Sashe 58
Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A hankali yayi parking motarsa ya mata key, harabar gidan tsit ba motsin kowa sai motoci birjik kamar wajan saida mota, a hankali ya cigaba da takawa duk da yana jin jikinsa kuka-kuka ya fara ji sama-sama hakan ne ya sasa tsayawa tare da kallon agogo hannusa mamaki ne ya lullu6e sadiq a hankali ya fara bin inda kukan ke fita, fatuha ce zaune sama resting chair tana raira kuka, qarasowa yayi gabanta firgigit ta dago a tsorace ganin sadiq ne yasa fatu mikewa tsaye ta ruga da gudu ta fada jikinsa ta qanqamesa tare da sakin wani irin kukan, rungume ta sosai sadiq yayi yana jin kukanta har cikin ransa tamkar shima ya fashe da kukan ko ya samu sauki cikin zuciyarsa daurewa kawai yake, d'ago fatu yayi suna kallon juna jawo hannuta yayi suka zauna a hankali yake shafa bayanta ba wanda yace ma dan uwansa ko da kalma daya, sun dau kusan 5 minutes a haka fatuha ce ta dako tana kallon sadiq kamar yarda yake kallonta cikin sanyin murya ta ce "Uncle.! ya naji jikin ka da zafi? dan smile sadiq yayi ya ce "Nima haka naji jikin nawa" kallonsa take cike da kallon tuhuma da tanbayoyi fal a zuciyarta ganin yarda ya rame ya zabge amma sai ta kasa magana komawa tayi saman fafadan qirjinsa tayi lamo tana sauke numfashi a hankali, kunsan a haka suka zauna har bacci ya dauke fatuha idanuwan sadiq biyu yana kallon fatuha har sai da ya fara jin kiran sallah asuba sannan ya tashe ta ya ce, "Dear tashi asuba tayi?" qarayin lamo fatu tayi jikin sadiq ta qanqamesa shafa gashin kanta yayi a hankali ya furta, "Fatuha..! a hankali ta ware eye's ball's din ta, ta ce, "Na'am.!
"tashi mu shiga gida asuba tayi" jiki ba qwari ta tashi har tayi gaba ta tsaya chak idanuta taf da kwalla da sauri ta waigo kusan lokaci daya suka waigo da sadiq suna kallon juna cikin murya mai matukar taushi fatu ta ce, "Yau ne zan rasa farin ciki na.! yaune mafarki na zai rushe, ina ma ace dogon bacci nake na farka ahalin yanzu" wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo mata ta ce, "Yanzu duk wata rayuwa da mukayi zata zama tarihi mai kyau? Numfasawa tayi saboda muryarta dake sarkewa ta furta, "ina ma fatan alheri Allah ya baku zaman lafiya da Basma.! tana ida zancan ta fashe da kuka mai ban tausayi ta juwa sadiq baya rungume ta sadiq yayi ta baya tamkar karamin yaro hawaye na masa anbaliya cikin sarkewar harshe sadiq ya ce "Fatuha ki kasance mai biyaya a daki'n mijin ki kin ji, majeed na sonki please karki bari majeed yayi kuka dake dai-dai da rana daya, duk wanda yayi hakuri a rayuwa zai ga ribar haka..! ya ida zancan yana share hawayansa ya waigo da fatu suna facing juna yana sakar ma fatuha lallausan murmushi dayafi kuka ciwo, suna kallon juna da sauri fatu ta shige cikin gida.
Duk inda ka wuce hada-hada ake da shagali abinci ke ta yawo da kayan motsa baki, kaji ko har ture su ake da naman rago yan'matan amarya na zaune a daki, shirya fatuha ake saboda wudil za'a wuce da ita sai an daura aure aje dauko ta, tunda ake mata make up take kallon agogo tana irga mintinan da suka rage ta zama malakin majeed, hawaye ne taf a idanuwanta bayan angama make up din ta zura kayan ta atamfa mai ratsin green, pink, brown masha Allah kayan sun mata kyau tasha danqareriyar sarqa ta gold da yan hannu sai sheqi take, Aunty bilki ce ta leqo ta ce, "Fatuha ku fito ga motocin da zasu kai mu wudil?" gaban tane ya yanke ya fadi dan har wani jiri take gani a haka su fatsima suka sata tsakiya aka lullu6eta aka kaita wajan su Mom sukayi sallama, anata guda har suka fito harabar gida, mota suka shige driver ya ja suka har ba kan titi.
Wanka angwayan kawai suke suna shiryawa Khaleed ne ya kalli sadiq ya aika masa harara tare da cewa, "Wai ina kaje jiya? bala masa harara sadiq yayi ya ce, "Ina ruwan ka da inda naje? ka fiye sa ido, irin kune ana ruwa kuna irgawa" dariya majeed yayi ya ce, "Kai dai tashi kayi wanka kaji baby ko ni ban tanbaye ka ba sai shi, ga kayan ka can tun dazu na aje ma ina so yau ka kasance cikin farin ciki kamar kowani ango.! majeed ya ida zancan yana zura kayansa a hankali sadiq ya miqe ya shiga toilet majeed ya bishi da kallo tare da ida shiryawa, tunda sadiq ya shiga toilet yake kuka kamar qaramin yaro sai da yayi son ransa sannan yayi wanka ya fito.
ko daya fito Dr yakub ne kadai daki'n kallosa sadiq yayi tare da kauda kai ya cigaba goge jikinsa da qaramin towel, sai da ya gama shafe jikinsa da lotion mai kamshi da sanyi dadi sannan Dr yakub ya balo magani ya miqawa sadiq dan bata fuska sadiq yayi yace "Wannan fa? daure fuska Dr yakub yayi ya ce, "Magani mana" bai ida rufe bakinsa ba aka turo kofa aka shigo, murmushi sadiq ya saki ganin ya jawad qarasawa yayi ya rungume jawad zame jikisa yayi tare da bata fuska ya ce, "Sai yauma zaka zo? smile jawad yayi yana bin sadiq da kallo yarda ya zabge ya rame ya ce "Sorry baby tun jiya na zo kuma na zo nemanka aka ce baka nan, ya naga ka wani rame ka zabge kamar ana dibar ka ana miya ko duk hidimarce"dan lagwabe kai yayi yana murmushi ya furta, "Toh shikenan, bayan makara harda sheri, ina su Aunty shukura?
"tana wajan su Mom"
"ok.! Dakakiyar fara shada ya jawo white getzner tasha aiki ta gaji malin-malin su jawad ne suka taimaka masa ya shirya tuni ya fito yayi kyau masha Allah duk da ya rame idanusa sunyi ciki, bayan sun gama shiryawa suka fita
Zaunawa sadiq yayi tare da kallon agogo dake manne a bangon daki, karfe 1:30pm saura minti talatin a daura auran su, haka ya dinga dane zuciyarsa yana bata hakuri.
Suna isa wudil gida ya dau gud'a baba jummai ta fito da sauri tana cewa "Ladingo amaryar fa ta iso" inna washe da baki ta bude masauki da su fatuha zasu sauka kusan tare suka shigo, Aunty bilki na riqe da ita masauki suka sauka nan aka fara jera masu kayan motsa baki, kama daga waina alkubus sinasir tuwan shinkafa da lafiyayin kaji da lemuka, yan'matan amaryar ko alwala suka fara daurawa suna sallah kasancewa azahar tayi haka itama fatuha ta gabatar da sallah sannan suka zauna aka fara gudanar da biki.
gwaggo ce ta aiko a kira fatsima tashi tayi ta fita har Nana zata bita sai kuma ta dawo ta zauna, ko da fatsima ta isa gidan su shima cike yake da baqi, mamaki ne ya lullu6e fatsima babban abinda yafi daura mata kai har da dangin babanta, to ko suma bikin fatuha suka zo? watsar da zancan tayi tare da shigewa daki inda gwaggo take washe da baki gwaggo ta tarbi fatsima ta fara mata magana. (duk yarda naso naji me ake cewa na kasa ji, hakan yasa ni da Aunty Rahenat muka bar gun jiki a sabule lol.)
Duk inda ka waiga a cikin masallaci Sheikh Isyaka Rabi'u mosque ya cika da manyan mutune yan daurin auren, sadiq ne cikin din bin jama'a, a nata masa Allah ya sanya alheri duk wannan abu Dr yakub na lura da yanayin shi majeed ma sai murmushi yake saki daka ganshi kasan yana cikin farin ciki, haka shima Khaleed dan yasha kyau har ya gaji tamkar ango, gyara lasfika da kayine yasa gaban sadiq ya yanke ya fadi, kirjinsa ya bada dam zuciyarsa ta tsinke bugun zuciyarsa ya qaru rawa jikinsa ya dauka gudun jinin jikinsa ya qaru take wata irin zufa ta fara karyo masa bugun zuciyarsa na harbawa fat-fat dam-dam tamkar ana lugude cikin zuciyarsa, tabbas yasan ana daurawa ya zama gawa dishi-dishi ya fara gani yana ganin jiri maganar mutane na lunkuwa cikin dodan kunnasa da kwakwalwarsa, a hankali ya fara kutsawa cikin taron jama'a yana tafiya, yana tari mai dauke da gudan ji tamkar kaki zufa ta jika shi sharkaf a hankali yake takawa dan yanzu ya fara yin nisa da masallacin.