← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 67

Sashe 48

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      Tsayawa tayi bakin steps ta share hawayan ta dan bata san Mom ta gane cikin nutsuwa ta sako, tana  wasa  da  yatsun  hannuta Mom da fitowar daga kitchen kenan ita da baba jummai murmushi ta saki ta  ce, "ah fatuha har kin dawo? eh tace tana qoqarin hadiye hawayan idanuwan ta Mom ta  ce, "Ahamdulillah ya su inna?
      "lafiya lau" ta ce, sannan Mom ta ce, "ina fata Baffa bai maki dole ba" d'aga kai fatu tayi  alamar a'a idanu  ta  taf da  hawaye tana  wasa  da  yatsun  hannuta baba jummai ce ta shafa fuskarta ta ce, "Alhamdulillah hajiya ni dai bani da abin cewa kun gama min komai a rayuwata" ta ida zancan tana matsar kwalla ta  cigaba  da  cewa, "daga kawo fatuha aiki sai gashi ta zama yar gida har zaku aura da ita hajiya na gode na gode, Allah ya bar zuminci" baba jummai ta fada tana share kwalla idanuwanta Mom  ta  ce, "haba baba ai duk mun zama d'aya ai fatuha ta cancanci abinda yafi haka, kamar  'ya take  waje  na" Mom  ta  fada  cikin  sanyin  murya  tana  mai  taya  sadiq  bakin  cikin  rashin  fatu duk  halin  da  yake  ciki  tana  sane  sarai, haka baba jummai ta dinga zuba Godiya sannan tasa kai ta fita, fatuha kuma ta shige bedroom  ko da shiga d'aki sana'ar ta fara wato kuka dan ya zamar mata jiki daga shekaran jiya zuwa yau,  bedside drawer ta bude ta ciro sarqar da sadiq ya bata tana kuka tana  zancan zuci, dama  duk  abin da sadiq  yake  mata  ba  so  bane  mai  yasa  captain  zai  mata  haka, bayan  ta  jima  tana  fama  da  sonsa  tun   kan tasan  me so tunda  tasa  kafarta gidan ta  kamu  da  son sa  amma sai gashi wani  sabon kuka ne  ya  kwacewa  fatu kuka  ta  ci sosai har ta gaji sannan bacci ya dauke ta.

      Bangaran Basma ban da murna ba abinda take daga  ta  kama  wannan  pillow  sai  ta  saki ta  Kama  wannan, tana  jujuyawa  cikin  dakinta  cike  da annushuwa, duk wasu qawayanta ta fesa masu zata auri handsome, har wani jin ta take a sama yanzu, zata  auri  captain.
                     majeed ko ya kira layin fatuha har ya gaji yanke shawarar zuwa gidan gobe yayi yaga sanyin idaniyansa, duk  da  cewa  yasan  ya  mata  katsalandan a ganin  sa  komai  zai  wuce, sannan ya juya ya gyara kwanciyarsa cike  da  kewarta.

      Washe gari
             Kiran sallah ne ya tashi fatuha jiki ba qwari ta shiga toilet ta sheqa waka ta dauro alwala wani irin jiri ke dibar ta, saboda kukan da tasha jiya dakyar ta iya gabatar da sallah ta zura uniform dinta ta dauki school bag din ta ta fito,

        Ko da ta qaraso dining area Mom ce da Abba sai angel dake gefe cikin nutsuwa ta gaishe su kamar kullun taja kujera ta zauna, ruwan tea kawai ta iya hadawa tana sha kamar tana shan magani kamshin turaran daya  doki  hancinta ne  yasata dagowa sadiq ne cikin uniform dinsa yana riqe da briefcase dinsa, yasha kyau har ya gaji sai dai fuskarsa ba walwala angel ce ta gaishesa ya amsa  tare da yi mata peck, kallon shi fatuha take har ta kasa kauda idanuwanta haka shima sadiq ita yake kallo tuni idanuwan ta suka ciko da kwalla girgiza mata kai sadiq yayi alamar kar tayi kuka, yana murmushin  dayafi  kuka  ciwo lumshe ido tayi tare da qoqarin hadiye kukan da ke niyar kuboce mata, sallamar majeed ce ta doki dodon kunanta, ware ido tayi tana kallon kofar sanye yake da uniform dinsa shima sai sheqi yake yayi  kyau  har  ya  gaji, qarasowa yayi tare da gaishe da su Mom amsawa tayi cikin fara'a, tare da cewa, "ya su Umma?
     "su Umma lafiya lau Mom" sadiq dake tsaye take fara'asa ta dauke daurewa yayi ya tataro nutsuwarsa ya saki murmushin karfin hali ya  ce, "my man yau kai ne da sasafe nan? Sosa keya majeed yayi tare da kallon fatuha kauda kai tayi ta cigaba da juya tea din dake  gabanta dan ba sha take ba.

        Haka sadiq ya dinga danne zuciyarsa, fatuha kuma haka ta gama juya tea din ta tashi tare da daukar school bag dinta, ta ja hannu jidda suka fice tare da yima Mom sai sun dawo, tana fita majeed yabi bayan ta haka shima sadiq kasancewar office zasu.

   Zata shiga mota majeed ya ce, "baki ji ba..! daure fuska fatuha tayi dan wata tsanar majeed take ji juyowa tayi a fusace dan ta gayamasa mara dadi hango sadiq tayi bakin mota da alama su yake kallo, kauda kai sadiq yayi yana wani jin suya a zuciyarsa da rad'ad'i bale murfin mota yayi ya shige, murmushi fatuha ta saki wanda iyakar shi la66an ta ta ce, "uncle majeed ina kwana" cikin zaquwa ya ce, "lafiya lau my love," cikin sanyi murya ya ce "Fatuha!"
       "na'am.! tace a taqaice dan dakyar take masa magana saboda tsanarsa da ke bin zuciyarta ya  ce, "nasan na maki laifi my love naje nayi abu bada sanin ki ba amma please kiyi hakuri" wasu sabin hawaye fatuha ta hade ta ce "Ba komai.! tana qoqarin bale murfin mota ta  tsinkayo  muryar  majeed "idan dai kin hakura please ki bini nayi dropping na ki? daure fuska fatuha tayi dan bata jin zata iya bin majeed a yanzu, lagwabe kai majeed yayi ya ce, "please ki bani dama duk da nasan bani da mazauni a zuciyar ki, musanman  dana  maki  karantsaye, amma dan Allah kiyi hakuri ki so ni koda kad'ane, tunda nataso ban ta6a samun yarinyar da ta kwanta min a rai ba kamarki ba, fatuha please ki bani dama na gwada maki soyayyar da nake maki" haka majeed ya dinga magiya dakyar ya samu fatuha ta shiga motar shima sai da jidda suka shige ya ja motar.

        Sadiq dake zaune cikin mota yana kallo su duk yadda suke, dakyar ya iya saita nutsuwarsa tabbas yasan duk ranar da fatuha ta zama malakin majeed ba abin da zai hana shi zama gawa, dakyar ya iya bude baki ya ce ma driver "ja mu  tafi.! ba musu yabi umarnin ogansa suka bar haraban gidan.
         suna zuwa wajen aikin Sadiq ya 6ale murfin mota ya fito tare da daukar jakarsa, ahankali yake tafiya kamar kazar da kwai ya fashema aciki, duk inda ya wuce ma'aikata nata gaisheshi hannu kawai yake d'aga masu, domin jiyake bakinsa yayi masa nauyi, yana zuwa office dinsa yabude yashiga, yayi jifa da Briefcase dinsa ya zauna bisa kujera wani kuka ne ya ku6uce masa mai radadi da ciwo, jiyake duniyar nayi masa zafi, bai ta6a sanin yana kaunar fautuha ba sai yanzu da yake shirin rasata, na  har  abada Why majeed ! me yasa zakamin haka? me yasa kake neman rushemin farin ciki na? me yasa zakace kana son Fatuha alhalin nafika bukatarta a yanzu, na  fika  son ta why  majeed..!  da karfin tsiya ya daki teburin dake gabansa ya ce, "nooooo Fatuha tawace insha Allah, danni aka  halice ta" wani murmushin karfin hali sadiq yayi (da ni Salma nakasa gane ma'anar hakan)

        Majeed nayin parking a harabar makarantarsu Fatuha ta kama murfin motar zata bude, da sauri ya dana wani remote ya rufe koffofin motar, cike da tsiwa ta dubeshi suna hada ido dashi ta sunkuyar da  kai kasa, batasan meyasa majeed yake mata kwarjini  ba duk yanda taso yimasa rashin kunya suna hada ido zata nemi nutsuwarta ta rasa, murmushi majeed yayi ya ce, "Haba My love, ya za'ayi kifita kibar mijinki da tsananin tunanin ki? ya kamata ki fada min wata kalma da zai sani tunanin ki koda ina office ne please matata kada kice min a'a" takaicine ya lullu6e Fatuha, ban da iskanci gidan uban wa aka d'aura mana aure dashi da har zai kirani matarsa taja tsaki a ranta mtsss, a fili kuma ta ce "Please uncle kabarni natafi dan Allah" ta karasa maganar kamar zata masa kuka "Sorry my lovely zaki tafi amma dan Allah kiyi min murmushi ko zan samu nutsuwar zuciyata?" Fatuha ta ce a ranta "Dan iska shege mugu kawai Allah yasa zuciyar ka ya dawama da bakin ciki kamar yarda kake qoqarin sani, A fili kuma tayi murmushi da iyakarshi le6enta, majeed ya bud'e masu kofar da sauri ta fita tayi gaba, jidda na qoqarin binta majeed yaciro kudi masu yawa yaba jidda shi kansa baisan ko nawane ba tayi masa godiya tare da masa peck a kumatu ta tafi da gudu domin har Fatuha tayi mata nisa, shima majeed cike da farinciki ya bar harabar makarantar.

Written by
      Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                     79_80

     Ko da fatuha  ta shiga class ba wani walwala, haka su Nana suka dinga tanbayar ta mai ke  damunta ta fada masu meke damun ta, amma firtaqi gaya masu damuwar ta, Nana ce ta ce, "fatuha kenan baki daukemu a matsayin qawayan ki ba ko wayanda  zamu  kashe  tare  mu  birne  tare ba? Shiyasa zaki boye mana abin da ke damun ki" Zara ce ta budi baki ta ce, "Kyale ta Nana ai dai mun san matsayin mu yanzu, bai  zama  dole  ta  fada  mana damuwarta  ba" Zara na qoqarin jan Nana subar seat, fatuha ta riqe Zara ta  ce, "please kuyi hakuri, zan fada maku damuwa ta.! ta ida zancan hawaye na sulalo mata, duk abin ya faru haka fatuha ta kwashe ta fada masu ta  karashe  zancan  da  cewa, "ina  son  captain  so  mai  tsanani  wanda  ke  tafiya  tare  da  bugun  numfashina  amma  sai  gashi  lokaci daya" kuka fatu  ta  saki mai  cin  rai ta  fada  jikin  Nana tana  gunjin  kuka, Zara taji haushi ba kadan ba haka  suka dinga bama fatuha hakuri tana raira kuka dakyar suka shawo kanta.

         Bangaran majeed ban da dad'i ba abinda yake ji, zuciyar shi fes take daya lumshe ido kyakyawar fuskar fatuha yake hagowa sai ya qara sakin smile, matsala sa  daya  da  fatu  ta  kasa  sakewa  da  shi.
Chapter 48 · 0% Book details