← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 67

Sashe 54

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Bata zame ko ina ba sai part din sadiq tun a parlour take kwallawa sadiq kira "Daddy..! Daddy.! Daddy..! Sadiq da fitowarsa daga wanka kenan yaji irin kiran da angel ke masa da sauri ya fito parlour tsaye ya  ganta tana  hakki  tamkar  wace  tayi tsere idanu ta  sunyi jawur  tashin  hankali  ya  fito  6aro-6aro a fuskarta tana  jifan  sadiq  da  wani irin kallo mai  cike  da  tuhuma, kirjinsa  ne  ya  qara  harbawa takowa  yake tamkar  me  sand'a ganinta da kati rike a hannu watsar da katin angel tayi suka  watse a  qasa tana kuka da  karfi  ciki daga  murya ta  ce, "menene  wannan daddy menene..! Sadiq  daya  rikice  ganin  abinda  angel  take  jikinsa na rawa ya  dauka ya  kasa  furta koda  kalma daya  angel ta  ce, "Dama daddy ba kai zaka auri Aunty fatuha? Mai  yasa  zaku  min  haka, ni  zaku  rusawa  farin  ciki, wallahi daddy ba zan ta6a zama da wata a matsayin uwa ba idan ba fatuha..! ta ida zancan tare da zamewa a qasa tana kuka kamar ranta zai fita, mamaki ne ya lullu6e sadiq bai ta6a tunanin angel bata san yadda abun yake ba, a hankali ya  qaraso kusa da ita tare da d'aga ta ya rungume kuka take sosai ta ce "Daddy in dai kana son farin cikina ka fasa auranka da Aunty Basma ayi da fatuha..! idan ko baka so a daura da Aunty Basma"
     "angel me yasa baki son Aunty ki Basma? ya fada zai qara bude baki ya qara magana angel ta  dago  daga  jikinsa  tana  jifansa  da  wani irin   kallo na mamaki ta ce "Daddy baka so na, duk  kai  ka  jawo, me  yasa  baka  aureta  ba  tuntuni  ba..! Sadiq  zai  jawo ta jikinsa da  karfi  ta ce, "Just leave me alone daddy don't...! ta  zaro  ido waje tana  kallonsa ta fita da gudu daga part din har ta bangaje fatuha da ta biyo ta lokacin da ta fita da gudu daga bedroom din su, kallo sadiq tayi dake tsaye ya kame kansa idanusa  sunyi  jawur, hawaye ne suka cigaba da yima fatuha zarya itama juyawa tayi da gudu ta bar wurin, zamewa sadiq yayi a gurin ya zauna hawaye  na  gangaro  masa  da  gaskiyar  angel  laifin sa  ne  shi yayi  wasa da  damarsu tarin da yazo masa ba  shiri  ne ya sasa miqewa ya shige toilet da gudu jini kawai ke fita yana tarin wanke face din shi yayi ya jingina da bangon toilet.

      Angel na shiga dak'i ta fada saman bed ta saki kuka, fatuha ce ta shigo dak'i dagowa angel tayi cikin d'aga murya mai sauti ta ce "Just leave me alone, bana  son  ganin  ku  ke  da  Daddy..! ta buga kofar daki'n da karfi zamewa fatuha tayi baki'n kofar ta saki kuka me cin rai dakyar ta iya jan jiki ta koma bedroom dinta bakin window fatuha ta tsaya tana raira kuka.
          a hankali iska ke kadawa kasancewar hadari ke akwai, a hankali ruwa ya fara sakowa mai cike da sanyi da karfi rufe window fatuha ta yi ta zame gefen gado ta cigaba da kuka, haka bangaran angel  ban da kuka ba abinda take, tana tuna irin rayuwar da su kayi a baya cikin ji dadi, haka shima sadiq rayuwar su yake tunawa a baya me cike da so da kwanciyar hankali, kuka fatuha ta Kuma saki tare da jawo picture din sadiq tana kallo tana tuno lokutan da yake yi mata fada farkon zuwan ta gidan, dariya take mai kuka-kuka ta daura hannu ta saman picture din ta ce "Mai kyau ina son ka.! tun bansan me so ba nake son ka amma sai gashi lokaci d'aya na rasaka, rashi  na har abada harma  da angel zan zauna da wanda zan koyawa kaina son sa" wani saban kuka ne ya kubuce mata.

       Haka suka wuni ranar cikin kunci. duk yadda su Hanan suka tanbayi fatuha mike damunta? sai tace masu headache ke damun ta, angel ko fir taqi cin abinci dan ko kofar daki'n taki budewa, fatuha tayi magana tayi magana har ta gaji part din sadiq ta shiga yana zaune a parlour ya jingina da bango.
     a hankali fatuha ta qaraso gaban shi cikin muryar kuka ta ce, "Mai kyau.! bude ido yayi na kallon fatuha kamar wanda ya dade bai ganta ba ta  cigaba  da  cewa, "mai kyau dan Allah kayi ma angel magana ta ci wani abu tun safe ta rufe dak'i taqi fitowa? sai faman kuka take please ka mata magana" lumshe ido sadiq yayi ya ce, "Fatuha I don't now how to do angel bazata saurare ni ba, sai dai idan zan bi abinda take so, kuma  ba  zaiyu  ba  bakin  alqalami  ya  bushe" kuka fatuha ta kuma sadiq d'ago ta sadiq yayi yana lallashita, sun dauki mintin 30 yana rungume da ita kanta ya dago yana kallon kyakyawar fuskarta ya kumbura ya ce  "Ina sonki Fatuha..!

        Ina kaunar ki ! tun ranar da kika shigo gidan nan Allah ya jarabce ni da sonki, a da Ina tunanin wasa ne a yanzu da nake shirin rasaki na gane cewa kece farin cikina, ke ce abin alfabarina, kevce annurin zuciyata, ban taba tsamani zan iya son wata diya mace ba, bayan rasuwar matata ba sai gashi Allah ya hadani da wacce idan na rasata ba makawa mutuwa zanyi, wallahi fatuha zan iya mutuwa idan kin zama malakin wanina, wayyo Allah na 😭 nayi zurfin ciki na kin bayanar miki da ke ce linzamin zuciyata, da ace wani ne ba majeed ba koda Zayn ransa komai nawa bazan bar masa ke ba, sai dai kash majeed ya wuce duk yanda kike tunani a wajena ina son majeed son da zan iya sadaukar masa da komai nawa ciki Kor har da ke, ya ida zancan sa hawaye na ciki ba da ambaliya a fuskar sa,  Majeed da tunda Sadiq yafara magana yake tsaye baki'n kofa basu lura dashi ba domin sunyi nitsa a duniyar su ta masoya, kamar gumki ya zama zufa ne ke fito masa a ko ina, wani irin jirine yake daukarsa ji yayi kamar ya kurma ihu domin a tunanin sa mafarki yake, dakyar da taimakon addu'a yabar wajen ko gabansa baya gani, yana zuwa falo ba kowa da sauri yayi waje.

     Fatuha Ko wani irin farin ciki ne ya kamata, takara shigewa jikin Sadiq , A cikin zuciyar ta ta ce "Ya Allah na gode maka, ashe bani kadai nake haukana ba, kuka ta fashe dashi da ta tuna cewa baki'n alkalami ya riga ya bushe daman Sadiq yasan bazata iya bashi amsa ba, dan haka ya kara rungume ta suka ci gaba da kukan su abin tausayi😢.

         Majeed Na shiga motar sa ya jata da karfin tsiya, da sauri mai gadin ya bud'e masa gate saura kad'an ma yabi ta kansa , ikon Allah bala maigadi yace domin abun yayi matukar bashi mamaki Allah ya kyauta yace yashiga dakin sa ya kuna redio yana saurare.

          Gudu majeed yake saman titi kamar zai tashi sama hawaye na bin fuskarsa , kuka yak'e sosai gashi kuma yana tuki na fitar h'ankali duk inda ya huce sai an bishi da kallo, yana shan kwana wata babban mota ta shiga gaban sa ji kake  kuuuuuuuuuuuuu😭🙆‍♀Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una.

  Vote
       Comment

Written by
Salma mas'ud nadabo

Edit by
Raheenat

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.CM

87_88

this page is for you Aunty Rahenat ina jin dadin yarda kike bani goyan baya tare da min good editing and every single person that always comment on this novel, I am in love with your comments

Firgigit sadiq yamike yana sauke ajiyar zuciya, ya jiqe sharkaf da zufa dakyar ya iya miqewa ya bude fridge ya tsiyayo ruwa cup yana sha. tarine ya sarkesa lokaci guda da gudu ya shige toilet yana aman jini dakyar ya saita kansa ya dawo saman bed yana furta duk addu'ar da ta zo bakinsa yana maida numfashi, bai taba mumuna mafarki irin haka ba, kuka ne ya kubuce masa dan baya fatan ranar da majeed zai rasa rayuwar sa saboda furucinsa a kan fatuha, wayarsa dake saman bedside drawer yayi saurin rarimowa ya fara kiran layin majeed kira biyu zuwa uku majeed ya dauka da alamama yayi nisan bacci ya furta, "Hello baby.! hamdallah sadiq yayi tare da sauke sanyayar ajiyar zuciya ya furta, "dama wani abu zan tanbaye ka tunda bacci kake shikenan..! sannan sadiq ya katse wayar tare da komawa toilet ya dauro alwala yana rokan Allah ya rage masa son fatuha a ran sa.

***
Kiran sallah asuba ne ya tashi fatuha alwala kawai ta daura ta gabatar da sallah, bayan ta idar ne ta wuce daki'n angel a hankali ta murda kofar taci sa'a ta bude cikin nutsuwa ta shigo angel da fitowar ta daga toilet kenan ta daure fuska kamkar bata ga fatu ba ta jawo hijabinta tatada sallah.
Bakin gado fatuha ta samu ta zauna tana jiran jidda ta idar da sallah, ko da ta idar bata kalli inda fatuha take ba sai ma qoqarin barmata dakin da take, riqe hannunta fatuha tayi cikin sanyi murya ta ce, "Angel fushi kike dani ko? shuru tayi kamar ba da ita fatuha take ba sai ma qoqari zame hannuta da take jin ta kasa zamewa ya sata sakin kuka tana cewa, "Ni ki sake min hannu ki kyale ni tunda baki son babana? kin zabi ki zauna da wani ba daddy na ba..! hawaye ne suka fara yima fatuha zarya tana girgiza ma jidda kai ta ce, "Angel ya za ayi nace bana son abban ki? please ki daina fushi dani.! fatuha ta fada tana shafa fuskar angel cire hannu fatu angel tayi ta ce, "Idan har kuna so na kuma kuna son farin cikina a cikin gidan nan to ku fasa auran da zakuyi daga ke har daddy..! ta fada cikin daga murya sannan ta fita ta barma fatuha dakin kuka fatuha ta saki tana furta, "na shiga uku wannan wani irin abune gabaki daya duniya ta mana kunci, ya Allah ka kawo mana mafita.! fatuha ta fada tare da tashi ta bar dakin.
Chapter 54 · 0% Book details