← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 67

Sashe 31

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Hira suka sha sosai Sadiq da Khaleed, basu suka tashi ba saida suka fara jin kiran sallar magrib,    alwala suka dauro a tare suka fito domin tafiya masallaci, ko da suka iso parlour ba kowa Khaleed sai kalle-kalle yake ko zai ga fatuha, hakan yasa Sadiq ya masa nisa juyawar da Sadiq yayi yasa Khaleed daga kafa bayan an gabatar da sallah suka fito daga masallaci direct gida suka dawo, basu zame ko ina ba sai dining area Sadiq ne ya shiga saving nasu lafiyayan tuwan shinkafa miyar egushi taji kaji da naman rago kamshi sai tashi yake, turawa Khaleed na shi yayi sannan ya zuba na shi tare da zuba masu juice a cup's, suna ci suna ta6a hira dan yau an hadu har basa gajiya da hira, bayan sun kamala suka dawo parlour da zama basu koma part din Sadiq ba wayar Sadiq dake aljihu ce ta shiga ruri hannu yasa cikin aljihu ya zaro ta sunnan da ya ganine manne a screen din ya sasa sakin smile, juyowa yayi ya kalli Khaleed ya ce, "gafa mutumin ka fa yake kira ni," murmushi Khaleed yayi ya ce, "kamar yasan ina nan" daukar wayar yayi tare da karawa a kunne ta daya bangaran majid ya ce "Hello big man"
   "Na'am.!
  "kana gida?
      "eh ina gida gani nan  tare da Khaleed,"
     "eyya kace ma0sa ina gaishe shi"
  "toh.!
   "yauwa dama so nake ka raka ni wata dinner please,"
    "dinner kuma? Sadiq ya maimai yana kwabe fuska  majid ya  ce, "ni dai ka rakani dan Allah nasan halin ka, yanzu ka fara min tsirfa"
     "au tsirfa ma zan ma ko? toh ban zuwa,"
    "haba kar muyi haka da kai mana please ka shirya kuma manya kaya zaka sa,"
     "bazan saba zafi ya isheni"
     "please kasa haba Sadiq nine fa"
     "toh  naji.!  naji.! ya ce masa tare da katse wayar yana kallkn Khaleed ya  ce, "ka ji ni da majid wata kuma dinner zai kwashe ni muje taso muje mu shirye muje,"
       "ni fa bana zuwa" harara Sadiq ya wurga ma Khaleed "lafiya.! Khaleed yace ya daure fuskar wasa "toh ai ji nayi ka ce baka zuwa"
    "wallahi ko aiki na can na jira na shiyasa yanzu haka fa gudo ma aikin nayi"
    "toh shikenan" part din Sadiq suka koma Sadiq ya shige bedroom tare da rage kayan jikin shi sannan ya shige toilet wanka ya sheqa ya fito daure da towel a jikin shi sai qaramin towel yana goge sumar shi lotion ya janyo ya shafa sannan ya bude wardrobe ya ciro dakakiyar shada shi brown tasha dinki da dark brown zare anmai irin dinkin nan na sarauta takalmin coffee colour yasa tuni ya fito yayi wani irin kyau, abinka da farar  fata  turare ya fesa mai kamshi da sanyin dadi tare da  manne agogwan shi silver sannan ya dawo parlour, khaleed dake saman two sitar  ya ce, "kai aboki na wannan sai kafi uban gayar kyau ai" smile Sadiq yayi ya ce "A hakan?
   "eh mana"
      "Cha6.!
   "so kake yan'mata suyi rushing kenan dama har yanzu kaqi yima angel Mom," smile Sadiq ya kuma yi ya ce "Nine Mom din jidda kuma nine daddy ta, so bata buqatar wata new Mom"
      "haka dai kake cewa lokaci nanan zuwa da zaka watsar da  wannan tunanin haka, ni ko ina sis naka har yanzu ban qara sata a ido na ba? dago ido sadiq yayi yana nazari wace sis can kuma sai ya tuna qaqaro murmushi yayi ya ce, "wai me sister na ta tsare maka tunda kazo kake zancan ta"
     "ah wallahi kawai yarinyar ta burge nine har na dan ji wani abu" kallon shi sadiq ya shiga yi kamar me neman wani abu a jikin shi can kuma sai yaja dan guntun saki ya  ce, "amma dai Khaleed wani abu ya shige ma kai ko? me za kayi da wa can yarinyar? yarinyar da ko 14 years bana tunanin ta kai, toh ka aure ta ka ji me? dariya Khaleed yayi  ya  ce, "wallahi aboki na baka kallon yarinyar nan wallahi irin sune idan suka ji kiwo kai kanka sai kayi mamakin abin da zaka gani"
     "mtsss har ka fara samin headache wallahi" wayar sadiq da tayi rurice ta katse ma Khaleed zance daukar wayar yayi ta daya bangaran majid ya ce, "Gani nan cikin filin gida ka fito mu tafi" to yace masa tare da miqewa  Sadiq ya kalli Khaleed  ya  ce, "tashi mu tafi dan zumudin har yazo," fita su kayi daga part din har sun kai bakin kofar fita sadiq ya ce "Ina zuwa"  parlour ya dawo tare da nufar dakin fatuha a hankali ya murda handle din kofar a zaune ya hango su fatuha saman daduma da alama yanzu suka idar da sallah, suna karatun AlQur'ani sallamar da yayi ne yasa fatuha aje Al Qur'anin tare da amsawa qarewa sadiq kallo fatuha tayi wani irin kyau ya mata kullun mai kyau qara kyau yake kauda idanuwan ta tayi, qarasowa dakin yayi jidda ta ruga ta fada jikinsa ta ce, "Daddy!
Na'am my angel.!
        "daddy ina zaka? zan bika"
     "angel ai yara basu zuwa" bata fuska jidda tayi tana shirin yin kuka tana dire-dire tana  cewa,  ni kam gaskiya daddy binka zanyi ban zama" langwabe kai sadiq yayi ya ce "Fatuha zo ki dauke ta" fatuha qarasowa tayi tana ma jidda murmushi ta ce, "yi hakuri kin ji jidda daddy nasan zuwa dake amma baya san dodo ya cinye ki  dodon yara yake ci" jidda ware idanuwa tayi tana kallon fatuha irin da gaske kike, sadiq ko wani irin dadi yaji yadda fatuha ke lalla6a jidda dan yasan idan ta kafa masa kuka har dinner fasa zuwa zai yi dan farin cikin jidda shine nashi, shafa kan jidda yayi ya ce, "kinji ko? ko mu tafin," maqe qafa tayi ta fada jikin fatuha dariyar da ke san zuwa ma fatuha ta guntse shima haka Sadiq peck yama jidda sannan ya fice ya fito lokaci Khaleed da majid suna ta hira yana qarasowa majid ya aika masa harara tare da cewa "Tunda nace ka raka ni sai ka shanya ni mtss"
     "oh haka nan zan bika banyi ma angel sallama ba ko? saima na fasa zuwa wallahi" hakuri majid ya bashi Khaleed dake gefe dariya yayi ya ce, "baku Gajiya da dirama wallahi har yanzu" murmushi su kayi tare da bude motocin su suka shige a tare da Khaleed suka bar unguwar.

    Sadiq na fita fatuha ta ja jidda toilet ta mata wanka itama tayi night dress suka sa tare da fitowa parlour, gidan yayi tsit ba alamar motsin mutane tsoro suka fara ji amma fatuha  daurewa take jidda kuka tasa mata ta ce  "Aunty"
      "na'am jidda"
  "Aunty ki zo muje part din daddy tsoro nake ji" shafa kanta fatuha tayi ta ce "Kiyi hakuri mu zauna anan" kuka jidda  ta fara rarewa fatuha hakan yasa fatuha daukar ta suka koma part din sadiq a parlour suka zauna fatuha ta kunna masu kayan kallo MBC 3 ta kai masu suka rashe suna kallon carton.

       suna isa wajan dinner  ke  da  wuya  kallo ya  koma  kan  su, wajen ya hadu   iyakar haduwa sun hadu duk wata mace dake wajan sai da ta yaba kyan su mata masu wayau a sace suka rinqa yaba kyan su marasa wayau ko har bin su sadiq suke, sadiq ko hade rai yayi kamar bai ta6a dariya  ba majid ko sai washe baki yake dama shi dan ina da yan'mata ne sunyi ciye-ciye da lashe-lashe majid sai da yayi kusan yan'mata biyar takaici ya hana sadiq magana  sai fuska da ya qara tsukewa kamar anmasa mutuwa, duk wadda ta zo tura kanta idan taga ba wasa a tare da sadiq sai ta ci birki ba su  suka bar wajan dinner ba sai 11:30pm lokaci sadiq har wajan ya fara hawa masa kai, ko da suka taho ba wanda yace ma wani qalla musanman majid ya san yana tankawa sadiq zai fara masa masifa dan yasan halinshi har harabar  gida majid ya saka hancin motar shi bala mai gadi sai daga masu hannu yake, tun kan majid ya ida parking sadiq yayi qoqarin fita dariya abin ya so ya ba majid amma baice komai ba yayi ribas ya fita yana shiga parlour ba kowa dama yayi tunanin haka saboda goma nayi jidda tayi nisan bacci bale kuma 11:30pm bedroom din fatuha ya bude a tunanin  shi suna ciki ganin ba kowa yayi tunanin suna part din shi haurawa yayi upstairs a hankali ya murda handle din kofar, TV ya iske nayi su tuni sunyi bacci, jidda ta dora kanta bisa cinyar fatuha, fatuha kuma ta jingina da kujera murmushi sadiq yayi tare da qarasawa ya kashe kayan kallon bedroom ya shige ya rage kayan jikinsa ya shige bathroom wanka ya sheqa ya fito sanye da bathrobe tsane jikin shi yayi da qaramin towel sannan ya zura night dress din shi parlour ya dawo har yanzu su fatuha bacci suke a hankali ya qaraso saman three sitar a hankali yasa hannu ya dau jidda bedroom ya kaita ya shinfideta parlour ya kuma dawowa, har yanzu fatuha bacci take a hankali sadiq ya kai hannu zai tashe ta sai kuma ya fasa gashin ta daya rufe mata fuska ya matsar tare da tsare  ta  da  ido yana qare mata kallo ya ga dai bacci take lumshe ido yayi tare da ware su, a hankali ya kai hannusa ya dauke ta aiko fatuha ta qara lafewa jikinsa tana sharar bacci yayi tunanin zai jita da nauyi amma sai yaji kamar ya dauki jidda a hankali ya sauke ta saman bed din shi ya ja masu blanket ita da jidda tare da qara masu gudun AC, sannan ya bude wardrobe ya ciro wani blanket din ya koma parlour ya kwanta saman three sitar ya dade kafin bacci ya dauke shi, zuwa can   bacci yayi awan gaba dashi.
Chapter 31 · 0% Book details