← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 67

Sashe 19

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Bayan angama breakfast har bakin mota sadiq ya raka jidda, fatuha na riqe da lunch box din jidda sai da ta tafi sannan suka juyo zasu koma gida, da gudu fatuha ta wuce sadiq sai da taje bakin kofa sannan ta juyo ta masa gwalo tare da kwaikwayar yarda yake tafiya ta fashe da dariya ta shige da gudu, cije lips din shi yayi tare da tura hannu shi cikin sumar sa ya  ce, "oh Allah ka bani ikon cima yarinyar nan sannan shima ya qarasa parlour ko da ya shigo ba kowa sai baba jummai da ke kwashe kayan breakfast, gaishe ta yayi ta amsa washe da baki, part din shi ya wuce ya murda handle din kofar ya ji rufe mamaki ne ya rufe shi fatuha da ke jingine jikin kofar ta ce, "mai kyau kwarankwatsi ban bud'e ma kofar nan sai na gama aiki na dan nasan halin ka kai mugune wallahi, ka na shigowa zaka bigeni" sadiq da ke wajan kofa yayi sororo yana mamakin raini da fatuha ta masa cige  lips yayi tare da barin gurin saboda ya san idan ya cigaba da tsayawa har kashe ta sai yayi dan bacin rai, fatuha jin ya tafi yasa ta cigaba da aikin ta tanayi tana yan'wake-wakyan ta har ta gama tuni daki yayi kyau sosai sannan tabi part din da turaran wuta tuni part din ya dau kamshi da kyau sannan ta qara gudun AC dakin ita kanta sai da taji kamar tayi bacci dan Kyan da part din ya mata.

     A hankali taje bakin kofa ta murda handle ta leqa taga ba kowa, sannan ta fito da sauri ta wuce sadiq da ke kwance  saman three star idanuwan shi lumshe kamar me bacci yana kallon fatuha ta ruga daki da gudu ta kule, tsoki ya ja tare da tashi duk kiyi ki gaba zan kamaki ne tare da wucewa part nashi dan bacci yake ji ko da ya shiga part din shi da kanshi sai da yayaba kyan da part din yayi, ga kamshi sai tashi yake da sanyi irin yadda yake so lumshe ido yayi ya ja jiki ya hau bed ya kwanta.

       Tana shiga bedroom kayan jikin ta ta rage ta shiga toilet,  tayi wanka sosai dan yanzu ba qaramin jin dadi take ba idan tana wanka  amma da a kauye sai anyi da gaske, yanzu ko fatuha ansan muhinmancin wanka, daure da towel ta fito ta goge jikin ta tare da shafe jikinta da lotion mai kamshi ta feshe jikin ta da turare yar hoda da murza duk ba wata kwalliya tayi ba masha Allah fatuha tayi kyau, uniform din ta ta zura sannan tataro gashin ta wanda ya cure gudaya tana qoqari kamashi amma ta kasa saboda yawan shi da tsaho 6ata fuska tayi tace, "Allah sarki inna da kina kusa da kin gyara min" magana da su kayi da Mom ce ta fado mata daure kan tayi da sauri ta haura upstairs dakin Mom ta shiga ba ta nan neman ta ta shiga yi,  kitchen ta shiga tare da tanbayar su rabi'a ina Mom, ta ce mata tana part din Abba ,toh tace tare da komawa parlour ta samu wuri ta zauna tana kallkn film din India tana washe hakora.

       Mom ce zaune da Abba a bedroom din shi tana zaune saman kujera a hankali ya qaraso ya rungume ta ta baya, murmushi tayi ya  ce, "madam kullun qara kyau kike baki tsufa gashi har da jikoki," dariya tayi ta ce "Ya za'ayi na tsufa bayan mijin nawa kullun yaro yake komawa"  hancinta ya ja cikin tsokana ya ce, "uhm next week zan koma uk kan magana nan gaskiya this time around ban tafiya ni kad'ai, tare nake so mu tafi" murmushi Mom tayi ta ce "Kamar kasan abinda ke raina kenan" smile yayi  ya  ce, "uhm kuma sai gashi na rigaki fada ba," ya ida zancan tare da yi mata kiss a kumatu ta  ce, "ni ko Abban sadiq kunyi waya da jawad kuwa?  dan murmusawa yayi ya ce, "Eh jiya munyi waya ya ce min yanzu shukura tsohhon ciki gare ta, so yake in ta haihu sai su zo ganin gida" murmushi Mom tayi ta  ce, "Allah ya sauke ta lafiya kamar  kasan nayi missing nashi wallahi ya kamata jawad ya dawo Nigeria da aiki, amma nasan ba lallai bane ya so ba saboda na lura yafi sin London sosai,"
         "uhm ke dai ki ce d'anki kike san gani, yauwa gobe ki shirya ina so muje wajan Ammi muyi masu sallama kafun mu tafi" to tace masa tare da tashi zata fita jawo ta yayi jikinsa ya  ce, "please idan kinje karfa ki dad'e ki bar tsohon mijin ki da jira kinji" murmushi tayi tare  da kashe masa ido.. lol ah tsofafi na konewa hehe. 

  ( shawara ga mata please mata ya kamata musani tsufa baya hana soyayya karki ce dan kina da manyan ya'ya ki ce ke kin girma ita soyayya bata girma, kuma gyara da tatalin miji shi ke qara dankwan soyayya, so da yawa wasu matan suke jawa maza jansu bin mata saboda kina ganin kin girma komai sai ki daina, idan mijin ki mai so ne daga nan zai fara bin ya'ya cikinsa a waje suna masa yana jin dadi please mata mu kiyaye) .

      Fatuha da ke zaune saman kujera tana kallo, Mom ce ta sauko daga upstairs, cikin ladabi fatuha ta gaishe ta tare da tuna mata maganar gyaran kan, toh shikenan Mom  ta  ce, "je ki shirya mu tafi,"
     "Mom bada wannan kayan zani ba?
"eh kisa kayan gida" toh tace mata ta shige bedroom, Mom ko part din Abba ta koma ta tanbaye shi zata fita ya bata izini, sannan ta dawo dakin ta ta shirya cikin atamfa  black mai ratsin red n yellow bubuce mai  kyau tuni Mom ta fito sosai bedroom d'in fatuha ta wuce tsaye, ta same ta ta rasa kayan da zata sa washe da baki momt ta qaraso ta  ce, "fatuha har yanzu baki shirya ba? shagwabe fuska tayi ta ce, "Wallahi Mom na rasa kayan da zansa ne, zabamin dan Allah" to tace mata wata hadadiyar gown Mom ta janyo brown colour mai ratsin milk da Stone's a jikin rigar mai dogwan hannu ce  sai veil milk, masha Allah fatuha ba qaramin kyau kayan suka mata ba cib suka mata qirjin ko kamar tasa bara saboda yadda kayan suka mata rolling veil din tayi da gashin ta data daure sai abin ya bada kala ta fito fes, takalmi tasa black mai kyau  suka fito,  direct parking space suka wuce Mom ta jasu suka fita sai fatima salon da ke gandu. 

   Basu wani dad'e ba a Solon din ba sosai aka gyara gashin fatuha dan ko  mai ba'a sa  mata  ba saboda laushin gashin ta dan idan aka sa masa mai, zai iya konewa gyara shi kawai akayi masha Allah ita kanta fatuha sai da ta tsorata da gashin ta saboda har qugunta ya kai, da yaji gyara amma sai ya rage yawa su kansu yan wajan yaba gashin su kayi  ana gamawa suka dawo gida, a parking space moym tayi parking suka fito har zasu shiga gida sai ga driven jidda ya kunno kai yayi parking da gudu jidda ta qaraso tare da rungume fatuha ta ce "Anuty kinyi kyau,waya maki kwalliya?" dariya fatuha tayi dan ita ba wanda ya mata kwalliya d'aukar jidda tayi suka qaraso parlour sadiq na zaune saman two star yana shan coffee gefensa kuma baba jummai ce suna d'an taba hira da shi da alama tafiya zatayi.

      Cikin sallama suka qaraso, sadiq ya amsa sallamar, fatuha  ke dauke da jidda, jidda ta zame daga jikin ta ta ruga wajan sadiq ta rungume sa wasa ya shiga yi mata tana dariya  qarasowa Mom tayi ta zauna saman three star ta ce "Oya a wuce aje a cire uniform, kin bar Anuty na jiran ki " sadiq ne ya dago ya kalli fatuha ya wani tabe baki tare wurga mata harara ya miqa mata jidda, baba jummai ko sai yaba kyan da fatuha tayi take tare da yima su Mom sai da safe fatuha kuma ta ja jidda zuwa bedroom.

Written by
       Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail. com

*fan's ana mugun tare dinnan sosai*🤝🏽

                      39_40

Bayan ta gama ma jidda wanka ta shafe ta da mai tare da saka mata kaya jeans n t-shirt riga pink wando bleu sannan ta gyara mata gashin ta, tuni jidda ta fito tayi kyau masha Allah, toilet ta koma ta d'auro alwala kasancewa 4:00pm tayi ita da jidda suka gabatar da sallah suna idarwa fatuha ta cire veil din kanta tana kallon gashin ta a mirror tana washe baki, jidda ce ta ce,  "Anuty gashin kine haka? jiyowa fatuha tayi washe da baki ta ce,  "kema kin gani ko? Ai Allah daga yau na gama yawo da d'ankwalli wallahi wannan gashi kamar ba nawa ba"
             "gaskiya Anuty kina da gashi dama ki qaramin.! Jidda ta ida zancan tare da washe hakora murmushi Fatuha tayi tare da maida dankwallin ta jawo hijabinta dana jidda suka  wuce wajan malam.

           Sosai suke karatun, damma karutun ya zo ma fatuha da sauki dan duk wani qari da malam ya mata jiya ta juye masa shi, shi kansa yana yabawa da qoqarinta,  qara musu yayi, dan haka basu suka shiga gida ba sai 6:00pm
Chapter 19 · 0% Book details