← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 67

Sashe 3

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

                          *****
        Sadiq ne  ya fito daga toilet sanye da bathrobe a  jikin shi ahankali ya leka fuskar Jidda da ke bacci yana shafa kanta, ahankali ya kai mata kiss a goshi, bud'e ido tayi ta sakar mai murmushi  ta  ce,  "daddy good morning"
  "morning  sweetheart oya tashi muje ayi wanka"
  "tam papa.! d'aukar ta yayi suka shiga toilet ya wanke ta tas suka fito yana mata cakulkuli tana gantsarewa tana dariya ta  ce, "daddy please stop"
  "naqi dear ba daddy zaki ma wayau ba"
"no daddy ba wayau zan ma ba fa"
"to menene to.!
  " uhm wani abu" ta ida tana hada hancin ta dana sadiq, kamar an mintsile sa ya ce, "oya tashi na shirya ki"
"tam papa" mai ya shafa mata ya sa mata jeans blue and pink t-shirt mai kyau da manyan flowers ya raba mata gashin ta gida biyu ba k'aramin kyau tayi ba Masha Allah peck ya mata a kumatu  ya  ce, "oya wuce wajan grandma, gani nan zuwa dana gama shiryawa"
"to daddy" ta fita da gudu ya bita da kallo shiryawa yayi cikin kakinsa na sojoji tare da gyara sumar sa ba K'aramin kyau yayi ba wow duk inda namiji ya ke to sadiq ya kai, briefcase nashi ya d'auko wanda ke gefen gado tare da ficewa dinning area ya nufa.
      "Mom good morning "
"morning son how was your night?
    "cool Mom and your's? ya ce tare da kai mata peck kumatu ta  ce, "the same"
"good" atsaitsaye yayi break saboda ya kusa makara ya fita yaran shi suka fara qamewa tare da  miqa gaisuwa motar shi wadda tasha wanki benz fara mai daukar ido ya shige yaron sa ya rufe suka fice daga gidan.

                           *****
          Baffa da fatuha ne a gona sai aiki suke cikin jin dadi fatuha na ma baffa hira, sosai ya ke jin fatuha a ranshi fatuha ce ta katse shurun da cewa, "baffa zanyi fitsari"
  "to fatuha ki qarasa can gefe kiyi kin ji, ki kulla da kafar ki"
  "to baffa" ta kutsa kai cikin gona sai da ta tabatar baffa baya hangen ta sannan ta lalla6a ta qara shigewa jejin  wani sasak'e  icce ta d'iba ta kule a leda, tana dariya ta matse azanin ta baffa da yaji shure ne ya fara kwala mata kira da gudu ta qaraso tana cewa, "baffa gani" tana hakki
  "yauwa yar albarka yo Ina kika shige yin fitsarin" baki ta washe ta qara gyara zanin ta hannuta ya ja suka zauna suna cin dumaman tuwon da inna ta aiko masu da shi suna gama ci bacci ya kwashe fatuha baffa ya ce "ikon Allah har kinyi bacci kenan.. ya tashi ya cigaba da aikin shi.

                          *****
      Cikin natsuwa yake aikin shi a office, office d'in Masha Allah sanyi AC sai ratsawa yake sosai, abokin shi majid ne ya shigo dauke  da  sallama ya ce, "ah big man ashe ka shigo"
   "yap tun 8:00am.. hannu ya mika masa suka gaisa ya samu guri ya zauna ya  ce, "big man ya Mom and sweetheart?
  "lafiya lau yauma rigima tamin zata biyo ni taga uncle majid"
  "Allah sarki me yasa baka zo min da  ita ba"
  "haba wallahi tana zuwa nan zata cikani da to much of surutu"
    "uhm kai dai ka sani mutun sai muskilanci"
    "naji d'in idan wannan surutun ya kawo ka to ka fita"
    "to ban fita tunda ba kaika kawo ni ba"  shuru sadiq yayi ya cigaba da aikin shi kiran sallah la'asar ne yasa suka fito su kayi sallah  suka koma.
         bashi ya dawo gida ba sai 5:30pm part nashi ya shige ya yayi wanka ya wuce bedroom din Mom  zaune take sama sofa tana karanta azkar yayi sallama ya mata peck Jidda ce ta rugo ta bashi hug ta  ce, "dady I miss u"
  "miss u more dear..!

      After ya gama lunch ya shirya Jidda da kanshi ya ja hannu ta suka je parking space, yaran shi har sun taso ya d'aga masu hannu alama su kad'ai zasu  kaitsaye gidan Anuty bilki ya nufa.

       Dai-dai wani madaidaicin gida su kayi parking mai gadi ya wangale masu gate, Masha Allah gidan ya had'u sosai plat ne mai kyau su hannan na filin gida suna wasa ganin uncle sadiq ya sasu rugawa aguje suna mai oyoyo, ya chabe su yana masu wasa tare suka karasa palour Maman hannan na ganin shi ta washe baki ta qwalawa talatu kira ta kawo mai abin motsa baki, dangin su fruit da sauran su har k'asa talatu ta duk'a ta gaishe shi Aunty ta  ce, "ah baby yau kai ne a gidan nawa hala Mom ce tace ka zo to yayi" smile  yayi  ya  ce, "oh kina nufi ban zuminci ko?
   "kamar hakan dai"
  "a'a aunty ke ma kin san bana zaman a naija sosai, but now na dawo Nigeria zanrinqa zuwa har saiki gaji dani"
   "toh shikenan Allah yasa da gaske kake"
  "haba anuty billy" ya ida zancan yana shagwabe fuska "ohni baby wai yaushe zaka daina shagwaba, duba fa har da d'iyar ka budurwa" dariya ya fashe da  ita, "ni dai sister kin samin ido wallahi" sannan ya kora lemo "toh naji na daina"
   "uhm wai ina mai gidan"
   "bayanan yana dubai"
"ok..
"sai end of this week zai dawo"
    "Allah ya maido shi lafiya"
"ameen" hira sukai sosai da yar 'uwarsa Kiraye-kirayan sallah magrib ne yasa suka tashi sadiq ya wuce masallaci.

                         ********
      Misali karfe 5:30pm har baffa ya gama komai a gona fatuha na kwance kamar maiyin bacci dare, saboda yasan halin ta in ta kwanta bacci bata san a tashe ta, yasa hannu  ya d'auke ta har suka iso gida inna na ganin su ta washe baki, tare dayi ma malam sannu da zuwa tare da kar6ar fatuha da ke sharar bacci d'aura alwala baffa yayi ya tafi masallaci bashi ya dawo ba sai bayan isha'i, lokacin fatuha ta tashi tana cin abinci hira suka d'an ta6a sama-sama sannan suka wuce ma kwantan su Inda fatuha ta matsu gobe tayi dan ta aikata abinda ke ran ta.

                         *****
      Bayan isha'i sadiq ya dawo yayi sallama da sister nashi sannan ya raba ma su hannan tsarabar su, karku  so kuga murna wajan su bayan sun fito haka ya biya da Jidda wajan shan ice cream ya mata siyaya sosai sannan suka dawo, tun akan hanya ma bacci ya d'auke jidda dan haka tana kwance a kafad'ar shi cikin sallama ya shigo Mom na palour tana kallo ita da baba jummai, baba jummai ce ta tashi washe da baki tare da amsar jidda shi kuma ya wuce dakin shi yasa ice creams din a fridge.

        Baba jummai tana zuwa d'aki tayi ma jidda wanka ta samata night dress nata blue riga dai-dai gwiwa, shima yana zuwa d'aki wanka yayi saboda ya gaji sosai ko da ya fito Mom har ta shinfid'e jidda saman bed kayan bacci shi yasa tare da jawo laptop din shi yana shan coffee ya dad'e yana aiki sannan bacci ya dauke shi.

                            ****
        Kiraye-kirayan sallah asuba ne ya tada fatuha bakin ta washe ta  ce, "kai narantse da Allah jiya da kyar bacci ya suran yadda na matsu yau tayi, wallahitalahi yau Rabi'u sai ya gane kuran shi qur'an ciki sauri tatashi  tayi sallah.

   Yau dai ba laifi fatuha ta taya inna aiki sosai ba dan komai ba sai dan tabarta ta fita, saida suka gama komai ta gyara zaman zanin ta wadda kullun jiya na leda na habar zanin ta sannan ta ce, "inna zani gidan su fatsima"
   "to fatuha karki dade"
       "to inna.. ta fita da gudu gidan su fatsima ta shige inna fatsima na tsakar gida tana wanke-wanke gaisheta tayi ta amsa da  cewa, "fatuha ya inna"
"inna lahiya lau"
    "ki ce ina gaishe ta inkin koma gida"
        "to za ta ji inna, ina fatsima?
"tana uwar d'aka"  fatsima da ke shara bacci saman tabarma fatuha ta d'aka mata bugu ta  ce,  "ke tashi..! firgigit ta tashi "kai fatuha.."
  "ke banza tashi muje"
    "oh na tuna fa Qur'an ban san sanda bacci ya sure ni ba" dankwalinta ta daura suka fita suna tafe suna tsokana dai-dai wata gona suka ci birki Rabi'u ne gindin bishiyar mangwaro da alamar rake ya gama sha bacci ya dauke  sa  saboda duk ga abin rake zube, lafewa fatuha  tayi  jikin bishiyar bedin ita da fatsima suna lekyan shi fatuha ta ce, "fatsima bilahillazi yayi bacci" ta kwashe da dariya "ai sai ya ci uba sa" qulin leda ta ciro daga habar zanin ta  ta nufi Rabi'u cikin sand'a ta bud'e ledar ta zuba masa tana k'ok'arin rugawa da guda bayan bedi Rabi'u da ke bacci cikin bacci ya fara jin rad'ad'i na susa ba arziki ya tashi yana soshe-soshe, yayi zuru-zuru su fatuha da ke bayan bishiya sai dariya suke sannan suka fito daga nesa dashi  ta  tsaya ta kwalamasa Kira ya waigo ta  ce, "ai dama na fad'a ma kwarankwatsi ba'a buguna na hakura" fatsima ta bushe da dariya ta ce,  "ka je gida mai tafasa tama magani kaji rabe' dagowa yayi idanun shi sunyi jaaa saboda  azaba ya  ce, "bala'iiiii zan ci uban Ku dama  kune kuka fesa min asosa? narantse na sha magani sai na zo har gida na ci uban ku"
    "yo zancan banza, ka zo muk'arama wani" injin fatuha taja hannu fatsima suka bargun suna dariya shikuma Rabi'u na soshe-soshe
CAPTAIN SADIQ
👮
Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
      blood sister deejah
Follow me on wattpad: salmamasudnadabo

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄

                      7_8
Chapter 3 · 0% Book details