← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 67

Sashe 6

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

        Turo kofar da akayi ne yasa Sadiq  tsagaita kukan da yake, Abba ne tsaye bakin kofa cikin sasarfa sadiq ya qarasa wajan Abba,  ya qara sakin wani sabon kukan Abbane ya rugume shi alamar lallashi ya  ce,  "shhh!! Sorry son be are strong man sai ka ce ba soja ba, insha Allah she will be fine" Abba ya  juyo kan  jawad  ya ce,  "Jawad ka kaishi gida ya samu hutu kaji"
   "Daddy..!
  "Shhhh..! ya isa kaji jawad  ka kai shi gida kawai" Haka ko akayi.
       jawad ne ke driving nasu cikin mota ba wanda yayi ma wani magana, sadiq idanun shi a lumshe har suka iso gida bala mai gadi ne ya bud'e masu  gate tare da  jajanta masu, parking space yayi parking suka fito a tare.
     bedroom d'in sadiq suka shiga ya kwanta saman bed tare da lumshe idanun sa, zuciyarsa na wani irin suya musanman idan ya tuna da halin da abin kaunarsa ke ciki, Jawad ne ya katse masa tunani ta hanyar shafa sumar kansa, ahankali ya ware sexy eye's ball's d'insa ya  d'aura su  kan jawad riqe yake da glass cup da fresh milk a ciki ya ce,  "Sadiq please ka daure ka ci wani abu nasan tun breakfast d'in safe baka qara sa komai a cikin ka ba, please ka gama ka sha magani headachen nasan yana damun ka" numfashi ya ja ya cigaba  da cewa, "insha Allah wife naka zata samu sauki kaji baby" kamar ba zai sha fresh milk d'in ba, amma saboda bai ga wasa a idanu yayan nashi ba ya amsa, Sha biyu zuwa uku yayi ya aje saman stool ya qara lumshe ido maganin headache jawad ya 6alo tare da ruwa ya bashi ya sha, sannan ya lullu6esa da blanket ya fita.

      Bacci ne mai nauyi ya d'aukesa bashi ya tashi ba sai yamma liqis wanka yayi yasa Jean's n shirt bleu mai dogan hannu sannan yayi sallah la'asar, ba qaramin kyau yayi ba sai dai fuskan nan fayau saboda kukan da yaci sannan cike take da alamar damuwa, car key nashi da ke saman stool ya d'auka ya fita.
         kaitsaye asibiti ya wuce yana parking motarsa a harabar asibitin aka fara kiraye-kirayan sallah magrib Masallaci ya shiga yayi sallah zai futo kenan suka had'u da Abban kausar, hakuri yake ta bashi ankan cewa bai san kausar bafa fad'a masa larurata ba sadiq  ya  ce, "ba komai Abba"
  "Toh shikenan Allah ya bata lafiya" 
"Ameen.!!
         d'akin da a kwantar da kausar ya shiga Mom na saman daduma tana lazumi, gaisheta yayi ta amsa a takaice sosai taji dad'in ganin sauyawar sadiq  ba kamar d'azu ba, Kausar ya kalla wanda ke kwance saman gado kamar gawa oxygen ne manne a hancin ta sai jini da ake qara mata, idanuwansa ne suka ciciko da kwalla tabbas yasan ya rasa kausar ya rasa mata tagari,  cikin  zuciyarsa  yake  sanbatu  da  cewa,  why mai yasa zaki mana haka kausar..! hawayan da ke neman zubo masa ya had'iye Mom ce ta katse masa tunani da cewa, "Baby ni zan wuce ka kulla da ita anjima matar jawad shukura zata kawo maku dinner, Son please ka rage damuwa wannan" Mom  ta  fad'a tare da shafa gefen fuskansa kamar jira ya ke hawaye suka fara mai zarya "shhh..! ya isa mana idan kana kuka ita kuma mai zatayi sokake ka tada ma kausar hankaline baby? Girgiza kai yayi tare da d'aura hannusa kan na Mom ya ce, "toh na daina"
   "ko Kai fa idan kasan kuka zaka cigaba dayi to sai mu koma gida Bilkisu ta kwana da ita"
   "Uhm Mom bazan sake kuka ba" wasu sabin hawaye ne suka zuba masa ya  ce, "Mom na rasa yarda zanyi control kai nane Mom nasan sarai na rasa my wife saboda wannan cikin" ya ja numfashi ya  cigaba da  cewa, "Mom kausar bata iya rainun cikin nan, Mom ki duba ki gani ita kanta duk month tana buqatar jini bale kuma yanzu data ke tare da ciki" ya ida zancen hawaye na zubu masa Mom ce ta share kwallan idanu ta ta  ce, "son ya isa haka kayi mata addu'a insha Allah lafiya lau zata raini cikin ta har ta haihu kaji" kai ya gyad'a mata tayi  peck nasa agoshi sannan ta masa sai da safe.

     Gashin kanta ya shafa  ahankali tare da kai mata peck a goshi ya  ce, "Allah ya baki lafiya my wife" sannan ya d'aura kansa saman gadon, a hankali take bud'e eye's balls din ta tasauke su kan sadiq da idanun sa ke lumshe kamar maiyin bacci,  a hankali ta miqa hannu ta saman sumar sa tanajin wani son mijin na ta na qara narke mata a zuciya, a hankali ya dago sexy eye's  ball's din sa ya sauke a kan wife din sa da  suka  canza  launi  saboda  kuka,  murmushi ta saki tana qoqarin tashi zaune ya  dakatar  da  ita  da  cewa, "no ki koma ki kwanta kiji my wife" ya ida zancen yana shafa cheeks nata ya  ce,  "My wife mai yasa kika 6oye min sick naki why? Idanun tane suka ciko da kwalla ta bud'e baki zatayi magana, sadiq  ya  ce, "Shhhh.. ya had'a bakin su waje d'aya yana mata salon sa mai kashe mata jiki..

                            **
           Rayuwa haka ta cigaba da tafiya sosai kausar ke samun kulawa wajan sadiq, inda suka bud'e babina soyayya, soyayya suke sosai kamar su cinye juna su inda duk month sadiq sai ya kaita asibiti an qara mata jini.

   Misalin qarfe 3:00am na dare sadiq kwance kausar na manne aqirjinsa ahankali yasa hannu yana cire mata hula da ke kanta, wadda bata bari ya cire mata, wasu siraran hawaye ne suka zubo masa saboda kusan rabin gashin ta ya zube saboda wannan ciwon, kuka ya sha sosai cikin daran sannan ya tashi yayi sallah ya nemamata samun sauqi wajan Allah, tabbas yasan ya rasa kausar ya rasa wani 6ari na rayuwarsa da irin wannan tunanin bacci ya d'auke shi.

   Akwana atashi ba wuya wajan Allah yau kausar cikin ta ya kai 9month, sadiq ne akwance yana bacci ya fara jin,  wash.! sadiq.! zunbur ya tashi hankali tashe kai tsaye asibiti suka wuce nurses suka kawo masu taimakon gagawa, gabaki d'aya sadiq ya rud'e har da yar kwallan sa, waya ya curo ya kira Mom ya fad'a mata cikin muryar kuka.
     Zirga2 sadiq ke yi ya kasa zaune ya kasa tsaye, Majid ne ya dafa shi  ya  ce, "cool down sadiq" tare da rugume sa alamar lallashi,  Doctor's ne ke kan kausar sosai suke aikin su dan suga ta haihu da kanta amma abin ya gagara.!!

          Doctor yakub ne ya fitu yana goge zufar face nashi, da sauri sadiq ya k'arasa wajan su da Mom da majid a  tare suka jefama doctor yakub tanbaya  "Ya kausar.?
   "da sauki muna kan bakin qoqarin mu, ga wannan paper captain sadiq kasa hannu kausar ta kasa haihuwa da kanta" jikin shi narawa ya amshi paper yasa hannu aka shiga tiyata tun dare ake abu daya sai da safe suka fito.
     daga Mom har sadiq ba wanda ya rintsa addu'a kawai suke, bayan ta haihu doctor ya sheda masu ta haifi baby girl murna wajan su Mom ba'a magana da sadiq.

      Kwance take a d'aki ita kad'ai tasan rad'ad'in da take ji wasu hawaye ne masu zafi  suka zubu mata tasa bayan hannu ta ta goge, gefen da baby take ta kalla jin an bud'e kofar ya sata d'ago eye's ball d'in ta, wani lallausan murmushi ta saki tana qoqarin tashi,  Sadiq ya qaraso ya  ce, "my wife" tare da kai mata peck a goshi yana qoqarin maida hawayansa kausar  ta ce, "Habibina.! cikin sanyin murya  Baby  sadiq ya d'auka yana  murmushi  ya  ce, "Masha Allah baby mai kyau da ita kamar  ke"
   "habibina..!
"Na'am"
  "ga amanar baby mun na baka please ka kula da ita"
  "shhh insha Allah tare zamu raini baby mu" yana qoqari boye hawayan da ke maqale a idanusa,  hannu ta kai  ta  shafa sajan fuskarsa mai laushi ta ce, "Wani suna zamu sama baby mu? Lallausan murmushi yayi ya ce, "Hauwa'u suna Mom, za'a mata laqabin ta Jidda" Fad'ad'a murmushinta tayi ta ce, "Jidda..! ta shafa cheeks d'in baby hannu ta ya riqe ya sunbata, tarine ya subuce mata jinine ya fara bi mata ta hanci da baki.
      Da sauri sadiq ya mik'e zai kira doctor, hannu sa ta riqe tana girgiza masa  kai  tana motsa baki can yaji jikinta yayi sanyi cikin  wata  irin  murya  rikice  ya  ce,  "Noooo..! Sulalewa k'asa yayi sumame.

Writing by
Salma mas'ud nadabo

Edit by
Blood sister deeja

📘 REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM

13_14

Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un duk wani mai rai mamacine yau dai kausar ta rigamu zuwa gidan gaskiya, shi kuma sadiq aka wuce da shi emergency dan bai san inda kansa ya ke ba, dangi sunyi kuka sosai na rashin kausar saboda kausar mutuniyar kirkice.
Chapter 6 · 0% Book details