← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 67

Sashe 55

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka angel ta dinga fushi da su fatuha dan ko saurarasu ba tayi, duk abin yabi ya dame su idan anga angel na magana to da Mom take gashi ta daurawa Basma karan tsana, dan ko bari batayi ta ta6a abu itama ta ta6a. abin duk yabi ya damu Sadiq tun Basma bata dauka abun da zafi har abin ya fara 6ata mata rai ga uban na mata diyar na mata.

Yauma kamar kullun mai gyaran jikin ta zo, tana masu kurkur tabi ko ina na jikin su dashi da saqo, sannan ta hada masu zuma cokali 3 madara peak ta ruwa rabin gwangwani da white egg 3 da lemon tsami d'aya ta had'a ta buga su ta murje amaran dasu, ga wasu turaru ka masu kamshi da suke wanka da su na tsumin lale. tuni fatar su ta fara canza launi ga wani sheqi da suke abunka da fararan fata ko kaya suka cire kamshi suke.

Bangaran kayan ni'ima ba'a magana dan wasu Mom da kanta take had'a masu, na kaza dana tantabara gashi kullun sai an basu madara da zuma sun sha kayan fruit ko har turewa suke, su kansu sun san tsumin nayi masu dan sun ga canji sosai a jikinsu, Mom ce ta saki murmushi ta ce "Kai amma wannan gyaran yana yi sosai.n! ji yarda suka murje yaran nan ku ni da nake mace idan na ta6a fatar su biyo ni take ina jin dadi bale kuma angwayan" rufe fuskar su sukayi dan Mom ba qaramar kunya ta basu ba.
bayan a gama gyaran jikin Mom ta raka batul mai gyaran jikin har bakin motar ta sannan ta juyo ko da ta dawo cewa tayi, su fatuha su hada duk abinda suke buqata dan jibi za'a koma family housa a fara gudanar da biki.

Jikin fatuha ne yayi sanyi, dan yanzu har ta fara fidda tsamani ya zamar mata dole ta koyawa kanta son majeed, ko da ta shiga bedroom dinta kayan ta ta shiga hadawa tana sana'ar wato kuka sannan ta aje trolley dinta a gefe.

Bakin wani hadadan gida sadiq ya tsaya da motarsa horn yayi mai gad'i ya bude gate, ya kunna hancin motarsa gaishesa mai gadi'n yayi a taqaice sannan yayi parking din motar suka fito tare da majeed kallon gidan majeed yayi ya ce, "Big man gaskiya gidan nan na da kyau" murmushi sadiq yayi ya ce, "Taho mu Shiga" babu abinda ba'a zubaba na morewar rayuwa ba cikin gidan, iyakar haduwa gidan ya hadu, sai dai kash ba muradin ransa bace zata kasance da shi ba, a wannan gidan ba haka suka gama zagaya gidan sannan suka wuce gidan majeed masha Allah shima gidan iyakar haduwa ya hadu dan sun kashewa gida jan kudi bana wasa ba, bayan duk sun gama dubawa sadiq ya aje majeed a gida sannan shima ya nufo gidan su.

Da sallama ya shigo angel na parlour zaune tana kallo, ciki-ciki ta amsa sallamar tana qoqarin barin parlour jawo ta sadiq yayi ya langwabe kai ya ce, "Angel nasan sarai kin san ba kyau fushi da iyaye? me yasa kike fushi da daddy kin uhm? nasan nayi laifi amma ya kamata by now an yafe min" kuka ta samasa tana cewa "Ni daddy Aunty fatuha nake so?idan ka aureta ka gama min komai" d'ago da fuskar ta sadiq yayi ya ce, "Me yasa baki son Aunty Basma? tana fa sonki angel, tana maki'n duk abinda kike so, kuma Aunty ki ce ko ba komai?" bata rai tayi ta ce "Ni bana son ka aure ta ne that is all.! ni Aunty fatuha nake so..! fuuuu ta wuce sadiq tayi daki tsaye sadiq yayi yana mamakin irin kafewar jidda jikinsa yayi mugun sanyi, fatuha dake qoqarin fitowa daga kitchen tayi lamo tana jin duk abinda suke, haurawa sama sadiq yayi ya wuce part dinsa fatuha tana ganin haka sai ta bi bayan shi a hankali ta bude kofar dakin.
tsaye ta hango sadiq a hankali ta isa ta rungumesa ta baya wani irin yar sadiq ya ji tun daga kansa har d'an yatsan sa na kafa har itama fatuha din, juyo da ita sadiq yayi suna facing juna yana smile dan ja mata hanci yayi yana binta da wani irin kallo ba qaramin kyau tayi masa ba, a hankali ya kai mata peck a goshi yana jin wani sauyi sosai a jikin fatu, itama peck ta masa tare da zame jikinta ta zauna zaman sofa, biyota sadiq yayi tare da kneeldown a wajan yana kallon kyakyawar fuskar ta ya ce, "Fatuha kinyi kyau..! yar dariya tayi tare da rufe fuskar ta, murmushi sadiq yayi a hankali yasa hannu ya cire hannuta dake fuskarta hawaye ya gani suna mata zarya, langwabe kai sadiq yayi dan shima da zai samu dama da kukan zaiyi, tashi yayi ya zauna saman sofa kusa da ita jawo ta jikinsa yayi yana lallashinta cikin sanyin murya can kasan maqoshi, "Please fatuha ki daina kukan nan please bana so.! lamo tayi a fafad'an qirjinsa tana jin bugun zuciyarsa tana jin wani irin feeling na da ban wanda bata ta6a jinsa ba sai akan Sadiq shima din yau, shima haka yake ji a hankali take sauke ajiyar zuciya, d'ago da fuskar ta sadiq yayi yana bin ta da kallo mai cike da so, zuciyarsa sai bijuro masa da wasu abubuwa take zame jikinsa yayi tare da komawa saman bed ya zauna yana kallon fatuha, itama di'n shi take kallo tamkar yau suka fara ganin juna, kauda kai tayi tana wasa da yan yatsun hannunta, miqewa tayi tana qoqari tashi sadiq ya ruqo hannuta tare da jawo ta ta fada jikinsa lallausan murmushi ta saki tana kallon kwayar idonsa kamar yarda ya kafe la66anta da ido a hankali ya daura lips dinsa saman nata ya fara kissing nata sosai sadiq ya fita hayacinsa yana kissing fatu jikinsa har rawa yake, kasancewa fatuha tasha tsimi har ta gaji hakan yasa ta kasa hanasa itama d'in martani take maida masa tamkar zasu cinye juna su, sai da sukayi kissing juna su san ran su sannan suka saki juna, suna bin juna su da kallo suna sauke numfashi cikin cool voice sadiq ya ce "Fatuha..! lamo tayi tana jin shi dan har bata san abinda zai sa ta matsa kusa dashi, shafa gashin kanta ya shiga yi a hankali hakan ba qaramin dad'i yake ma fatuha ba, tana jin yarda hannu sadiq ke mata tafiyar tsutsa a dokin wuyanta can kamar an tsinkuli sadiq ya miqe yana tari da sauri ya shige toilet fatuha ta biyo bayan shi tun kafi ta iso ya kule toilet din da key, dan baya so taga halin da yake ciki, aman jini yake sosai ya dade a toilet din yana abu d'aya fatuha ko duk ta rude sai faman kiran suna sa take tana yan hawaye yana bude toilet ta fada jikinsa a rud'e tana created "Mai kyau me ke damun ka please ka fada min?" ta fada ta shafa masa gefen fuskarsa saman bed ya hau tare da jawo fatu ya ce, "Ba komai kawai na kware ne" haka fatuha ta dinga masa sannu sannan tasa kai ta fita.

Washe gari

Bayan fatuha tayi wanka ta shirya cikin lace dinta maroon mai kyau masha Allah tayi kyau har ta gaji, fatar jikinta sai sheqi take ko da ta fito parlour ba kowa bedroom din angel ta shiga kwance ta hango ta, d'an girgiza kai fatuha tayi tare da bud'e wardrobe ta tafido trolley jidda ta fara zuba mata kayan ta sai da ta gama zuba kayan tsaf ta aje trolley din tana qoqarin fita angel ta tashi ta ce, "Aunty.! cikin sanyin murya juyowa fatuha tayi tana kallon jidda idanuwan ta taf da kwalla da gudu jidda ta rugu ta rungume fatuha tare sakin kuka itama fatuha kamar jira take ta fara nata kukan ba mai lallashin wani sai da suka ci kuka son ransu sannan suka yi shuru suna sauke ajiyar zuciya a tare angel ce ta dago ta ce "Aunty shikenan yanzu bazaki auri daddy na ba? dan smile fatuha tayi tana goge hawayan idonta ta ce, "Angel bai kamata kina damun kanki ba kinji? idan kina son bina sai ki bini mu zauna tare" 6ata fuska angel tayi ta ce, "Aini nafi so na ganki da daddy bada kowa ba"
"Na sani angel, amma shima uncle majeed ai daddy kin ne, da shi da Abban ki duk daya ne, ko kin manta irin son da second daddy yake maki ne My angel Uhm" haka dai fatuha ta dinga lallashin angel sannan ta tafi.

Direct part din Sadiq ta wuce a hankali ta bude kofar part din ta shiga, parlour ba kowa sai kamshi dake tashi bedroom ta shiga kwance ta hango shi qudidine cikin blanket, a hankali ta qarasa zama tayi gefen bed din, a hankali ta fara janye blanket din tana kallon face din sadiq a hankali ta kai masa peck a goshisa, ware sexy eye's ball's dinsa yayi ya sauke su kan fatuha smile ya saki tare da juyawa ya gyara kwanciya dai-dai saitin kunan shi ta ce cikin cool voice din ta "Uncle ka tashi kowa ya gama shiryawa kai kadai ake jira" ware idanuwa yayi yana kallon ta jawo ta yayi ta fad'a saman fafadan qirjinsa ya ce, "Fatuha me yasa kike so ki katse min bacci, ko kun tafi zan iya biyo ku okey.! lamo tayi a qirjinsa ta ce, "Saboda na dinga kallon ka kafin muyi nisa da juna, shiyasa na tashe ka" ta fada idanuwan ta taf da kwalla tashi zaune sadiq yayi yana facing nata shima ji yake kamar yasa kuka, kawai daurewa yake shiyasa yake nuna mata rashin damuwarsa langwabe kai fatuha tayi ta ce, "Ka hada kayan ka ne?
"nope.!
"ok bari na hada ma"
Chapter 55 · 0% Book details