← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 67

Sashe 46

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Direct part din Sadiq ta wuce a hankali ta murda handle din kofar tare da shigowa cikin sallama zaune sadiq yake saman two sitar da laptop gabansa kallo d'aya zaka masa kasan baya  cikin  dad'in rai zaka  gane  akwai  abin da ke  damunsa fuskar nan  nasa babu annuri ya  koma  captain sadiq  na  da  sak bakin  fatu  na  rawa  ta  ce, "Uncle..!  dogo kai yayi ya kalli fatuha tare da lumshe ido ya kauda kai ya ce, "Just leave me alone" sadiq ya fada a tsiwace tare da tatara takadunsa dake gabansa da laptop dinsa ya shige bedroom tare da buga kofar da karfi, har  saida  fatu  ta  razana  da  yarda  ya  buga  kofar kafarta  kasa  daukar  gangar jikinta  yayi  saboda  tashin  hankali  na sauyawar  sadiq  lokaci  daya kuka fatuha ta saki tare da fita daga part din da gudu jin ta fita yasa sadiq jingina da kofar bedroom ya lumshe ido har  cikin  ransa  yake jin  sautin  kukanta, amma  kishi  ya  hana sa  saurara mata.

      Da gudu ta wuce Mom a parlour ta shige daki saman bed ta fada tare da sakin kuka maicinrai har  da  shesheqa, kuka taci ta gaji.
         Mom dake parlour bin fatuha tayi da kallo tana mamakin mai ya hada su da  sadiq  haka, koma dai menene ai sun saba zasu shirya ne amma abin mamaki basa kai haka, kauda zancan Mom tayi tare da cigaba da kallon ta.
          Duk yinin yau babu wanda yaci abinci cikin su, ban da kuka ba abinda fatu take, shi ko sadiq sai bak'in rai dayake fama da shi.

    Iskace mai sanyi da ke ta kad'awa da alama ruwa za'ayi saboda damuna data fara shigowa, qara cida ce kawai ke tashi bakin window sadiq ya tsaya a hankali ruwa ke saukowa kallon ruwan yake yanda yake saukowa da karfi, a wannan karan lumshe ido yayi tare da ware su, ya koma saman bed ya kwanta jikinsa  ba  dadi.
       bangaran fatuha tunda aka fara ruwa ta lullu6e cikin blanket jikinta  yayi  rau  da  fever.

      Gabaki daya yini yau ba wanda yayi ma wani magana, cikin fatuha da sadiq, horan d'aki sukayi wa kansu ba tare da sun nemi abin sama bakin sallatin su ba, ba wai  kuma  basu  jin  yunwar  bane  a'a  abinci  ne  ba  zai  samu  mahali  ba, har bacci ya kwashe su.

           Washe  gari
      Shiryawa yake cikin manyan kayansa kasancewar yau zasu je family meeting, fatuha ce ta fado masa a rai kawar da tunanin yayi dan har yanzu bai huce ba ko yana hucewa sai ya dawo daga meeting.
                cikin Isa yake saukowa daga upstairs, lokacin har su Mom sun shirya suna parlour zaune suna jiran fitowar sadiq da fatuha ganin sadiq ya sako yasa Mom cewa, "angel kira Aunty mu wuce.!  ko da angel ta shiga d'akin kwance ta samu fatuha qudindine cikin blanket, fitowa tayi da sauri daga bedroom din ta ce, "Grandma Aunty bacci take"
      "toh fa! amma ai fatuha bata kai haka tana bacci" shiga d'akin Mom tayi tare da qarasawa wajan bed din fatuha ta ce a hankali, a hankali fatuha ware idanuwan ta da suka yi nauyi saboda tsabar kuka, kallonta Mom tayi ta ce "Mike damun kin fatuha? dafe kai tayi ta  ce,  "Mom kai nane ke ciwo"
    "eyya sorry dama meeting zamu tunda baki jin dad'i ki zauna kawai a gida" to kawai tace tare da shigewa blanket, sannan Mom ta fita ko da ta fita sadiq ta aika ma harara tare da ayana ma ranta idan sun dawo zatayima  tufkar hanci.

       Katafarin parlour su da aka ware danyi meeting suke zaune, tunda sadiq ya shigo gabansa ke yankewa yana fad'uwa yarasa dalilin hakan addu'a da ke  bakinsa ya furta dan samun nutsuwa, duk  kuma  ya damu  da  yanayin  daya  bar  fatu yafi  tunanin  harda  hakan  ya  hanasa  nutsuwa, majeed ne ya shigo tare da zama gefen sadiq ya  miqa masa hannu suka gaisa dakyar sadiq ke danne zuciyarsa kan majeed  da bata hakuri.
        Alhaji Babba ne ya shigo sanye da babba riga tasha aiki sai sheqi kayan suke, da sallama ya shigo tare da zama a kujerarsa ta musanman wato kakan su sadiq, Ammi na gefansa na dama sauran jikoki da iyaye na gefe da yan uwa.
            Taro ya fara budewa da addu'a sannan ya fara jawabin cikin nutsuwa ya  ce, " ina  maku  barka  da  zuwa Allah yasa yarda  ku  ka zo  taron  nan  lafiya  mu  koma  gida lafiya, kuma  na  ji  dadin  yarda  kuke  zuwa  wannan taro na  qara dankon  zuminci kamar yarda kuka sani ko  wani  lokaci  muna  samun  alherai  da  yawa  bangaran  kasuwancin mu  ina  ma albishir da abubuwa da yawa na farin cikin a wannan shekara mun samu kimanin billioths of naire cikin ribar kasuwancin mu, mun talafawa gidan marayu da asibitoci  mun biyawa mutun 30 kujerun maka..! kabara wajan ya dauka tare da hamdallah.
      Gyaran murya Alhaji yayi  ya ce,  "Kuma ga muhimiyar sanawar Majeed ya  samu matar da zai aura..! sadiq dake zaune saman kujera gabansa ya qara yankewa ya fadi ras-ras muryar Alhaji babba ce ta dawo masa dodan kunne, "Alhamdulillah  mun  nema an bamu saboda  karamci, ba kowa bace sai yar gidan ibrahim wanda yake ruqo fatuha..! har gidan iyayan ta muje munyi bincike ashe ma akwai sanaya a tsakanin mu kuma sun aminci sun bada haka ya  mana  dadi matuqa..!  wani irin gumi ne ya karyo ma sadiq maitsananin zafi take nan ya fara ji wutarsa na d'aukewa jikinsa  rawa  ya  d'auka  jin  kalaman  Alhaji  yake  tamkar  saukar  aradu, wani  irin  amo  kalaman  suke  masa  cikin brain, ba sadiq ba hata Mom sai da ta girgiza da wannan furucin, ita  dake qoqarin  furta  abinda  ke  ranta sai  gashi an masu shigar  sauri  da  karfi  kirjinta  ke  bugawa  tana  tunanin  halin  da  d'an  autanta  dilo  zai  shiga, wata kalmar ya qara jefowa a karo na biyu "sadiq kuma mun yanke shawarar bashi kanwarsa Basma amma da sharadi idan har ya kawo wadda yake so nan da sati daya kamin asa biki to za'a basa dama ya auri wadda yake so, Basma ma kuma ta hakura wannan shine hukuncin dana yanke.! sannan ya kalli baban Basma ya  ce, "Alhaji khabiru cika mana taro da addu'a..!

      Gabaki d'aya parlour juyawa sadiq yake dakyar ya samu ya miqe, jiri  na  neman  kadasa majeed ban da murna  ba  abin da yake  finally  yanzu  zai  samu  fatu  shawo  kanta  kawai  ya  rage masa, ko ta kan sadiq bai bi ba haka Basma baki har kunne tana  ganin shawo  kan  sadiq  ya  so ta  abu ne  mai  sauki  kamar  yarda  Umma ta  sheda  mata.
           sadiq ne kadai da Mom basu farin ciki, sai Hanan da tashin  hankali  ya hanata  motsi  sanin  matsayin da  fatu  ta  aje  sadiq.
               yana fitowa daga parlour parking space ya nufa cikin sauri ya bale murfin mota ya shiga, da gudu ya fisgi motar ya harba kan titi gudu yake tsulawa kamar zai tashi sama, ko  ganin  gabansa ba  yayi  saboda  tsanin  tashin  hankali  mara  musaltuwa,  fatu  da  majeed  abun  kamar  a  mafarki, yana isowa gida ya danna horn da  karfi  dan  sam  bai  san  mai  yake  ba, bala mai gadi na bude masa geta ya ce "Subhanilillah..! Saboda yadda sadiq ya shigo da motar da  mugun  gudu  kamar  zai  tashi  da  bala  mai  gadi.
      ko daidaita parking ya kasa ya bale murfin motar ya fito, cikin sauri ya wuce part dinsa yana shiga ya zame bakin kofa tare da dafe kansa, jijiyar  kansa  duk  ta  taso  saboda  tsabar  tashin  hankali maganar Alhaji babba na dawo masa, cikin  dodan  kunne miqewa yayi ya shige bedroom saboda har yanzu bai dai na ganin jiri ba, gani  yake kamar  kunnasa  bai  ji  dai-dai ba  wani irin kuka sadiq ya saki mai tsuma zuciyar mai saurare kneeldown yayi a wurin bakinsa na  rawa  yana  furta, no..! No..! I cant believe abinda  kunne  na  ya  ji  noo..! fatali da kayan d'akin sadiq  yake kamar sabon kamu, duk  abinda  ya  dauka  ya  wurga sai  ya watse  ya  dawo  kasa sai da yayima d'akin fata-fata ya shiga toilet da kayan jikinsa sakar ma kansa shower yayi, maganganun Alhaji babba har yanzu  ke masa yawo a brain wata zuciyar ta ce "Wato jiya fatuha tabama majeed izinin turawa gidan su? Dama  fatu  ba  so  na  take  ba? Jikin  sadiq  na  rawa ya  furta  Kalaman bakinsa hadeye  kukan da yake yayi ba shiri ya fito sharkaf ya zauna kasan carpet bai damu da kayan dake jikinsa ba ya  takure  waje  daya.

      Bangaran fatuhu ko tunda su Mom suka fita gabanta ke faduwa, ta rasa dalilin haka ta rasa sukunin ta jin an bude kofar d'akin ya sata waigowa Mom ce tsaye bakin kofa murmushi fatuha ta saki wanda iya karshi la66anta ta  ce, "Mom har kun dawo da wuri haka? eh tace tana qoqarin danne damuwarta, ta  qarasa shigowa zama tayi kusa da fatuha cikin sanyi murya ta ce "Fatuha gobe da safe ki shirya zaki je wudil Baffa nasan ganin ki?" sannan ta tashi ta fita kallo fatuha tabi Mom da shi take nan jikinta ya haubari da tsoro-tsoro ko dai uncle ya kai qarata kauda zancan tayi tasan ma ba zanyi haka ba, amma zuciyarta na cike da tanbayoyi, ganin bata da amsa ta hakura.

      Ola sadiq ya kira a waya bugu d'aya zuwa biyu ya dauka, "ina san ganin ka" sadiq ya fada a taqaice.
           ko da ola ya zo ganin watsin da akayima dakin sadiq ya tsorata kallon sadiq yayi da magana a bakinsa, ganin fuskar sadiq ba annuri yaja baki ya tsuke, nuni ya masa daya gyara d'akin shi kuma ya shingida saman sofa, yana  jin  wani  quna  da  suya  da  zuciyarsa  ke  masa hawaye daya na bin daya saman fuskarsa kamar ba soja ba,

      Gabaki d'aya gidan Alhaji Ibrahim ba wanda ya rintsa, daga angel sai Abba ne kawai suka samu bacci,
        bangaran sadiq ban da kukan zuci ba abinda yake, fatuha kuwa tunanin me yasa Baffa ke neman take?  ko dai inna ce ta rasu? ba'a son fada mata girgiza kai kawai  tayi.
Chapter 46 · 0% Book details