Sashe 47
Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda safe fatuha ta tashi ta shirya cikin riga da sket dinta na atamfa yellow mai ratsin white a jiki masha Allah kayan sun hauta sai dai fuskarta tayi fayau, bayan ta kamala ta fito parlour cikin nutsuwa ta gaida Mom da Abba dake ta break angel na gefe itama ganin bata ga sadiq ba yasa gaban ta ya qara faduwa a karo na biyar jiki ba qwari ta zo ta hada tea kurba biyu zuwa uku ta aje Mom ce ta ce, "Fatuha har kin koshi?
"eh Mom dama idan zan yi tafiya bana wani cin abinci" to Mom tace, sannan ta qara da cewa, "ga driver nan zan had'a ku da shi idan ya kai ki yau zai maido ki, ki gaida mutun gida sannan idan kin isa ki kira ni ki fada min" lagwabe kai fatuha tayi ta ce, "Mom ai jiya wayar ta lallace"
"garin yaya?
"fadowa tayi daga saman dressing mirror ta dauke"
"eyya to bari na baki baby Nokia idan kin dawo a sake wata" to fatuha tace tare da shi ga daki ta dauko sim dinta, miqa mata wayar Mom tayi ta zura sim dinta ciki har ta kai bakin kofa ta dawo ta haurawa sama part din sadiq ta nufa a hankali ta murda handle din kofar taji kule gam tsoro ne ya kamata amma ba yadda ta iya haka ta dawo, tare da yima mom sallama angel ko sai rigama take sai tabi fatuha Mom ta hana.
Shigewa mota tayi driver ya harba da su kan titi cikin dan qanqanin lokaci suka isa wudil, cikin kwatancan fatuha har driver ya kawo ta gida fitowa tayi a hankali tana qare ma gidan su kallo gabaki daya gidan ya canza a yadda ta san sa, mamaki ne ya bayana a fuskarta qarasa shiga tayi ciki da sallamah Inna dake parlour ce ta fito da murna tana yima fatuha maraba da zuwa duk da fatuha ba'a cikin jin dadi take ba bata yadda inna ta gane ba, parlour ta jata suka shiga har yanzu mamaki ne shinfide a fuskarta tana qarewa gidan na su kallo yarda yayi kyau ko abirni sai haka ta ce cikin sanyin murya "inna waya gyara gidan nan? murmushi inna ta saki ta ce, "yaron arziki sadiq wallahi shi ya mana abin arzikin nan, ya canza mana gida ya koma kamar aljanna duniya" murmushi fatuha ta saki mai cike da jin dadi Baffa ne ya yaye labilan dakin ya shigo har qasa fatuha ta tsugunna ta gaisheshi amsa mata yayi a taqaice sannan ya samu wuri ya zauna, itama fatuha qasa tayima kanta mazauni tana jiran jawabin Baffa gyaran murya Baffa yayi da cewa, "Fatuha.!
Na'am Baffa.!
"Fatu nasan cewa na maki laifi amma kiyi hakuri ina fatan bazaki watsamin qasa a ido ba? ina fata bazaki bani kunya ba? duk wannan jawabin da Baffa keyi kan fatuha na qasa d'ago kai tayi ta ce, "insha Allah Baffa bazan baka kunya ba"
"yauwa diyar albarka, dama nasan baza ki watsamin kasa a ido ba, dama d'an uwan sadiq ne ya zo neman auran ki tare da iyayansa jiya daddare, mukanmu munyi mamaki da wannan zuwa fatuha ganin halacin da zura'a suka mana gashi nasan baban yaron hakan yasa na amince dan na lura yaron mai nutsuwa ne, Kuma dama neman auran budurwan anso iyayanta su za6a mata miji na gari da wannan nayi la'akari na za6a maki majeed a matsayin miji..! dagowa fatuha tayi a razane dan sai yanzu ta fahimci inda aka dosa idanuwan ta taf da kwalla suka ciko nan take hawaye suka fara anbaliya a fuskarta me yasa mai kyau zai mata irin wannan horan me yasa zai mata haka dama hukuncin daya dauka kenan dama majeed ne dalilin fushin da mai kyau yake da ita mai yasa bai ji ta bakinta ba, fita tayi daga parlour da gudu ta fada dakin inna ta saki wani irin kuka mai tsananin ban tausayi, inna ce ta dafa bayanta tana lallashinta cikin tattausar murya, "haba fatuha bai kamata ki watsawa muta nan qasa a ido ba duk halacin da suka maki banyi tunanin haka daga gare ki ba, kuma yaron nan kin san sa, kuma kowani mutun da qadarar dake zuwa masa fatuha idan dai majeed alkhairi ne a gare ki Allah ya tabatar ke dai na ki addu'a ne" haka inna ta dinga bitana tausar fatuha har ta samu tayi shuru tana sakin ajiyar zuciya, ko ruwa kasa sha fatuha tayi sai bayan sallah la'asar suka dau hanyar kano wayar tace dake cikin jaka taji qara message ya shigo sai a lokacin ta tuna da Mom tace ta kira ta curo wayar tayi ta karanta message din kamar haka,
Sister ina matukar farin cikin sanar dake yau buri na ya cika, mafarki na ya kusa zama gaske, tun jiya nake qoqarin kiran ki wayar taki shiga ba wani albishir bane ila yaya sadiq ya kusa zama miji a gare ni, sannan ina taya ki murnar zama in-law a gidan mu cikin family din mu daga Basma your sister..
Wani irin kuka fatuha ta saki mai cinrai ko qarasa karanta sakon ba tayi ba wayar ta fadi jikinta ban da bari ba abin da yake, ashuru driver ya juyo ya ce, "haba fatuha komai yayi zafi maganin shi Allah bai kamata kina kuka irin haka ba , addu'a ce makamin mumini..! duk wannan magana da ashuru yake fatuha ba jin shi take ba kalmar sadiq yazama miji na kawai ke yawo cikin qwaqwalwarta har suka iso garin kano fatuha na sheka kuka kamar ranta zaifi ta, ko da ashuru yayi horn aka bude geta kafin ya tsaida motar ta bale murfin motar ta fita da gudu sadiq da yanzu ya ji qarar shigowar mota daga labila yayi tare da koma ya cigaba da zarya a bedroom.
Da gudu fatuha ta haura sama ko kallon mutanan parlour batayi ba part din sadiq ta wuce Allah ya bata sa'a tana bude kofar ya bude, ganin bata gashin a parlour ba yasa ta shigewa bedroom da gudu.
fadawa tayi jikin sadiq dake tsaye tare da sakin kuka mai cinrai, rintse ido sadiq yayi yana jin yadda fatuha ke sheqa kuka, sai yanzu ya gane ba sa hannu fatu cikin abinda ya faru cikin sarkewar harshe ta ce, "Uncle dan Allah karkamin haka wannan horan yamin nauyi wallahi bazan iya dauka ba, kaji mai kyau..! my uncle..! my happiness..! dama ace mafarki nake abin da nake ji ba gaske bane..! ta ida zancan tare da sakin sabon kuka ta zame kasa.......
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★
http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn= H-R
*Email* [email protected]
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERS FORUM.COM
77_78
Kuka fatuha ke rairawa kamar ranta zai fita, gabaki d'aya jikinta rawa yake qafafuwan sadiq ta riqe cikin shashekar kuka ta ce, "Please uncle I beg you in the name of God a janye maganar auran nan, wallahi ban shirya yin aure ba yanzu ba, babu abinda ke tsakanina da majeed i swear.! taqara rushewa da wani sabon kuka har yanzu jikin fatuha 6ari yake bakinta na rawa ta ce, "uncle ya zanyi da karatu na? bayan duk duniya ba abinda nake so sama da shi, wallahi uncle ba abinda ke tsakanina da majeed kaji..! ta qara sakin kuka mai cin rai ( ko ni salma sai da na matse kwalla😥) da kyar sadiq ya sai ta kansa ya hade hawayan dake maqale a kwayar idanuwansa, juyawa yayi, ya d'ago fatuha tsaye dake durqushe tana kuka ya zaunar da ita zaman bed amma duk da haka ba daina kukan tayi ba jikinta sai rawa yake tana faman sauke ajiyar zuciya, fridge ya bude ya curo robar ruwa ya tsiyaya a cup ya miqa mata, kuka kawai take baji ba gani, aje cup din sadiq yayi saman bedside drawer ciki cool voice sadiq ya ce "Fatuha..! tsagaita kukanta mai sauti tayi tana kallon sadiq hawaye na sulalo mata, lallashin ta sadiq ya shigayi cikin sanyi murya ya ce, "Fatuha ina so ki sani ko kadan bani na maki haka ba dan me zan maki haka ba tare dana ji ta bakin ki ba" daura hannusa yayi a fuskarta, haka itama fatuha ta daura nata saman hannusa tana sauke ajiyar zuciya, ya cigaba da cewa "Bayan na dau alqawarin samamaki farin ciki har qarshan rayuwar ki fatuha? dan meyasa zan rusa maki mafarkin ki da alkwarin dana dauka? ina so ki kasance mai daukar qadara mai kyau da mara kyau, da anyi shawara dani fatuha ba abinda zai sa na amince a katse maki karatun ki, ko a baki abinda baki so, ko yanzu nasan majeed zai barki kiyi karatu kinji, ki kasance me yima iyayan ki biyaya zaki ga ribar haka, kuma insha Allah zaki so majeed saboda majeed nada kyawawan hali kuma yana son ki zai baki duk wata kulawa, ba zai bari ki taba zubar da hawayan ki a kansa ba, na tabbata yana sonki so haqiqa ki daure ko so d'aya ne ki sama ranki son majeed ko dan yana dan uwa na..! wasu zafafan hawaye ne suka gangarowa fatuha tana bin sadiq da kallo, dan ko bakin magana ta rasa, dama mai kyau bai ta6a jin sonta ba dama ita ke haukarta, tunda gashi shawara yake bata ta so wanin sa.
sadiq ko ban da daurewa ba abinda yake dan numfashinsa neman yankewa yake, sai ya numfasa yake cigaba da maganar saboda zafi da quna da qirjinsa ke masa ganin fatu zatayi nisa da shi, glass cup sadiq ya miqa ma fatuha da ruwa ciki amsa tayi jiki mace ta kafa kai ta shanye ruwan a hankali taji sanyin ruwan na ratsata, shiru suka dauka na mintina ba wanda ya tanka, can sadiq ya ce, "Fatuha kimin promise baza ki tada hankalin ki ba" dakyar fatuha ta iya furta to wasu hawayan suka sulalo, jiki ba qwari ta tashi tana qoqarin fita sadiq ya bita da kallo dan bai jin zai iya tsaida ta saboda ganin tama qara famamasa ciwo ne a ransa.
Tana fita sadiq ya kafa rubar ruwan ya shanye yana maida numfashi tare da ganin wasu taurari namasa yawo.