← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 67

Sashe 65

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Jawo ta sadiq yayi yana lallashin ta ya ce, "ai na ce na fasa tunda kina so yanzu" lamo tayi a jikinsa cikin cool voice ya ce, "My love me zaki ci? cikin shagwaba ta ce, "Dan wake" bata fuska sadiq yayi ya ce, "gaskiya babyna ba zaici mai da yaji ba," kuka ta fara shirin samasa ganin ba yadda zaiyi  haka ya fada ma baba asabe tayi mata dan wake ba laifi taci dan wakyan sosai da akayi har da side plate.

        Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda fatuha ke samun kulawa sai dai cikin tana mai laulayi ne sosai, kusan a tare suke laulayi da su fatima amma sai dai duk ta fiso wahala ga wani shegyan kwadayi da ya samata angel ko da taji Mom na da ciki murna ba'a magana Mom za tayi mata qani ko qanwa ta samu abokiyar fira.

      Shirye-shirye ake sosai na bikin Hanan dan yau duk kusan sun halara family house saboda yau ne za'ayi kamu, bayan sun gama exam din mathematics a school driver ya zo daukar fatuha bai zame da ita ko ina ba sai family house, a gajiye likis ta dawo yana sauke ta tashigo gida umma ce ta tare ta, ta  hada mata ruwan wanka ta shiga toilet ta fito kasancewar ansan yadda cikin ta yake farfesun kifi Mom ta mata mai dadi tana fitowa ta iske kayanta saman bed after dress ce ta zura sannan ta fito parlour tana fitowa ta samu su fatima suna ta kwasar  nasu farfesun, kwabe fuska fatu tayi tana kallon Mom da itama kallon ta take dariya daki'n ya dauka Mom ta jawo ta jikinta tare da bude mata kola ta fara feeding nata tana amsa sai janta suke ta fiye raki harara da dinga aika masu Mom ta ce, "taje tayi din kuma din ai kawai shuru kukeyi da baku rakin kuma raki ba'a sani sai ranar juyewa" ammi dariya tayi ta ce, "kai hauwa kina fama da surukan nan naki, kina shan drama" ya zanyi ammi, komai cikin walwala da jin dadi da soyayya suke dan sun samu gidan maza jan nasu ya zama kamar gidan iyayan su dan yanzu sunfi mazan ma samun qugun zama har qorafi mazan keyi saboda banbanci da ake masu anfifita matan a kansu musanman yanzu da suke da juna biyu..
Written by
      Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM

                      101_102

     Godiya ta musanman gare ku REAL-HAUSA-FULANI-WRITERS-FORUM wannan shafin naku ne, ana mugun tare irin   sosai din nan Allah ya bar zuminci Allah ya qara hada kanmu

          Qoqarin sa rigar ashobenta  take da mami ta dinka masu, amma sket din ya kasa shiga saboda hips dinta daya qaru, lagwabe kai tayi tana qara tura skirt din tana jin kamar tayi kuka jin an bude kofa ya sata waigowa sadiq ne ya shigo dakin, kuka ta fara rera masa tunkan ya qaraso gareta, qarasowa sadiq yayi da sauri ya dago da fuskar fatu da tayi shafe-shafe da hawaye ya ce, "My wife me ya saki kuka uhm? wani kukan ta qara saki ta ce, "Habibina ashobe na ya kasa shiga ta tun dazu nake jan sket din yaki shiga" ta ida zancan tana sa masa kuka jawo ta jikinsa yayi ya zaunar da ita saman bed ya ce, "Wannan ne matsalar?" d'aga kai tayi alama eh, "toh shikenan bani kayan na gani" amsar kayan sadiq yayi ya duba Allah ya taimakesa akwai space,  zaunawa yayi ya warware skirt din da rigar sannan ya miqa mata tasa maqale qafa tayi ita bata iya sa kayan hannu ta nauyi yake mata, lakace mata hanci sadiq yayi ya ce, "My love yau baby  na rigima ya saki ko? turo baki tayi gaba cike da shagwaba kiss nata sadiq ya fara ko ta ko ina ganin zai zarce yasa fatu samasa kuka, smile yayi ya ce, "sorry.! sannan yasa mata kayan shima shirya cikin manyan kaya sannan ya jata suka fito ko da suka fito lokacin su fatima sun shirya ita kadai suke jira ta fito, tana fitowa fatima ta ce, "Sai muje ko?  ta ida zancan tana aika mata harara wasa murguda mata baki fatu tayi sannan suka fice sadiq kuma ya wuce wajan angwayan saboda kamun ba maza.

          Suna shigewa mota fatima ta ce, "Ke haka ake? daga shiga sa kaya saiki maqale da miji"
      "kam me kika daukan to nayi din" ta fada tana aika ma fatima hararar wasa Fatima ta ce, "abin da kike tunani" dariya suka kwashe da ita a tare Fatima ta ce, "wannan cikin kamar ya dawo maki da halin ki na baya" dariya fatu ta saki ta ce, "har kin sa na tuna san da muke zuwa gonar mai gari.! dariya suka kuma saki suna tuno yarintar su mai cike da drama  kallon juna suka yi tare da cewa, "Allah mun gode maka bamu ta6a tunanin ganin mu a haka ba, rayuwa kenan" rungume juna sukayi tare da  hade bakin su suka furta, "Allah ya bar mana zumincin mu har ya'ya da jikoki ameen Fatsima" harara ta aika ma fatu ta ce, "ke mijina ya hana fadin wannan suna," dariya sukayi tare da cewa, "sannu mai miji" a haka suka isa wajan kamun  kasancewar sune manya-manyan qawayan amarya hada-hada kawai suke biki yayi biki su Zara da Nana ma sai da suka zo ansha biki sosai sai kusan yamma likis suka dawo, gidan mami suka wuce direct.

        Da sallama suka shigo angel dake zaune da friends nata ta qaraso ta rungume fatuha ta ce, "Mom a I miss you"  
          "miss you more dear, kin manta da mamanki tunda biki ya kama ko? to ai gashi nan ni na biyo ki bana iya hakuri kimin nisa" fatuha ta fada tana shafa kanta smile tayi  ta ce, "Nima haka Mom" ja mata hanci fatu tayi sannan ta koma cikin friends din ta.

          Shirye-shirye na zuwa dinner suke, cikin material lace green and black yan'matan amarya, amarya kuma ta shirya cikin black lace mai ratsin white, sosai sun fito sunyi kyau musanman da suka sha make up, cikin  motaci na gani na fada aka zo kwasar yan matan amarya, fatuha ko motar sadiq ta shige, lallausan murmushi sadiq ya sakar ma fatu ya kama  hannu ta yana murzawa a hankali cikin salo yana sakin murmushi yasha kyau har ya gaji yana sanye cikin shada milk tasha aikin hannu,  kamshin turaransa na fizgar fatu ya  ce, "My wife kinyi kyau masha Allah" smile fatuha tayi ta ce, "na gode hubi, kai ma kayi kyau har na ji kishi kar mu je yan mata su dinga kalle min kai" fatu ta fada tana d'an 6ata fuska yar dariya sadiq ya saki yace, "ni ba mai kallo na mijin mace daya daga fatu na rufe" murmushi ta sakar masa mai cike da sakonni sannan ya ja mota hannu sa daya na maqale dana fatuha.

              Hall ya cika maqil anata gudanar da biki, inda abun ya zama abin sha'awa da birgewa amarya da Ango sunyi kyau har sun gaji, kasancewar bikin masu hannu da shuni ne  manya-manyan ya'ya masu hali da masu fada aji sun halara, fatu da sadiq kam sun zama abin kallo dan sadiq baya iya boye irin son da yake ma fatuha koma a inane nuna mata so yake, sai nan yake da ita haka aka gudanar biki, ayi ciye-ciye da lashe-lashe  naira tayi kuka dan anyi barinta sai dai mu ce Allah ya bada zaman lafiya.

          Da misalin karfe 10:00pm taro ya watse sadiq ya wuce da fatuha gida, maqale qafa tayi ita baza ta koma gida ba ya maida ta gidan mami, cikin yan'mata amarya fir sadiq yaki saurarata haka ta cika taf kamar ta fashe, horn yayi mai gadi ya wangale geta ya kunna hancin motarsa cikin gida yayi parking a parking space, kashe motar yayi ya bude murfin motar fatuha ko zaune tayi tana qoqarin fara raira kuka Allah ya gani gidan Mami ta so kwana ba gida ba, zagayowa sadiq yayi ya 6ale mata murfin motar ganin fatu bata da niyar fitowa sadiq ya dauke ta kamar baby ya shiga da ita gida sai rigima take zuba masa har da kuka dakyar ya lallashi fatu ta saurara masu sukayi baccin dare.

   Washe gari

   Yau d'ibin mutane suka sheda daurin auran Dr yakub da Hanan    akan sadaki naira dubu dari, zuciyar Dr yakub fes sai washe baki yake da ka gansa kasan yana cikin farin ciki, ana kamala daura auran Dr yakub yaji alat a account dinsa kallon sadiq yayi tare da sakar masa murmushi sannan ya masa godiya,  bayan  kamala biki ango ya dauki amaryar sa sai airport inda Hanan ke ta zuba kuka.

            Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dad'i inda sadiq ke bama fatuha kulawa sosai, yanzu haka sun fara exam, alhamdulillah exam din ta zo mata da sauki, cikin ta ya dan fito.

     Murna suke sosai na ganin cewa yau sun gama paper, sosai fatuha ke jin dad'i a gaskiya bata da abinda zata ce ma mai kyau ya gama mata komai a rayuwa, ko da ta fito sadiq ne ya zo daukar ta, kasancewar Saturday ne ya zo weekend gida cike da farin ciki ta qarasa gaban motar ya 6ale mata murfin mota ta shiga, su Zara ko d'aga mata hannu su kayi tare da yimata alqawarin sai sun zo ranar suna.
Chapter 65 · 0% Book details