← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 67

Sashe 63

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Kuka fatuha take ta sheqawa, a hankali Sadiq ya miqa hannu ya dauke ta kuka ta kuma samasa tana mutsu-mutsu tana cewa "Ni ka kyale ni? cikin dashashiyar muryata zama sadiq yayi  ya sa hannu ya shafa kanta ya ce "Am sorry love..! kuka ta  saki saboda tuna  azabar da tasha, daukar ta kawai Sadiq yayi sai tsala-tsale take ya sake ta bai dire ta ko ina ba sai cikin ruwan dumi, miqewa tayi tana qoqarin fita ya mai data kuka ta saka masa ta ce, "Dama har yanzu mai kyau ba ka daina cin zali ba? Kuma wallahi yau gida zan kwana.! sadiq bai ce mata komai ba sai ma tausayi  da take bashi, dan ba qaramar dirza yayi  mata ba ko a hakan ba koshi yayi ba kawai ya tausaya mata ne, da kanshi ya mata wanka sannan ya fito ya barta tayi wankan tsarki, ko da ya fito bedsheet  ya cire ya canza wani tare da qara gyara dakin ko da fatuha ta gama wanka kuka ta qara saki saboda ta kasa fitowa, jin kukan yayi yawa yasa sadiq komawa toilet din zaune ya same ta, harara ta aika masa ta ce, "shikenan ka mai dani musaka" ta ida zancan tana rushewa da kuka, abin dariya yaso ya bama sadiq daukar ta yayi  sai saman bed, ya taimaka mata ta shirya ya zura mata hijab, shima a gurguje ya shige toilet yayi wanka yana fitowa jalabiya ya zura ya ja su sallah bayan sun idar  ya maida ta bed, a hankali ya jawo ta jikinsa ya rungume tsam tamkar ya maidata cikin dan so ya ce, "Fatuha Allah ya sa maki albarka bani da bakin da zan iya gode maki my wife, kin sani farin ciki mara musaltuwa kin kore min duk wata damuwa my love, naji dadi da kika kilace min kan ki har wannan lokaci, nayi maki alqawarin zan baki farin cikin har qarshan rayuwata fatuha" wani irin dadine ya lullu6e fatuha son mijinta na qara narke mata a zuciya, lamo tayi a jikinsa tana sauke numfashi a hankali  d'ago da face nata yayi ya sakar mata peck ya furta, "am sorry my wife, nasan na wahalar dake amma ai.! bai ida zancan ba fatuha ta hada bakin su guri guda tana masa french kiss, take ta qara rikitashi da salon ta ganin zai zarce tasa masa kuka, dariya yayi tare da ja mata hanci ya ce, "Matsoraciya kawai"
         "naji din ba komai kuma gida zaka mai dani wallahi"
         "lallai kam kwarankwatsi ba inda zaki" ya fada yana kallon fatuha, dariya suka saki a tare ya ce, "My love akwai drama" ya  ida zancan yana lakace mata hanci qara matse ta yayi suka shige blanket suka koma bacci.

          Basu tashi ba sai kusan shadaya,  a hankali sadiq ya zame jikinsa ya  shige toilet, ya qara hadawa fatuha ruwan dumi daukar ta ya dawo yayi ya kaita toilet yana dire ta ta bude ido tare da lumshe su, wata irin kunyar shi take ji a wannan lokacin, ruwan dadi ya mata taji dama-dama, sannan ya maidota bedroom shima ya koma yayi wanka ko da ya fito ta shirya cikin riga da sket na atamfa dinkin ya mata kyau sosai ga make up tasha lallausan smile Sadiq ya saki tare da qarasowa ya rungumeta ta baya ciki cool voice ya ce, "My love kinyi kyau" murmushi tayi ta ce, "Thanks love" lotion ta jawo tana shafa masa ita da kanta ta zaba masa kaya wani hadadan yadi mai tsada ta curo masa milk da ratsin brown mara kauri ya sha diki da dark brown zare taimaka masa tayi yasa, tuni suka fito sukayi kyau masha Allah, knocking din kofar da ake ne ya sa sadiq qoqarin fita kusan a tare suka fito da fatuha parlour ta bi da kallo wani irin kyau ya mata gidan kamar ba'a qasar Nigeria take ba dan yayi matukar tsaruwa.

     A hankali ya bude kofar baba jummai ce riqe da kuloli, murmushi sadiq ya saki tare da gaishe ta angel ce ta fada jikinsa ta rungumesa ta ce, "Daddy.! dariya sadiq ya saki ya ca6e ta, qarasa shigowa baba jummai tayi ta aje kulolin, fatuha qarasowa tayi ta gaida baba jummai ta amsa angel sakowa tayi daga jikin daddy ta rungume fatuha smile fatuha tayi ta ce, "I miss you angel" tare da yi mata peck a kumatu.

        Parlour angel ta dawo ta ce, "Daddy  kunna min kallo"   kunna mata yayi  shima ya zauna kusa da ita baba jummai ko jan fatuha daki tayi ta bata sakon Mom na kayan tsimi da turaru  ka  masu kamshi da tsada, Godiya fatuha ta dinga jera mata suka fito a tare, murmushi baba jummai tayi ta ce, "Jidda taso mu tafi ko? 6ata fuska fatuha da angel su kayi lokaci daya fatu ta ce, "A barta anan munyi missing nata ni da baban ta ko? ta fada tana kallon sadiq, murmushi yayi tare da daga mata gira yana jin dadi yadda fatuha ke gwada ma angel so da kauna, baba jumma sakin baki tayi ta ce, "ni da zuwa da yar rakiya ku da amshe min ita, to ai shikenan ni na wuce Allah ya bada zaman lafiya" har bakin kofa fatuha ta rako ta sannan ta dawo parlour hannu jidda ta janyo ta ce, "Zo muje kiyi break nasan ba kiyi ba" tashi su kayi a tare taja ma sadiq kujera ya zauna, sannan angel ta zauna, saving din su fatuha tayi a hankali sadiq ya fara feeding  fatuha itama tana feeding nashi da angel sai murna suke suna jin dadi cike da so da kauna ida sadiq ya zage yana gwada masu so

    Agurguje

              Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi,  fatuha ce tsaye gaban dressing mirror sanye da uniform kasancewar yanzu ta koma  school, yanzu haka tana SS3 kuma ita ce Head girl tana shirya sadiq cikin uniform nashi smile  yayi tare da yi mata peck ya ce, "I love you"
    "love you more habibina" briefcase din sadiq ta dauka da school bag din ta suna  fitowa angel suka samu zaune saman dining area ta fara break gaishe su tayi tare da yi masu peck suma kujera suka ja suka fara break, bayan sun kamala fatuha ta kira yar tsohuwar mai aikinta ta ce ta kulla da gidan sannan karta dafa abinci sai ta dawo zata daura da kanta to tace mata tare da yi masu Allah ya kiyaye hanya, ta koma bakin aikinta, mota suka shige sadiq ya ja su bai sauke su ko ina ba sai harabar makaranta yana parking angel ta bude kofa ta fita fatuha na qoqarin fita ya riqe ta, murmushi ta saki a hankali ya jawo ta jikinsa yayi kissing na ta lumshe ido tayi ta ware su a kan sadiq ta ce, "Habibina zanyi missing naka?"
          "nima haka my love," Sannan fatuha ta bale murfin motar ta fita,

    Tana Shiga class su Zara suka dau shewa suna cewa, "kai Head girl kina wuta wallahi," harara ta aika masu tana cewa, "wallahi na kusa maganin ku" yar shewa sukayi  tare da cewa, "lallai ma"  wata dariyar shaqiyanci Zara tayi ta ce "kwanan naga wani sheqi kike me sirin? littafin hannu ta fatuha ta gefa ma Zara dariya suka sa a tare suka ce, "zakiyi bayani wallahi" ganin uncle ya shigo yasa su nutsuwa aka cigaba da gabatar da darasi,  kasancewa yau juma'a karfe 12:30pm suka tashi drive ne ya zo daukar su  direct gida ya dire su.

         Wanka suka yi sannan fatuha ta shirya cikin 3 quarter pink da t-shirt  milk  ba qaramin kyau fatuha tayi ba, sai gashin kanta da ta sharce ya kwanto har gadon bayan ta fitowa tayi daga bedroom ta shiga kitchen, tuwon shinkafa ta daura miyar Egushi taji naman rago kamshi sai tashi yake sannan ta ahada juice din mangworo dan ba qaramin dadi yake mata ba, kwana biyu nan bayan ta kamala ta dawo dining ta jera sannan ta koma bed ta qara sheqa wanka ta fita ta shirya cikin gown din ta maroon mai stone's dikin ya hauta sosai parking din gashi kanta tayi jin a shigone ya sata waigowa angel ce tsaye bakin kofa, murmushi tayi ta ce, "Mom kinyi kyau" murmushi fatuha tayi ta ce, "thank you my angel" langwabe kai angel tayi ta ce,  "Mom ina so naje gidan Mami yau ne birthday Jamal" smile fatuha tayi ta ce, "To shikenan amma sai kin fara lunch" dan shagwabe fuska tayi ta ce, "Please Mom kin san fa nice best friend tare zamuyi komai"
         "ok naji ina zuwa" wata hadadiyar gown ta curo daga wardrobe tare da gift ta ce, "gashi wannan gown din taki ce ita zaki sa ki tafi" wani irin tsale angel tayi ta rungume fatuha tana mata peck ta ce, "thanks Mom.! Sannan ta zame jikin ta dariya fatuha tayi tare da lakace mata hanci ta ce, "Wannan  gift din kuma na Jamal ne" Godiya ta mata tare da rugawa daki ta shirya girgiza kai fatuha tayi ta cigaba da abinda take, rungumeta ta bayan da akayi yasa fatu lumshe ido  ta ce, "Habibi na" ajiyar zuciya sadiq ya saki ya ce, "My love gabaki daya make up din nan ta gigitani kinyi kyau" smile tayi tare da juyowa suna facing juna a hankali ya kai hannu ya warware parking din....

Written by
        Salma mas'ud nadabo

     Edit by
          Raheenat

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM

                           99_100

1 Month letter

   Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi, inda sadiq ya samu qarin girma dan yanzu haka abuja ya koma da aiki sai weekend yake dawowa kano, fatuha kuwa  shirye-shiryan SSCE suke angel kuma JSSCE, sosai suke samu kulawa wajan sadiq inda yake fifita son su dana kowa, ya ware masu guri na musanman a zuciyarsa haka itama fatuha sosai take bashi kulawa da nuna masa tsantsar soyayya.

    Bangaran su fatima majeed ya sama mata makaranta su fatuha ta fara tun daga jss1, sosai take maida hankali dan ganin taci ma burin ta.

        Basma kuwa Khaleed ya sama mata admission a BUK tana karanta english, sosai take samun kulawa wajan  Khaleed. 

    Dr yakub kuwa soyayya suke zubawa tsakaninsa da  Hanan har manya sun shiga maganar.
Chapter 63 · 0% Book details