← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 67

Sashe 35

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Ba ita ta tashi ba sai kusan karfe 10:30 brush kawai tayi tare da gyara gashin kanta ya kwanta har gadon baya, sannan ta fito parlour sanye da gwon black mai kyau masha Allah fatuha tayi kyau ga wani haske da ta qara, gashi kullun yan matan ci bayana yake a jikinta.
       Jin bata ji kamshi bane yasa gaban ta ya fadi leqawa kitchen tayi taga wayam ba rabi'a ba alama dan bata rai tayi ta dawo parlour tare da wucewa dining area, bude kulolin jiya ta fara yi jiya ma kusan ita kadai ta ci abincin dan guntun tsaki ta kuma ja tare da kwashe kayan ta wuce kitchen, gyara kitchen d'in ta shiga yi sai da kitchen din ya fita tas sannan ta d'aura ruwan zafi kan wuta ta fita sai da ta gama gyara ko ina sannan ta dawo kitchen, ta juye ruwan zafin cikin flacks  sannan ta soya kwai ta juye a plate ta rufe yan ciki ta fido a fridge suma ta wanke ta gyara ta d'aura a tukunya tare da gyara kayan miya ta zuba da k'yan kamshi tuni kitchen din ya gwaraye da k'amshi dad'i,  parlour ta fito tare da haurawa up stair's a hankali ta murda handle din kofar part din sadiq wani irin sanyi da kamshi dadi suka doki hanci ta, lumshe ido tayi tare da ware su tana qarewa parlour kallo tsit parlour ba kowa, hakan ya tabatar mata da mai kyau ya tafi wajan aiki kofar bedroom ta nufa tare da bude ta a hankali  ta shiga dakin kamar yarda ta saba, sanyi AC ne kawai ke tashi sai kamshi kayan d'akin ta fara tatarewa duk da d'akin ba wani dati yayi ba blanket ta jawo zata linke sai taji anja, ware ido tayi waje tare da fara jin tsoro ko lafiya qara jan blanket din tayi taji anja dawowa tayi gaban bed din tayi tsaya a hankali ta kai hannu duk da zuciyar na dukan uku uku saboda tasan yau tuesday sadiq na zuwa office kuma baya kaiwa wannan lokacin bai fita ba, a hankali ta sa hannu ta fara yaye blanket din dai-dai fuskar sadiq taja ta tsaya Chak, saboda ba abinda sadiq yake sai rawar dari, a rude fatuha ta ce "Mai kyau me ya same ka? ta fadi bakin ta na rawa inbada rawar dari ba abinda ya ke sai hawayan fever dake bimasa fuska dan ko magana bai iyawa sai ma rintsa ido da yayi yana qoqari jawo blanket ya rufe jikin shi, riqe blanket din fatuha tayi tana  kallonsa  cike  da  tausayinsa har da yan  hawayanta tana  cewa, "mai kyau dan Allah me ke damu ka? hannuta  na  rawa  ta  kai hannuta tata6a goshin shin wani irin zafi taji rau take nan ta hau reramai kuka duk fever da ke jikin sadiq sai da fatuha ta dan bashi dariya, da  tausayi  ganin  yarda  take  damuwa  da  shi  sosai  duk da basa  wani  shan  inuwa  d'aya, yadda  ta rude sai ka ce yau ta fara ganin ana fever amma sai ya guntse dariyar tare da qara lumshe ido dan bai san ganin wannan kukan ko mutuwa yayi ai sai haka fita tayi daga d'aki ganin zaman bai fishe ta, tana zuwa bakin k'ofar fita suka ci qaro da ola shima zai shigo ya ji ko lafiya Oga bai fito ba, ganin fatuha na kuka yasa shi tsayawa tanbayar ta lafiya kora masa bayani kawai tayi sannan, shima ya haura sama part din sadiq wayar shi dake aljihu ya ciro ya kira doctor yakub sannan ya zauna saman sofa fatuha kuma na zaune kusa da sadiq tasa ruwan a ruba da towel tana dadana masa akai saboda jikin nashi ba qaramin zafi yayi ba cikin 15 minutes doctor ya qaraso gaishe shi fatuha tayi tare da matsa masa ya zauna, shi kuma ola ya fice, duba sadiq ya shiga yi  yan rubuce-rubuce yayi tare da gwada Bp din shi ya hau sosai kallon sa doctor yakub yayi tare da gwada kai ya curo allura zai  masa fatuha dake gefe sai ka ce  ita za ayima wa ritse ido tayi  tana  ji  tamkar  ita  doctor  zai  ma  allura dan ba abinda ta tsana kamar allura, bayan ya kamala duk abinda yake Dr yakub ya juyo cikin fara'a ya ce, "insha Allah anjima zai tashi kuma insha Allah fever zata sauka karki  damu anjima zanzo" fido magunguna doctor  yayi ya  ce, "dan Allah idan ya tashi ya samu yaci abinci dan babu alamar ya ci abinci, idan zan dawo zan dawo da ledar ruwa" to fatuha ta ce masa tare da masa godiya ta rakoshi har bakin kofa ta koma ciki, Ko da ta koma ciki, kitchen ta shige ta qarawa farfesunta dake wuta ruwa sannan ta koma part din Sadiq leqa fuskar  shi tayi ganin yana bacci yasata sakin ajiyar azuciya tare da ta6a goshinsa ta  ce, "Alhamdulillah zazza6in ya sauka" sannan ta rage gudun AC d'aki ta fara gyara part din.Written by
        Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

  📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com-Real-Hausa-fulani-writers-forumRHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*_Email_*
realhausafulaniwritersforum@gmail. com

*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                       61_62

       Sai da ta gama gyara part din tsaf sannan ta koma kitchen, lokacin har farfesun yayi ta juye a kula tare da plate ta zuba a  tray da bread a hankali take taka upstairs saboda ta cika tray din da kayan abinci, bakin kofa ta aje tray din sannan ta bude kofar ta shiga har cikin bedroom ta aje a stool qara leka fuskar sadiq tayi a qaro na biyu murmushi ta saki tare da zama gefan shi tana kallon yadda sajansa ya kwanta luf har mamakin kyau irin na sadiq take, sai dai yayi yar rama sannna fuskarsa tayi fayau dariya tayi ta ce "Ohni sangami ciwo yayi kamu kayi bulun buqwi tunda likita ya tsulama allura kaji zafi sai bacci kake, qila ma suma kayi saboda  zafi, kai  ma ka  ji  yarda naji  ranan yadda kayi bacci kamar ba masifafe ba, amma da ka warke zaka fara cika mana gida da tsuwa, na huta da masifar ka ko ta kwana biyu ce uhm bari na lalla6a naje nayi wanka a toilet din ka tunda kai ka zama gawar shanu dan tashin ka ba yanzu.

       Tashi fatuha tayi ta bude wardrobe ta ciro qaramin towel ta rage kayan jikinta tasa towel, duk wannan abun da fatuha ke duk a kunnan sadiq dan ya dade da tashi kawai dai yayi lamo ne, toilet din ta shige ta sheqa wanka ta fito ko da fito cikin sanda take tafiyar har ta qaraso gefe bed leqa fuskar sadiq tayi tana riqe da qaramin towel tana goge gashin kanta ta  ce, Allah sarki ba wan Allah sai bacci kake baka san wainar dana ke toyawa ba wai da zaka tashi dana sha masifa, yarfe gashin kanta tayi wanda hakan yasa ruwan gashin ya watso ma sadiq a fuska dan motsa ido yayi hakan yasa fatuha zaro ido tare da yin lamo tana zare ido tana yarfe hannu ganin ya juya ya gyara kwaciyar shi ya sata sakin a jiyar zuciya, baki dressing mirror din shi ta tsaya tana kallon mayukan dake baje akan dressing mirror  tsuru-tsuru tayi tana tunanin man da zata shafa can ta kai hannu kan wani mai na gashi kasancewa fatuha ba boko yasa ta d'auka ta fara shafawa sadiq dake kallon ta ta qasan ido sai dariya yake guntsewa, in taqaice maku duk wani mai dake saman dressing mirror sai fatu ta shafa dan taji ya mai kyau ya ke ji sannan ta fita daga d'akin, tana zuwa bedroom dinta kaya tasa sadiq dake d'aki dariya yayi sosai har da riqe ciki dan guntun saki ya ja tare da cewa "Yar kauye kawai..! Sannan ya tashi a hankali duk da har yanzu baya jin karfin jikinsa wanka yayi sannan ya fito yasa jallabiya ash mai kyau sannan ya gabatar da sallolin shi, yana idarwa  ya qara koma wa ya kwanta dan karfin hali kawai yake.

    Sket da riga tasa na atamfa mai ratsin dark green da coffee brown sai gyara gashin kanta da tayi tare da yin  ture ka ga tsiya dauri, sannan ta qara fesa turare rufe bedroom din tayi ta fito sannan ta haura upstairs direct bedroom din sadiq ta shige kwance ta gan shi amma sai dai wannan lokacin idanuwan shi biyu murmushi ta saki tare da qaraso wajan shi cikin sanyin murya ta ce "Mai kyau ya jiki?" lumshe ido yayi tare da ware su kan fatuha jim yayi yana qare mata kallo ba qaramin kyau tamasa ba musanman dan qaramin lips din ta pick kauda kai yayi tare da cewa, "da sauki.! ya lumshe ido smile ta kuma yi tare da jawo tray dake saman stool ta cigaba da saving nashi cikin nutsuwa kasancewa tasan bai cin abinci bane sosai, shiyasa ta zuba masa farfesun yan cikin kad'an ciki dan boll,
Chapter 35 · 0% Book details