Sashe 49
Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jingine yake saman kujera office ya rasa sukuninsa, idanuwan shi na lumshe saboda nauyin da suka masa har wata masasara ke rufe shi ga wani irin zafi da qirjinsa ke masa, tamkar an daura masa dutse mai nauyi a hankali ya ware sexy eye's ball's dinsa da suka rine sukayi jaa wayarsa dak'e ruri cikin aljinhunsa ya curo sabuwar number ce baro-baro a screen din, da kamar ba zai dauka ba sai ya daure ya dauka tare da karawa a kunne, daga dayan bangaran cikin zazakar muryata cikin yauki Basma ta masa sallama, amsawa yayi a taqaice tare da tanbayar, "wake magana? gyara kwanciyar tayi daga inda take tare da kankame wayar dan wani irin sanyi ke ratsata, dan gyaran murya tayi cike da shagwaba ta ce, "Yaya sadiq ni ce fa Basma..! ko number ta ashe baka da ita? ta ida zancan cikin shagwaba Sadiq dake kishingide saman kujera, ranshine ya qara suya dan shi duduniya ba macan dake birge shi ko bashi sha'awa kamar fatuha, ko wannan magana ma da take yi jiyake kamar tana watsa masa ruwan zafi, tsuke fuska sadiq yayi kamar tana ganinsa ya ce, "Yanzu ina wani aiki ne letter mayi magana idan na dawo gida" bai jira cewarta ba ya katse wayar tare da yin wurgi da ita ta daki bango ta dawo watse ko ta kanta bai bi ba ya sa kai ya fice daga office din, domin idan ya cigaba da zama tabbas kwakwalwar shi da zuciyarsa suna iya bugawa.
bin wayar tayi da kallo tare da dan bata fuska, ta aje wayar ta kwanta.
Ko da aka tashi su fatuha majeed ne ya zo daukar su, ganin shine yasa ta had'a gira sama data kasa dan ba abinda ta tsana kamar ganinsa, ba yadda ta so haka ta bale murfin motar ta shiga tare da gaishe shi, kallon ta yake mai cike da so da kauna, sannan ya ce "My love daga gani yau kin sha wuya da yawa? ina fata dai kina kulla min da kanki?" dan guntun tsaki fatuha ta ja ciki-ciki sannan ta ce a cikin zuciyar ta "Har wani kira kake na kulla ma da kaina mtww dan iska kawai" muryar majeed ce ta doki dodan kunnan ta a karo na biyu ya ce, "My love! ko duk gajiyar ce tasa ko magana ba'a san yimin?" dan smile fatuha tayi wanda iyakar shi la66an ta ta ce "A'a" murmushi majeed yayi tare da cigaba da driven, haka ya dinga janta da surutu tana amsa masa sama-sama sannan ya wuce da su shoprite yayi masu siyaya ice cream da cake, jidda ko sai dadi take ji dan har yanzu bata san inda aka dosaba.
Suna kunna hancin motar su, suka ci karo da sadiq wanda shima dawowarsa kenan wani irin dogon numfashi sadiq yaja a duk lokacin da yaga majeed da fatuha, numfashinsa sai ya nemi ya dauke ko qirjinsa ya dinga masa zafi, dakyar ya iya d'aga kafarsa dan baya so ko fuskar su ya gani sun fito a tare, amma sai dai kash majeed ya riga ya kira sunan sa. lumshe ido yayi ya tsaya chak! sai da ya kwashe yan mintina sannan ya waigo tare da sakin smile din karfin hali, ta gabansa fatuha ta raba ta wuce jidda nata zuba masa surutu sannan itama ta shige, miqa mashi hannu majeed yayi suka gaisa ya ce, "big man duk yau ban ganka a office ba"
"oh ina cikin office ina wani aiki ne gobe ma nake so na wuce Lagos"
"Lagos kuma? me zaka je yi lagos? cewar majeed
"zan je nayi 2week ne cikin ruwa na dawo"
"Eyya to Allah ya taimaka"
"Amin..! yana qoqarin shigewa majeed ya ce, "Baby..!
"yes..! ya ce a taqaice
"dama ina so muyi wata magana"
"ok mu shiga ciki" ok majeed yace tare da bin bayan sadiq suka shiga part din sadiq briefcase dinsa sadiq ya aje tare da rage kayan jikinsa ya shiga toilet, ya dade a toilet din baiyi wankan ba yana kukan bakin ciki sannan ya tashi yayi wanka, sanye da bathrobe ya fito da qaramin towel a hannusa yana goge jikinsa, majeed na zaune saman sofa shima tashi yayi ya shige toilet ya sheqa wanka ya fito ko da ya fito lokacin sadiq ya shirya cikin black 3 quarter da white shirt mai gajeran hannu, yana zaune saman sofa idanuwansa lumshe, shiryawa majeed yayi a tsanake sannan ya bude wardrobe din sadiq ya ciro riga da wando riga blue sai dark blue jeans sannan ya bude fridge ya curo fresh milk ya tsiyaya a cups ya miqama sadiq ya amsa.
zama yayi kusa da sadiq ya ce, "Please ina so kamin taimako guda daya please?
"ok inajin ka indai baifi karfina..! murmushi majeed ya saki ya ce "Bai fi karfin ka ba" gyara zama sadiq yayi yana sauraran majeed riqe hannusa majeed yayi cikin lagwabe kai ya ce, "please baby kamin hanya fatuha ta so ni..! tsura masa ido sadiq yayi da idanuwansa da suka ciciko da kwala hadiye su yayi yana saurara majeed ya cigaba da cewa, "baby ina son fatu wallahi ina sonta i love her more than how you think, ban ta6a jin son wata d'iya mace ba kamarta ba, baby karkayi tunanin irin son da nake ma sauran yan'mata nake mata a'a son ta nake da gaske ba da wasa ba, idan har na rasata zan iya rasa rai na ina jin sonta mai yawa sadiq na kamu da sonta mara musaltuwa ina manta kai a gabanta ita ce bugun zuciyata sadiq...! majeed ya fada, da sauri-sauri numfashin sadiq ke gudu zaune yake tamkar an dasa akwai yana bin majeed da ido kamar sakarai gabaki daya jikin shi ya mutu sai zuciyarsa dake tsinkewa kamar zata fito waje dan tashin hankali, dan matse hannusa da majeed yayi ya sasa dawowa daga duniyar tunanin, smile ya saki yana kallon majeed ya ce, "my man karka damu kaji d'an jama aji take amma nasan zata so ka kaji, kasan yadda mata suke amma nasan zata so ka har ku dai-daita babu macan da zata same ka ta fasa kai kasan da haka, kana da abinda kowace 'ya mace zata so ka" murmushi majeed ya saki tare da kaima sadiq hug ya ce, da gaske Bros..!
"Eh mana.!
"Ka tabbata fatu zata so ni?
"Sosai ma..! hawaye dake maqale idon sadiq ne suka cigaba da anbaliya dan ko yasan ya rasa fatuha, dan baya fatan abinda zai samu majeed dan uwan shi abokinsa mai son farin cikinsa bashi da aboki dan uwa saman da majeed, mai yasa ma tun farko yake kishin d'an uwan nasa, lokaci yayi da ya kamata ya ba zuciyarsa hakuri jin majeed zai zame jikinsa yasa sadiq saurin share hawayansa tare da sai ta kansa murmushi suka sakar ma junan su, fira suka fara sama-sama kiran sallah magrib ne ya tashe su.
1week letter
Shirye-shiryan aketayi a family house, kasancewa yau za'a sa rana biki duk wanda ka kalla cikin farin ciki yake musanman Basma da majeed.
zaune suke cikin d'akin yan'mata sunata zuba hira muryar Basma kadai ke tashi fatuha na gefe tana matsar kwalla dan har yanzu gani take kamar wasa, kamar kuma a mafarki tashi tayi ta fita daga d'akin ganin kayan da ake ta wucewa da sune yasa jikin fatuha qara sanyi.
fitowa tayi daga parlour hango qanan Baffa tayi su baba Barau kasancewa komai Abban sadiq ya ce zaiyi tunda fatu hannusa take, wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo mata yanzu ta tabbatar za'a samata rana da wanda bata so a matsayin miji kuka ne ya ci karfin ta, fita tayi daga gidan gabaki daya dan ko sanin inda zata ba tayi ba jefa kafar kawai take kan titi, can baba jummai ta fado mata a rai keke napep ta tara ta shige ta ce, a kaita gadan qaya" kasanwcewar gidan baba jummai kan titi yake bata wani sha wahala kwatantawa mai napep gidan ba kukan da take yasa mai keke napap din bar mata kudin saboda ya tausaya mata.
ko sallama bata cika ba ta shige gidan, baba jummai dake qoqari fita, fatuha ce ta fada jikinta tare da sakin kuka kamar ranta zai fita, rud'ewa baba jummai tayi tana kallon ta baki sake tana cewa, "ke lafiyar ki 'yan nan wani abune ya faru? zaunar da ita saman kujera Baba jummai tayi tana qara tanbayar ta lafiya kuka take sosai, cikin shasheqar kuka ta ce, "Wallahi baba bana son majeed bana jin zan iya zaman aure da shi..! ta ida zancan tana rushewa da kuka, sallati baba jummai ta hauyi tare da tafi tana cewa, "na shiga uku ni jummai , me nake ji haka fatuha sokike ki ja mana abin fade? kowa yana mana addu'a Allah ya rufa mana asirri ya kai ki gidan sutura, yanzu kuma ki ce ba haka ba, toh idan ba majeed ba wakike so? kuka ta kuma saki cikin shasheqar kuka bakin ta na rawa ta ce, "CAPTAIN SADIQ nake so Baba..! Baba idan na rasa sadiq mutuwa zanyi, ni shi nake so" ta ida zancan tana kuka mai tsuma zuciya, zaro ido waje baba jummai tayi ta ce, "na shiga uku ni jummai..! rungume fatuha tayi tana lallashi dan ita kanta ta tausayama fatuha ita kanta taso ace da sadiq din za'ayi, amma ya zasuyi tunda shi bai ce yana so ba? d'ago da fatuha tayi tana share mata hawayan ta ta ce, "kiyi hakuri fatuha kinji ki cigaba da addu'a Allah yana tare dake Allah zai dubi zuciyar ki ya baki mafi alheri fatuha, ki sama zuciyar ki sallama kinji" ajiyar zuciya kawai take saki tayi lamo a jikin baba jummai.