← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 67

Sashe 60

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

               A hankali fatuha ta fara ware idanuta wayanda suka mata nauyi tana bin dakin da kallo, yunqurin tashi tayi ta kasa dakyar ta iya miqewa zaune dafe da kanta dake tsanata sara mata tamkar zai rabe biyu, ta juyo ganin sadiq kwance  kefan ta ya dagawa fatu hankali yunkurin sauka daga saman gadon ta je wajan sadiq  ta kalli drip din dake  hannuta, hannuta tasa ta cire drip din dake hannuta tana kuka da sauri ta matsa kusa da sadiq kuka tasa ganin halin da yake ciki kuka take sosai tamkar ranta zaifi saboda tsanin firgita da halin da sadiq yake ciki a hankali ta fara cewa, "mai kyau meya same ka haka, karka tafi ka barni ka ji idan babu kai babu ni ka ji sadiq d'ina, ina son ka handsome I love you more than how you think please don't leave me alone, na rokeka  nima mutuwa zanyi.! Sosai fatu ta rikice dan bata cikin hayacinta duk  tabi ta rude sai fama kuka take har sautin kukan ta ya fara fita waje Mom da shigowar su asibitin kenan suka shigo dakin dan duba jikin fatu dana sadiq.
                 kuka fatuha take tana mai cigaba da cewa, "mai kyau ka tashi wallahi na rasa ka mutuwa zanyi, Allah bana iya zaman aure da majeed please ka tashi, ni kai nake so kai ne farin ciki na ka ji sadiq" ta ida zancan tana kuka mai cin rai Mom ce ta jawo ta, ta rungume tana shafa bayan ta fatu na cewa, "Mom sadiq nake so Allah bana son majeed ku ce masa ya tashi karya tafi ya barni" kuka fatu ta kuma saki ta qanqame Mom "shhhh ya isa kukan haka fatuha, ki kwantar da hankalin ki kin ji indai mai kyau ne ya zama naki..! dagowa tayi tana kallon Mom da mamaki idanuta sunyin jawur lokaci daya kukan da take ya dauke tana jin kalaman Mom kamar ba dai-dai ta ji murmushi Momta sakar mata ta ce, "yes abinda kika ji haka ne,  yanzu ba kuka ya kamata kiyi ba kulla da mijin ki ya kamata kiyi idan kun dawo  kunji bayani gabaki daya" wani irin farin ciki ne ya lullu6e fatu wanda bata iya boyewa lallausan murmushi fatuha ta saki tana goge hawayanta da bayan hannuta ta qarasa bakin gadon sadiq tana dariya mai had'e da kuka tana cewa, "mai kyau kana jin abin da suke cewa wai da gaske na zama matarka, kayi sauri ka warke ka ji handsome.! majeed dake gefe smile ya mata yana daga mata gira wata irin kunya ce ta lullu6e fatu, sai yanzu ta tuna da su Mom da sauri ta miqe tana qoqarin ta fita daga dakin da gudu saboda tsabar kunya, Basma ce ta tare ta, "ina zaki je kibar mijin naki, ko kin mata kema baki da lafiya kina buqatar kulawa" waki-waki fatu tayi dan tama manta bata jin dadi, harara wasa ta aikawa Basma dan ta bata hanya ta wuce, gabaki daya dakin aka fashe da dariya, sunkunyar da kai fatu tayi.

            Khaleed dake gefe ne yaja Basma suka wuce gida dan ta samu hutu kafin anjima akaita dakinsa kusan a tare suka fito da majeed yana qoqarin bude mota, motar su ya jawad ta tsaya shida shukara suka fito tare da fatsima sai matsar kwalla take qarasawa majeed yayi tare da cewa, "haka ake sai ku fito min da mata ba tanbayar izini"  harara jawad ya aika masa  ya ce, "ka raina mutane ai matar taka zaka tanbaya mai yasa ta biyo masoya" ya kai masa duka ya goce yana dariya jawo fatsima yayi jikinsa ya rungume tsam cikin cool voice ya ce, "my wife me ya saki kuka haka kina so ki bata min kwalliyar ki" fatsima da tayi wiki-wiki tana raraba ido neman kwace kanta take dan rashin kunyar yan birni tafi karfinta kamar bai san mai ya kawo su asibitin ba, amma sai wani iskanci yake dan murmushi majeed yayi ya ja karan hancin fatsima washe baki fatsima tayi tare da rufe face nata (lol su fatsima anqaro wulaqanci😜)

          Bayan an gama shirya komai flight din su sadiq ya tashi sai London suna isa london babba asibiti suka sauka kusan amaran tare suka tafi, saboda suma honeymoon za suyi a chan Khaleed sai zuba ma Basma soyayya yake sai yanzu Basma ta gane me so yanzu ta san ta fara so ashe da ba so take ba, haka shima majeed sosai ya samu piece of mind har cikin ran sa yake jin son  fatsima  yana ta gwada mata so ita ko sai kunya yake bata,
                    ko da aka wuce da sadiq asibiti emergency suka wuce da shi saboda yana buqar aikin nan kusa fatuha ta kasa zaune ta kasa tsaye sai zarya take tana duk  addu'ar data zo bakin ta, fatima ce ta dafata ta ce, "fatuha ya kamata ko wani abu ne ki sama cikin ki, raban ki da abinci tun jiya insha Allah lafiya lau sadiq zai fito, da yardar Allah za'ayi aikin cikin sa'a kin ji" haka Basma da fatsima suka dinga bata baki sannan ta ci abinci, shima d'in d'an kadan ta ci bayan ta kamala cin abincin duk da ba wani ci tayi ba su fatsima suka mata sallama akan zasu wuce masaukin su, su huta anjima su dawo haka ko akayi fatuha ta dawo ta zauna haka shima majeed yana asibitin dan ba da shi suka koma masauki ba, sai kun san yamma likis aka fito da sadiq Alhamdulillah anyi aikin cikin sa'a tashi fatuha tayi tabi gadon da sadiq ke kai har aka bashi daki sannan doctor ya nemi ganin majeed, magunguna ya bashi tare da masa congrat ya ce, "an gama aiki lafiya kowani lokaci yana iya tashi sai dai yana buqatar kyakyawar kulawa jan ku," bakin majeed har kunne hamdallah yayi da godewa Allah ko da ya dawo albishirin da yayi ma fatuha kenan, curo wayarsa yayi bugawa su Mom yayi masu albishir sannan suka shaidamasa suma gobe zasu iso fita yayi ya bar dakin tare da shaida ma fatuha tare zasu dawo da su Basma to ta ce masa ta shige toilet dan ta dauro alwala.
Chapter 60 · 0% Book details