← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 67

Sashe 53

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Bangaran su fatuha ko tana tashi wanka tayi, sannan ta shafa lotion mai kamshi ta zura after dress black ta mata kyau sosai sai dai tayi yar rama kad'an saboda tunani, parlour ta fito ta iske Basma na kallo cikin fara'a ta qaraso ta zauna kusa da ita, yar hira suka ta6a sama-sama sannan suka shige kitchen kusan a tare suke aikin, inda baba jummai ke ta bin fatuha da kallo saboda gabaki daya yanzu fatuha bata walwala ga wata yar rama da tayi, haka dai suka dinga aikin bayan sun kamala Basma da rabi'a suka kwashe kulolin suka kai dining area, a lokacin ne baba jummai ta ja fatuha gefe tana mata yar na siha kan tayi hakuri kar ta jama kanta ciwo ta  rage tunani, dan ta lura kwana biyu nan ko  abinci bata ci, kuka tasa mata lallashin ta baba ta dinga yi har ta samu tayi shuru tana qoqarin goge hawayanta Basma ta shigo kallon ta tayi ta ce, "Fatuha me ya saki kuka?" murmushi fatuha ta qakaro wanda iya karshi la66an ta ta ce, "Albasa ce ta shigar min ido"
       "eyya sorry ke je ki wanke fuskar" to tace tare da fita daga kitchen din, ko da ta shiga toilet sana'ar ta cigaba wato kuka sai da tayi san ranta ta fito kaya ta canza tasa riga da skirt na atamfa ash mai ratsin pink masha Allah kayan sun mata kyau, sai dauri da tayi kasancewa hutu take ko sallah ba tayi ba.
       fitowarta daga daki yayi dai-dai da shigowar su majeed mutuwar tsaye majeed yayi yana binta da kallo dan ba qaramin kyau ta masa ba, son ta  da  kaunarta  ne  ya  qara  lullu6e majeed, haka shima sadiq ji yake kamar yaje yayi hug nata saboda  ba  qaramin  kyau  ta  masa  ba cikin sauri-sauri majeed ya qarasa wajanta yana sakin smile ya ce, "My love kinyi kyau" murmushi fatuha tayi wanda iya karshi la66an ta sadiq na tsaye bakin kofa dan ko qarasowa ya kasa, kamar zai rungume ta majeed yayi yana magana can qasan  maqoshi yarda  futu  kad'ai  zata  iya ji "My love kullun qara kyau kike, ji nake kamar na jawo lokacin auran nan namu" sadiq dake gefe sai hadiyar bakin ciki yake dan har ya fara ganin jiri a hankali yake jefa kafarsa da bai san inda zai wurga ta ba, har ya samu ya haura upstairs tun kan ya Isa bedroom ya fara tari da bin bango ya isa toilet, tari kawai yake tare da jini zamewa yayi a qasan toilet yana mai da numfashi yana cire buttom  din rigarsa dan ya samu iska ya dau mintina goma yana a haka, a hankali ya ja jiki ya koma bedroom  kayan jikinsa ya rage yasa jallabiya ya bude bedside drowe ya ciro magani ya sha tare da shigewa blanket saboda fever dake damun shi a yanzu, lumshe ido yayi wasu hawaye masu zafi daya na bin daya.

      Sakin ta majeed yayi tare da yi mata peck a goshi kallon kofa tayi wayam ba sadiq ba alama, haka shima majeed, "oh sweetheart kin ga kin rudani da yawa ko sadiq na manta da shi" ya fada yana dan langwabe kai, fatuha da ta cika taf dan qiris take jira ta fashe daurewa kawai take ta ce, "Ai sai ka bishi..! ta fada tana qaqorin shigewa bedroom  hannun ta ya riqe yana  sakin murmushi ya dawo ya rungume ta ta baya rintse ido tayi tana jin wata tsanar shi cikin  rawar muryar ta ce "Majeed please ka bari? so kake su Mom su fito su ganmu haka? ta fada tana qoqarin kwace kanta majeed ya  ce, "uhm to me dan sun ganmu how many day's ya rage ki zama tawa"
    "naji duk da haka ai da kunya" fada  tana sa masa kuka sakin ta yayi yana bata hakuri ko sauraran shi ba tayi ba ta shige daki tare da fadawa saman bed ta saki kuka.

       Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wasu na farin ciki wasu na bakin ciki, inda ciwo keta cin sadiq dan yanzu sosai yake zubar da jini duk da yana shan magani da zai sa yaji sauki, amma abun sai gaba yake dan har ya fara fida rai da duniya.

      Cikin kayan ta na uniform take shiri duk da jikin ta ba kwari, bayan ta kamala ta fito su Mom na zaune suna break cikin nutsuwa ta gaishe su ta zauna ta jawo cup zata hada tea, kamshi turaran da ya doki hanci tane ya sata waigowa, sadiq ne sanye cikin  uniform dinsa masha Allah yayi kyau sai yar rama da yayi gaishe da Mom yayi tare da yi mata peck ya ja kujera ya zauna, cup fatuha ta jawo zata hada masa tea, da murmushi Basma ta mika hannuta amshi cup din dake hannu  fatu ta ce "Fatuha barshi kawai na hada masa da  kai  na, tunda ke kinga school zaku tafi karku makara" miqa mata cup din fatu tayi jiki ba kwari ta zauna tana juya nata tea din idanuwan ta taf da kwalla, taki yarda ta dago idanuwanta? kuma taki shan tea din, tana gama had'a tea din ta miqo wa sadiq yana miqa hannu zai amsa ya saki cup din ya fadi tea din ya bare a dining area dagowa fatuha tayi saboda tea din ya zuba, kallon sadiq take shima ita yake kallo lallausan murmushi ya sakar mata Basma da  duk  ta  rud'a ta  ce, "yaya sadiq tea din bai bata maka kaya ba ko?
     "Eh Basma"
  "ok bari na hada ma wani"
"barshi kawai nama koshi" dan 6ata fuska tayi, tana kallonsa ta ce "Yanzu baza ka ci komai ba? mom ce ta ce, "Kyale shi indai wannan ne ya saba da haka" to kawai Basma tace tare da fara tatare inda tea din ya zube.

        Kasancewar yau majeed be zo daukar fatuha ba yasa sadiq ne ya sauke su a makaranta, duk da ba wata magana sukayi ma juna ba amma hakan ba qaramin dadi ya masu ba, basuki su dawa ma a haka ba.

   2weeks letter

          Biki ya matso gadan-gadan yasa Mom ta samama amaran mai gyaran jiki, gyara suke sha sosai dan har sun fara murjewa da kyau da sheki dan yanzu Mom ko bari batayi su sadiq su  ga amaran.

       Tunda bikin ya matso kullun sadiq da fever yake kwana yana  tashi  duk  ya  wani  fige  ya  koma  Kala tausayi  kamar  ana  dibarsa ana  miya, gashi yaqi zuwa Dr yakub ya duba shi har yayi mita ya gaji, majeed  yayi  tanbayar  duniyar  nan  sadiq  ya  fada  masa  damuwarsa amma  fir yaki sai  dai  ya  ce, ba  komai.

        Majeed ne ya shigo bedroom din sadiq, sadiq na zaune saman sofa ya jingina ban da tunani ba abinda yake, dafa shin da majeed yayi ne ya sasa ya dago murmushi ya sakar masa sannan ya zauna, ya ce "Ga katin ka nan tun dazu nake kiran wayar ka bata shiga"
     "na kashe wayar ne saboda bana son takura" sadiq ya fada "to ai shikenan yanzu dai ga katin daurin aura anjima zan amso na dinner" katin sadiq yabi da kallo sannan majeed ya sa kai ya fita yana fita sadiq jawo katin yana  kallo  wasu hawaye ne masu zafi suka zubo masa, a hankali ya fara daukar katin d'aya bayan d'aya yana yagawa yana kuka, haka ya dinga bin kati yana cewa, "shikenan fatuha kin zama ba tawa ba, me yasa nayi nauyin baki? na kasa fada maki abinda ke rai na, duk  laifi  nane  da  nayi  wasa  da  damata, har  na  bari  majeed  ya  rigani  furta maki  abinda  ke  rai  na, shikenan na  rasa  farin ciki na, fatuha bana iya rayuwa bada ke ba..! ya qara rushewa da saban kuka😭.

      Zaune suke a bedroom, Hanan ta shigo da katin bikin, ta miqa ma fatuha nata da Basma wani irin murmushi Basma ta saki ta ce,  "Yanzu ni zan auri yaya sadiq? finally buri  na  zai  cika" ta rungume katin tana jin dadi, angel da shigowar ta yanzu kenan amsar katin hannu fatuha tayi ganin ansa majeed baro-baro jikin kati kirjin angel  ya  bada  ras-ras kallon su angel ta shiga yi kamar  yau  ta  fara  ganin  su ta  aje  katin  ta  karo  d'ako  wani haka  dai  idonta  ke  gane  mata  Babanta  da  Basma fatu  da  majeed bakinta na  rawa ta ce, "dama.. Dam.. Aunty fatuha uncle majeed zaki aure..? Baki  ta  kama bata ida zancan ba ta fita daga dakin da gudu tana kuka.
Chapter 53 · 0% Book details