan sak, zama tayi saman bed tare da cire veil din ta ce, "wash na gaji wallahi" dariya fatuha tayi take ce, "wai kin gaji, aiki me kikayi da kika gaji? murmushi Hanan tayi tare da cewa "Kai fatuha karki ce min wannan uban gashin naki ne?" fari da ido fatuha tayi ta ce, "na Hanan ne.! bugu Hanan ta kai mata cikin wasa ta ce, "kai amma fa kin ji dadi" murmushi fatuha tayi ta ce "Ina Jamal da afra?"
"suna parlour tare da grandma nima tanbayar ki nayi sai grandma ke ce min baki ji dadi ba, shine fa na shigo na maki sannu toh ashe har kin warke kin fara make up" ta ida zancan cikin tsokana, dariya fatuha tayi ta ce "Wallahi naji sauki danma Mom bata barni nayi aiki ba"
"ai ta kyauta wallahi"
"amma yau baki je school ba?
"eh exam muke na JSCE shiyasa ban je ba yau bani da paper Jamal kuma fever yake shiyasa," murmushi fatuha tayi take ce, "ni wallahi ina san makarantar nan sai ma na shirya jidda zata tafi sai naji kamar na bita"
"ai karutu akwai dadi akwai wahala kiyi ma Mom magana mana" smile fatuha tayi tare da cewa toh jidda ce ta shigo bedroom din ta fada jikin fatuha murmushi tayi ta ce "Yan makaranta har andawo kenan?" daga mata kai jidda tayi ta "eh Anuty kin ga daddy ya siyo min ice cream da zamu dawo har da chocolate da yawa kuma fa naba daddy naki ya aje mana" murmushi fatuha tayi ta ce toh a zuciyarta kuwa cewa tayi ta6 wannan daddy naki ai sai ke Hanan ce ta katse mata tunani da cewa bari naje wajan uncle nima na amshi nawa tana fadin tana qoqarin daukar veil din ta zata fita ta ce, "fatuha idan kin gama shirya jidda ki same ni a parlour muyi lunch" toh tace mata bawai dan tasan me Hanan ke nufi da kalmarta na qarshe ba daukar jidda tayi ta shige da ita bathroom ta wanke ta tas sannan suka fito ta shafeta da mai tare da samata gwon pink mai qaramin hannu sai gashinta da ta gyara mata tayi kyau sosai masha Allah.

Direct parlour suka fito Anuty bilki na saman two sitar zaune, Mom na zaune saman three sitar suna kallo gaishe su tayi Mom tayi mata ya jiki ita da Anuty bilki da gudu jidda ta koma wajan Jamal da ke zaune saman daya daga cikin kujerin dining area itama ta zauna cikin fara'a fatuha ta qaraso ta fara saving din su, Hanan dake saukowa daga upstairs tana zunburo baki gaba cikin bacin rai ta qaraso dining area din fatuha ta kalle ta ta ce, "Lafiya naga kamar an bata maki rai ? dan guntun tsaki taja ta ce, "wallahi uncle ne ya bata min rai shi kullun cikin bakin rai maganar arziqi ba taba hada ku dashi" murmushi fatuha tayi ta ce "Yi hakuri kinji zauna mu ci abincin mu idan mungama mu fita farfajiya shan iska"
"yauwa tawa..! abinci suka ci cikin nishadi bayan sun gama fatuha da Hanan suka kwashe kwanikan sunka kai kitchen sannan suka fita farfajiyar gidan domin shan iska.

Saman resting chair suka zauna, suna dan taba hira fatuha ba qaramin jin dadi gurin take ba saboda har da yan shuke-shuke lumshe ido tayi ta ware su Hanan ta ce, "kai fatuha karki ce min wai bacci kike ji"
"ah ba bacci nake jiba kawai wajan yamin ne ina san guri kamar haka, shiyasa sanda nake akauye kullun muna bakin rafi ni da fatsima" murmushi Hanan tayi sun dade sosai a filin gida suna hira kiran sallah magrib ne ya tashe su a wajan suna tafe suna hira, sadiq da ke qaqorin fitowa zai je masallaci sanye da jalabiya milk fatuha bata lura da mutum ba tayi kansa ba tayi masauki ko ina ba sai saman fafad'an kirjinsa rintse ido fatu tayi tana zare ido tayi lamo a kirjinsa tana jira taji saukar aradu saboda tuni hancinta ya mamaye da kamshinsa, wata iri tsawa sadiq ya daka mata wadda yasa yan hanjin ta katsawa tayi baya zata fadi ya tarota cikin zafin nama idanusa waje kamar yarda fatu ta zaro nata duka waje kirjinta na bugawa da sauri da sauri, sakinta sadiq yayi da sauri Hanan ko take ta kama gefe jikin fatuha ta rabe, harara ya aika masu su duka cikin 6acin rai ya ce, "stupid girl's kuna tafiya kuna kalle-kalle baku kallon gaban ku mtss..! sannan ya sa kai ya fita, sauke ajiyar zuciya Hanan tayi ta ce, "ba dai jaraba ba mtss, sannu fatu indai uncle ne haka yake kullun cikin bakin rai da hargowa" fatu data dauke wuta na wucin gani murmushi tayi ta ce, "ni zan fada maki haka..! sannan suka shige cikin gida.

Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
    Raheenat

http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

                        47_48
Chapter 24 · 0% Book details