← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 67

Sashe 33

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

     Kiran sallah ne ya tashi fatuha toilet ta shiga tare da yin wanka  tare da dauro alwala daure da towel tafito  Dan karamin towel na hannunta tana tsane jikin ta dashi,   shafe jikin tayi da lotion tana gamawa tabude wardrobe ta  ta janyo wasu riga da sket masu stone's a jiki masu kyau   tana gama sasu ta dauko aftar dress ta aza bisa domin  gabatar da sallah tana idarwa ta koma  saman bed ta kwanta bacci ya qara kwasheta, ba ita ta tashi ba sai karfe bakwai kallon agogwan dake manne jikin daki tayi tare da yin miqa toilet ta shiga tayi brush ta fito tare da sharce sumarta ta kwanta a gadon bayan ta a hankali ta bude kofar daki ta zuro kai ta laleqa taga ba kowa fitowa tayi ta nufi dining area tana qaraso wa taga sadiq zaune cikin shirin shi na unform yasha kyau har ya gaji dago eye's ball's din yayi su kayi ido hudu da  fatu, kauda kai yayi ya cigaba da breakfast gaisheshi tayi ya amsa a taqaice qoqarin barin gun take har ta juya yace "Fatuha.! waigowa tayi hakan yasa iska ta hura gashin kan ta har ya shifi fuskar sadiq lumshe ido yayi tare da ware su a kanta itama din shi take kallo kauda kai yayi ya ce "Ki dawo kici abincin ki" washe baki tayi tare da jan kujera ta zauna saving din kanta tayi tare da janyo plate din gaban ta Sadiq kallon ta yake ta qasan ido hannun hagunta tasa ta gyara gashinta da iska ke yawo da shi ta zura hannun ta, cikin plate ta fara cin abincin, chips ne da farfesun kifi wani irin dadi ya mata sai kada kai take tana ci sadiq mamaki qazantar fatuha yake, cin abinci da hannu ko wankesu batayi ba kallon ta yake sosai dagowar da zatayi da kanta ta  kai wata lomar sukayi 4 eye's murmushin karfin hali ta masa tana qoqarin boye hannu ta dan kwata-kwata ta manta yana wajan kauda kai yayi tare da daukar briefcase din shi kallon shi fatuha take tayi rau-rau da ido ko kallon ta baiyi ba yasa kai ya fice, ture plate din tayi take nan taji abincin ya gundire ta, kwashe kwanikan tayi ta kai kitchen a nan ta ci karo da rabi'a na aiki gaisheta tayi ta amsa cikin fara'a taya ta aiki fatuha ta shiga yi tun tana  hana ta har ta kyale ta, kusan tare sukayi komai na launch sannan suka jera a dining area bayan sun kamala fatuha ta shiga rokar rabi'a kar tatafi ta barta ita kad'ai aiko taci sa'a rabi'a ta tsaya taji dadin hakan sosai, dan haka ta wuce part din sadiq ta gyara shi tas ta dawo parlour suka cigaba da hira da rabi'a ko da aka kira sallah azahar  tare sukayi sannan su kaci abinci, sai kusan qarfe hudu rabi'a tayima fatuha sallama, fatuha bata ji dadi ba amma hakanan ta hakura ta zauna kiran sallah la'asar ne ya sata shiga bedroom ta shiga toilet tayi wanka tare da alwala saboda yau tasha aiki ba laifi wata hadadiyar riga da isket ta kuma sawa, hijabinta ta zura tayi sallah bayan ta gabatar da sallah ta cire hijabin ta dawo parlour, jin zaman parlour ya isheta ta yasa ta fita farfajiyar gida su ola da Sunday ne da sauran yaran sadiq suketa shawagi a gidan resting chair ta samu ta zauna tare da jingina da kanta ta lumshe ido wani iska ke kadawa mai dadi da sanyi, Sunday ne ya zuguro Emeka dake ta kallon fatuha har yana lashe baki ya  ce, "hey Emeka stop looking at her, mind ur business this girl past ur level  na Oga consin sister be that"
     "I don't now fa amma this girl na beautiful"
    "Oh u no go stop looking at her I will tell  Oga"
     "sorry Sunday haba kar muyi haka da kai"  Emeka ya fadi cikin hausar sa mara dadi Sunday ya  ce, "leave me alone" Sunday ya fada
      "sorry lemme leave the place ma" Emeka tabirim bala mai gadi ya koma duk abun nan da sukeyi fatuha bata sani ba.

      Yau yasha aiki sosai wajan a office sai kusan yama likis sadiq ya nufo gida, yana zuwa bakin gate horn yayi bala mai gadi ya wangale masa gate ya kunno hanci motar shi, hango fatuha yayi harabar gidan  saman resting chair gashin ta ya bage kusan rabin qirjin ta duk waje suke domin riga da isket ne ajinta sun  dan matse ta sosai  dakyar take numfashi,  Emeka da ke gefan bala mai gadi sai kallon ta yake, yaransa sadiq yake  bi  da  kallo  wayanda  ke  harabar  gidan  kusan  rabin su  hankalinsu  na  kan  fatu,  take  farin  cikinsa  ya  d'auke lumshe ido sadiq yayi tare  da  ware  su yana ji wani  abu  mai  zafi  yana  masa  yawa mota ya  ja da karfi dai-dai parking space yayi parking ko dai-daita parking  baiyi ba ya fito cikin zafin rai fatuha dake kishingide ya nufa cikin zafi rai ya daka mata tsawa da  cewa, "me kike  a  waje  mai  ya  fito  dake? sadiq  ya  rintse  ido  yana  ta  masifa ganin  fatu  ta  tsare  shi  da ido  duk  ta  rud'e  sam  ta  kasa  gane  masifar  me  yake  mata mara  dalili  cike  da  masifa  sadiq  ya fisgota ba  shiri  tayi  masauki  bisa fafadar kirjinsa tana  sauke  numfashi  cike  da  tsoro  yanayin  sadiq  matse  mata  hannu  yayi sai  huci  yake   kamar  zai  hadiyi  zuciya  ya  mutu  saboda  masifa, ware ido tayi tare da saka masa kuka saboda  masifar  da  sadiq  yake  yayi  yawa janta  ya shigayi tana  rike  hannusa  tana  kuka  tana  cewa,  "mai  nayi  kuma  mai  kyau  Allah  banyi  komai  ba" ya cigaba da janta  cikin  zafin  rai  sai da ya zo parlour  yayi wurgi  da  ita saman kujera har sai da kanta ya bigi kujera kuka ta qara saki tana kallon sadiq dan bata san laifin data masa ba,  shima  d'in numfashi  yake  saukewa  cike  da  6acin rai cije  lips  yayi  yana  jin  wani  suya  a zuciyarsa  mara dalili, kallon ta yake ido cikin ido matsowa yayi daf da ita har tana jin saukar numfashinsa idanusa sun  kad'a  sunyi  jawur  rintse  ido  fatu  tayi  tana  kuka  mara  sauti hannu  yasa  ya matse mata fuska cikin daka tsawa yace "Uban waye yace ki fita waje haka? ya fadi a tsawa ce har cikin kanta sai da taji tsawar da sadiq ya mata runtse ido tayi tana girgiza kai tana kuka sakin fuskar yayi ya ja gashin kanta har saida ta saki qara tare da rushewa da wani sabon kuka cikin  daka  tsawa  sadiq ya  ce, "idan na qara ganin ki kin fita farfajiyar gidan nan baki sa hijabi ba sai na kona gashinan" ya ida zancan tare da matse mata fuska da karfi kuka ta kuma saki tana kallon sadiq wani irin tsanar shi na fizgar ta, lumshe ido tayi tana jin zafi da radadin, wani wawan tsaki sadiq ya ja tare da tura ta  ta bige da kujera sannan ya dau briefcase din shi ya haura sama da  sauri tamkar  zai  tashi  sama, kuka ta saki  mai ban tausayi.

     Yana shiga parlour shi ya wurgar da briefcase din shi ya zauna bisa kujera tare da lumshe ido, yana  sauke  ajiyar  zuciya wata zuciyar ta ce masa "Kai sadiq ina ruwan ka da harkata? idan ma tsirara zata dinga yawo me ruwan ka? runtse ido ya kuma yi" wata zuciyar tace masa "Ko dan saboda tarbiyar diyar ka ka taka mata birki? saboda duk abinda tayi shi jidda zata kwaikwaya?" duk wannan zancan a zuci yake kiran sallah magrib ne ya tasheshi bedroom ya shige ya rage kayan jikin shi agurguje yayi wanka, yana fitowa ko mai bai shafa ba ya zura jallabiya a hankali yake sauko wa daga upstairs, inda ya bar fatuha har yanzu nan take tana kuka jin alamar tafiya ya sata dago jajayan idanuwanta  ta kalli sadiq, sadiq ma kallon ta yayi  tare da aika mata harara ya ja  tsaki mtss ya fice, kuka ta kuma saki sannan ta ja jiki ta shige daki tana alwala tana kuka har ta gama, haka tafito ta zura abaya tana idar da sallah ta cigaba da lazumi   har sai da aka kira isha'i ta tashi tayi sannan ta ja jiki ta koma bed ta cigaba da raira kukanta kanta har ciwo yake mata amma dan jaraba takasa daina kukan.
Chapter 33 · 0% Book details