← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 67

Sashe 67

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

        sosai Mom ta zage tana gyaran ya'yan nata inda suke ta shan gyara  jikin da tsimi wani irin kyau da sheqi suke  zubawa, baby's kuwa sunyi wayau gasu yan duma-duma saboda suna samun ruwan nono sosai kullan angel na maqale da Aslam sai fatuha zata bashi nono sannan angel ke bata shi, dan wani irin son duniya ta daura mashi, bata da  lokaci kowa sai na Aslam.

      Sanye da qaramin towel ta fito daga bathroom tana goge gashin kanta da qaramin towel, gaban dressing mirror ta tsaya tana shiryawa lotion ta jawo zata shafa, ta hango sadiq ta cikin mirror lallausan murmushi ta sakar masa a hankali ya qaraso ya rungumeta ta baya sanyayar ajiyar zuciya ya saki yana shinshinar kamshi jikinta lumshe ido fatuha tayi tana amsar sakonin sadiq, dan ba qaramin kewarsa tayi ba qoqarin zame towel di'n jikinta yake ta riqe tana kallonsa ta cikin mirror, lumshe shanyayun idnusa yayi ya ce, "Please..! yana qoqarin zame hannuta dake saman towel din kasa magana fatu tayi har sadiq ya samu nasara zame towel din rintse ido tayi tare da waigowa ta shige jikinsa, daukar ta cak yayi ya daura saman bed ya fara aika mata sakonni da zafi-zafi lokaci daya suka fice hayacin su, gani zasu lula yasa na silale na fice.

        Shiryawa take cikin atamfa riga da sket cike da shagwaba ta ce, "Habibina gaskiya ka tashi ka fita bana so Mom ta zo ta gan ka, tana ganin ka zata gane" ta ida zancan tana parking  gashin kanta smile sadiq yayi  ya rungumeta sosai ta baya can kasan makoshi ya ce, "Uhm my love baza ta gane komai ba kinji"
      "da gaske" daga mata kai sadiq yayi alamar eh tare da ciro wasu takadu daga aljihusa ya miqamata, wani irin tsale fatuha tayi ta qanqanme sadiq dan murna ba komai  bane yasata farin cikin ba sai admission na north west university data gani.

      Da sauri fatuha ta fita tana kwalawa Mom kira, fitowa tayi daga kitchen ta ce, "na'am fatuha" fadawa tayi jikin Mom tare da nuna mata admission murna Mom ta tayata tare da yima sadiq godiya sosa keya yayi angel itama fitowa tayi riqe da Aslam amsarsa sadiq yayi yana mashi wasa, haka su fatima suka dinga taya fatuha murna.

    3  years letters

      Sosai fatuha ke maida hankali a karatun ta tana karanta law yanzu haka tana level 2, Aslam yayi wayau sosai dan har tafiya yana yi ba ida baya zuwa zai kai  2years ga surutu  tsiya komai ya gani sai ya tanka, angel kuma na SS2 an fara zama yan'mata sosai.

       Yauma kamar kullun a  gajiye ta dawo daga makaranta tun safe taje school sai 5:00pm suka gama lectures, a gajiye likis ta dawo gida ga wata irin kasala dake damunta, Aslam ne ya sako daga jikin baba asabe rugo da gudu ya fada jikin fatuha, daga shi sama tayi tana chabesa yana dariya  zaunawa tayi saman three sitar tare da gaida baba asabe amsawa tayi atakaice ta shige kitchen Aslam zama yayi saman cinyar ta yana zuba mata surutu, cakulkuli ta shiga yi masa yana dariya tsagaitawa tayi ta ce "Ina yaya?, daga kai yayi cikin tsamin murya ya ce, "yaya na bacci" ok fatuha tace tare da tashi ta shige bedroom bata zame ko ina ba sai toilet ta sheqa wanka ta fito  ta gabatar da salolin da ake bin ta, turo kofar da akayi ne ya sata smile angel ce tsaye bakin kofar sanye da jean  n t-shirt ta ce, "mom sannu da zuwa,"
      "yauwa" fatuha tace qarasowa tayi ta ce, "Mom  ki zo muyi lunch tun dazu na dawo daga school naqi cin komai sai kin dawo," murmushi fatuha tayi ta ce " Karki qara barin kanki da yunwa kinji angel? d'aga kai tayi ta ce,  "ai nasha fresh milk"
      "ok muje" dining area suka wuce  lafiyayan doya ce da miya tasha kaji da naman rago sai kamshi ke tashi sosai fatuha taci abincin dan wani irin san doya take kwanan kusan kullun sai ta ci ga wani iri ci da take yanzu kamar runbu da san bacci har mamaki kanta take, bayan su kamala cin abinci suka dawo parlour suna kallo  Aslam sai wasa yake da kayan parlour komai ya gani abin wasa ne da an hanasa sai kuka yace zai fada ma daddy, yanzu ma haka 6ana yake fatuha jawo hannuwansa ta hada biyu tana masa fada kuka ya sa mata kamar ta daura masa wuka sadiq da shigowarsa yanzu kenan harara ya aika ma fatuha ya qaraso ya dauki Aslam ya wuce da shi bedroom nasa, ta6e baki  fatuha tayi tare da bin bayansa ko kallon ta baiyi ba sai ma wasa da yake ma Aslam yana dariya miqa hannu tayi ya bata Aslam ya wurga mata harara  ya ce, "Baki shi zanyi ki ida kasheshi ko me? ya  ida zancan yana qara rungume Aslam dariya fatuha tayi ta ce "Dama ka bani shi saboda yanzu zai fara daura ma headache, yaron nan baya ji sam"
        "hmm  zakiyi bayani na kama ki kina dukar min d'a" jawo ta Sadiq yayi ta fada saman bed yana kai mata naushin wasa shi da Aslam dariya take sosai rungume sadiq tayi a hankali yake shafa bayan ta ya ce, "I miss you love" zame jikin ta tayi tare da kashe masa ido ta dauki Aslam ta maida shi parlour kana ta dawo taimaka ma sadiq  ya rage kayansa suka shige toilet maqale da juna suka fito suna shan soyayya.

     4 Years letter

      Wata kyayakwar yarinya ce wadda baza ta wuce  4 years  ba ta shigo parlour tana kuka ta fada jikin sadiq dake zaune saman three siter yana karanta newspaper idanusa manne  da farin glass yana sanye cikin  English wears ya qara kyau ya murje hutu ya zauna masa ya qara girma, cikin shasheqar kuka ta ce, "Daddy ka ga yaya Aslam ya amshe min baby wasa na ko" daukar ta sadiq yayi yana lallashita ya ce, "sorry little Mom, rabu da shi zan siya maki sabi okey" fatuha da fitowar daga kitchen kenan jin kukan little Mom, tana sanye cikin green lace tasha kyau har ta gaji ta ce, "Wai me yasa Aslam baya jin magana ne, duk wani neman fita ya iya? zai shigo gidan ya same ni ai sorry dear" yar yarinyar dake jiki sadiq sunan ta kausar amma suna kiran ta da little Mom saboda sunan margayiya kausar aka saka mata sosai fatuha ke ji da ita saboda ita da kanta tasa sadiq yasa sunan, yanzu haka sun koma abuja da zama fatuha ta gama karatun ta aiki take angel kuma na university.

          Kasancewar lokacin lunch yayi kowa ya halara dining area suna lunch suna dariya, sadiq ne ya curo wayarsa dake cikin aljihu yace selfy su duka suka matso tare da saki murmushi happy family life.

           Tamatubihamdulillah

  A nan na kawo karshan wannan littafi nawa mai suna captain sadiq, ina mai miqa godiya ga dinbin masoyan wannan littafi.

  Abinda muka fada dai-dai da wanda bamu fada dai-dai ba Allah ya yafe  mana.

   Ina godiya irin sosai din nan ga Aunty  Raheenat da ta bani goyan baya wajan rubuta wannan labarin tare damin good editing dan ya qayatar da masoya wannan novel,  ina miqa godiya ta irin sosai din nan muna mugun tare.

    Gamai buqatar littafi na ga number ta kamar haka 07063683025

Gargadi: Ni Salma Mas'ud Nadabo ban amince kowa yayi anfani da littafina Captain Sadiq tako wacce Siga ba, duk wadda tayi\Kayi na bar mutum da rabill izati dan haka a kiyaye.

Taku har kullun salma mas'ud nadabo
Chapter 67 · 0% Book details