← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 67

Sashe 12

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

     Part din ammi ya fara zuwa  tana zaune saman one star tana kallon film din India wanda ko za'a kashe ta bata san me suke cewa ba, washe da baki ta juyo tana cewa "Ah'ah yau mai gidana da kansa? ya  Hauwa'u ita da  Ibrahim d'in?"
         "lafiya lau" ya ce tare da zama
    "Ka ce min da sarkin surutu ka zomin yanzu ta fara min wannan yaran nasu na yahudawa" Murmushi Sadiq yayi ya ce, "Kisha kurimin ki Ammi ai koya maki take"
            "Ah ni ina zan iya wannan gwalangwatsin wannan sai ku" Asiya ta kwallawa kira, cikin sauri ta qaraso  tare da gaishe da sadiq Ciki-ciki ya amsa kamar mai koyan magana Ammi ta  ce, "Yauwa yan'nan kawo ma mai gida furar dana dama d'azu tana cikin fridge"
            "toh Ammi" ta mike ta wuce kicin.
    Haka akayi ta kawo masa fura ya sha sosai, saboda shi Sadiq mutun ne mai son fura sai da ya sha ya koshi sannan suka wuce part d'in Umma,

  Suna shiga part d'in da Basma suka ci karo, sanye take da riga da wando riga mai dan gajeran hannu pink mai manya flowers tayi kyau sosai duk da yarinya ce hakan yasa shape din ta fitowa, Kallo d'aya Sadiq ya mata ya watsar Gaishe sa tayi tare da jan hannun Jidda tana mata wasa  sadiq ya ce "Basma ina umma?
       "Umma na bedroom"
"OK ki  ce  mata  na  zo" Sannan ya samu  guri ya zauna.
        Umma  da murmushi ta fito sun dad'e suna hira, Inda tasa talatu ta cika masa tray da kayan motsa baki ,suna cikin hira majid ya dawo suka dasa sabuwar hira.

                        *******
  Sosai suke jin dad'i gadar inda yau sai da su fatuha suka taka, duk da ba wani abu suka iya ba, Sosai sun burge mutane ita da fatsima saboda cikin tsari suke rawar su kamar manyan yan'mata....!
Writing by
         Salma mas'ud nadabo

Edit by
       Raheenat

📘 REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★ we are the best★

https://mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&_tn_=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

                    25_26

         Basu suka dawo gida ba sai bayan isha lokacin har jidda tayi bacci,  d'auke yake da ita har suka qaraso  parlour, lokacin rabi'a tana qoqari fitowa daga kitchen, wani irin kallo ya wurga mata jiki ba qwari  ta gaishe shi har tayi gaba ya ce, "Keeee.! Tsayawa tayi cikin tsoro da fargaba, Harara ya qara wurga mata cikin tsawa ya ce mata "Sai ki zo ki amshe ta ko?" Jiki a sa6ule ta amshi jidda, ya  ce,  "Kiyi mata wanka sannan ki samata night dress ki kawo min ita d'aki na dan ban yarda ta rinqa kwana da ke ba ki koya mata halin bera" tsaki yaja  Mtsss, sannan ya wuce part din Abba.

            Abba na  zaune  saman two star fuskar shi manne da glass, sanye yake da fara jalabiya blue remote ne a hannusa yana kallon news, Mom na gefen sa tana yanka fruit.
         D'au da  sallama ya shigo tare da gaishe da Abba,  cikin fara'a Abba ya amsa ya ce "Ah har kun dawo daga zuminci?
           "Eh Abba"
"toh masha Allah ina jidda?
          "jidda tayi bacci"
     "madallah" sun dad'e suna hira sama-sama daga nan Sadiq ya wuce part nashi, ko da ya shiga d'akinsa ya iske ankwantar da jidda shima bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito sai da ya gama shirin shi na bacci sannan ya had'a coffee yana sha yana dana laptop din shi ,ya dad'e a haka sannan ya ture laptop d'in tare da janyo jidda jikin shi bacci ya d'aukesa.

                     *****
       Bayan an gama gad'a kowace ta wuce gidan su, da sallama fatuha ta shigo gida lokaci Baffa ya dawo gida yana zaune bisa tabarma inna na kusa da shi baba jummai na gefe su, gefan baba jummai ta je ta zauna washe da baki itama baba jummai murmusawa tayi sun danyi hira sama-sama da fatuha daga nan bacci ya sureta.

      Baba jummai ce tayi gyaran murya ta ce "Dama jauro ina so muyi wata magana da kai" inna da ke kusa da Baffa tayi qoqari tashi baba jummai ta ce "Kema  zauna" haka ko akayi inna ta samu guri ta zauna.
   Gwoggo  ta  cigaba  da  cewa, "Dama so nake nama ka magana kan fatuha ina so idan zan koma birni sai mu koma tare," Zaro ido Baffa yayi waje yana kallon yar uwar tasa a zuciyarsa ya ce "Anya ko baba jummai tasan me take fada kuwa?"qara murmusawa tayi ta ce, "jauro ina fatan ba za ka watsamin qasa ido ba, a ganina fatuha nima d'iya tace  jauro," Baffa ne  yayi tsale  ya dare ya ce bai san zancan ba babu inda fatuha zata tanan kauyen nan tare da shi baze lamunci hakan ba, baba jummai ce ta fara matsar kwalla tana cewa "Ba komai jauro dan ka ga Allah bai bani haihuwa ba shine zaka wulaqanta ni kan diyar ka, jauro da Allah ya bani haihuwa da yau ba zanji zafin abinda kayi min ba," tana maganar tana kuka inna sai lallashinta take, ganin kukan da take yasa jikin Baffa yayi sanyi dan shi a ganinsa babu abinda baba jummai zata nema a rayuwar shi ya hana ta, sai  gashi  kan  fatuha suna  neman  samun  Matsala da  yar  uwarsa.
              Bayan da ya iya haka ya hakura ya amince  tatafi da fatuha, aiko washe da baki ta masa godiya tare da yi masa alqawarin zata riqe amanar fatuha sosai daga nan kowa ya wuce dakinsa.

                          ******
     Ko da ya tashi ya gama shirin sa ciki uniform masha Allah yayi kyau sosai,  zai d'au briefcase d'in sa kenan jidda ta tashi washe da baki ta ce, "Daddy morning"
          "morning too angel"
"uhm yau ma daddy guduwa zakayi ka bar little princess din ka a gida? langwabe kai yayi ya ce "Sorry angel daddy work zai tafi kinji kuma yara basa zuwa, kema very soon zaki fara zuwa school ai kinaso ko angel? washe baki tayi ta ce "Yes daddy zan fara zuwa school kamar yarda su yaya Hanan ke zuwa da Anuty Basma ko?
       "Eh mana angel" tsale tayi ta kai masa hug "thanks my daddy" smile yayi tare da yimata peck ya  ce,  "please angel ki tsaya rabi'a ta maki wanka kin ji, naji grandma na cewa kullun sai kin yi rigima" 6ata fuska tayi ta ce, "Daddy...!
         "shhhh.! tare da yi mata peck a kumatu ya fice.

      A dining area ya had'u da Abba shima yana breakfast, Mom na  gefen shi a hankali ya qarasa yayi masu peck sannan ya samu waje ya zauna ya fara breakfast, lafiyayan chips ne da plantain and egg sai tea mai kauri wanda ya sha ovaltine, cikin natsuwa suka gama break d'in su, Abba da Sadiq tare suka fito inda yaran Sadiq ke ta kwasar gaisuwa wajan Abba   tare da qamema Sadiq d'in cikin natsuwa motocinsu suka fita daga harabar gidan.

                         ****
    Ko da fatuha ta tashi wanke-wanke tayi, sannan ta d'au tulun ta gidan su fatsima ta biya tare suka fito suna tafe suna hirar su, kandala suka hango d'auke da farantin gyadarta qarasowa su kayi wajan ta, Kallon su take jiki ba kwari  harara suka wurga mata tare da cewa "Bamu gyad'a ta murtala" jikinta baqwari ta fara zuba masu gyad'ar tasan ko zata mutu baza su bata kudin gyad'ar ba, kuma ta matsa masu  su tona mata asiri sai da ta gama zuba masu sannan fatuha ta amsa ta ce  "Cikin Murtala da d'an mai gari ya mana alqawari ne muka amshi gyadar, sannan kice masa ko ya bamu murtalar mu ko kuma murtala ta rinqa haihuwa" sannan suka wuce suka barta tsaye tana matsar kwalla.

            Suna isa rafi suka aje tulu nan su gefen rafi suka wuce gonar mai gari suka fara tsinkar mangwaro da gwaba, sai da suka d'iba son ransu sannan suka zo zasu fita mai gadi ya kama su.
          "kai-kai uban wa ya baku ikon shigowa gonar mai gari? har ku tsinke  masa mangwaro.! Fatuha ce ta turo baki gaba ta ce, "bala ne ya bani izinin shigowa"
     "shegiya mai kama da mayu, shi balan sa'an kine? Koko  sabo  da  raini  irin  naki  dama  kin  rai  uban  kowa, inama kika san balan? harara fatsima ta wurga masa ta  ce, "idan baka yarda ba sai ka kai mu wajan shi ka ji da kunnan ka" ta ida zancan tana gyara d'aurin zaninta.
            "Ai  dama  ba  kunya  ta  ishe  ki ba mindin   naji  akasin  haka  na  lahira  sai  ya  fiki  jin  dad'i "
      Aiko haka akayi mai gadi jan su fatuha yayi har gaban bala, sai yan harare-harare suke koda ya  suma bala ya  masa  bayani sai ya ce, "shi ya ce su d'inba dan yasan in bai ce ba tuna masa asari zasuyi, na  sun  ta6a kamasa  da  kandala gari  kowa  ya  sani  ana  ganin sa  da  mutunci sannan yasa mai gadi ya sake su wani irin dad'i suka ji suna ta shewa suka isa rafi suka debo ruwa.

                        *****
Bai zame ko ina ba sai Yandutse college dan samoma jidda admission, bai sha wani wahalla ba ya samama ta inda duk angama abinda za'ayi, ranar Monday sai ta fara zuwa school sannan ya wuce office, a cewar shi inya dawo gida da yamma zai samamata malamin adini.
Chapter 12 · 0% Book details