Sashe 13
Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
****
Kwanci tashi asarar mai rai yau satin baba jummai d'aya a wudil inda take ta had'a kayanta dana fatuha, Fatuha sai kuka take har da majina dan ita a ganinta baba jummai bata mata adalci ba ita tace mata tana son birni da zata kwashe ta su tafi, toh Wallahi sai nayi rashin mutunci idan sunje kenan, cewar fatu a zuciyarta baba jummai ce ta juyo ta ce, "haba fatuha sai ka ce za'a cinye ki sai kuka kike haba fatuha kinsan muna tare kuma zan kula da ke kamar yarda inna zata kula da ke, dan Allah kiyi hakuri kiyi shuru kinji" Inna da ke gefe duk da tana jin wani irin amma tasan baba jummai ba zata tayi abinda zai cutar da fatuha ba amma ko yaya tana jin zafin rabuwa da fatuha saboda fatuha yarinya ce mai shiga rai, ta wani fanni kuma gara fatun ta tafi ko muta nan kauyan sun huta da jarabar fatuha, a hankali inna ke lallashin fatuha har tayi shuru haka shima Baffa da ke gefe haka baba jummai ta gama had'a kayan fatuha cikin yar leda gari yayi zafi ta miqa mata ta rungume.
Baffa kuma yaje taro masu mashin, Sallama fatsima tayi ta shigo falon kallo d'aya zaka mata kasan itama ta ci kuka har ta gaji, wani saban kuka suka dasa ita da fatsima dakyar aka lallashe su sannan baffa ya shigo ya sheda masu gamai mashi din.
Suna kallon su har suka 6ace maganin su Baffa ya goge yar kwallar shi, dan shi kad'ai yasan yarda yake ji, suna isa tasha suka samu motar Kano basu wani dad'e ba motar ta tashi.
*******
Idanuwansa lumshe kamar wanda ke bacci, zaune yake saman resting chair yayi crossing leg's nashi ta6a shin da akayi ne ya sasa ware sexy eye's ball's d'in sa ba kowa bane sai majid murmushi yayi ya ce "Yaushe ka zo ban sani ba?
"yanzu na shigo Mom ta ce min kana nan" sannan ya zauna daya daga cikin chairs din sadiq ya ce, "OK ya aiki?
"Alhamdulillah soma nake na dawo nan da aiki, kai Allah ya taimake ka har yau basu ma transfer ba"
"Aiko dai ai bana fatan hakan wallahi" murmushi sukayi su duka suka cigaba da magana a matsayin su na abokai kuma yan'uwa...
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
27_28
Misalin karfe 5:00pm motar su fatuha ta tsaya a tasha lokacin har bacci ya d'auke ta tana kafadar baba jummai rungume da jakarta gari yayi zafi, ahankali baba jummai ta shiga tashin ta, aiko nan tatashi tana wani wiqi-wiqi da idanu da qarewa tashar kallo, mutanene birjik haka suka zuro kafafun su suka fito daga motar, Baba jummai ce ta zaro wayar ta cikin zani y'ar baby nokia ce ta fara kiran Mom ta sheda mata isowarsu bugu d'aya zuwa biyu Mom ta d'auka washe da baki baba jummai ta ce, "hello hajiya gani na iso ina tasha.! daga d'ayan bangaran Mom ta murmusa ta ce.. "masha Allah yanzu zan aiko driver ya d'auke ku"
"Toh hajiya" sannan ta datse kiran tana Murmushi ta kalli fatuha ta ce, "Yanzu za'a zo d'aukar mu kin ji yan'nan" kad'a kai fatuha tayi dan ita a wannan lokacin haushin kowa take ji.
Ba'a fi 30 minutes ba driver ya qaraso tare da kwashe kayan su ya zuba cikin mota, inda yayi-yayi da fatuha ta bashi Jakarta ta qi ba yanda ya iya haka ko suka tafi.
Kai tsaye sultan road suka wuce nan fa fatuha ta fara zare ido tana qarewa unguwar kallo kamar wadda ta zo aljana haka take gani, Washe baki tayi ta juyo tana kallon baba jummai ta ce... "Baba jummai dama ashe aljanna kike zuwa? Baba jummai dariya tayi ita da driven ta ce.. "a'a fatuha nan ba aljanna bane birni kenan"
"kai amma kwarankwatsi kinyi da kika zo dani dafa tare da fatsima kikaso zuwa ko?
"ke da kikaita kuka baki san zuwa"
"Qur'an yanzu ina san birnin 😃.! ta ida zancan lokacin yayi dai-dai da isowarsu katafarin gate din gidan Alhaji Ibrahim, zanso kuga yanda fatuha ke zarar ido.😂
Dai-dai parking space drive yayi parking baba jummai ta kwaso masu kayan su fatuha dai na maqale da ledar ta, ta gari yayi zafi.
Katafarin parlourn gidan suka shiga, qauyanci wajan fatuha ba'a magana dan ko zama taqiyi saboda tayals sai da baba jummai tayi da gaske sannan ta zauna saman carpet tana ta zara ido.
Mom ce ke saukowa daga upstairs cikin murmushi ta ce, "ah sannu da zuwa baba jummai" tare da qarasowa parlour da zama saman two star tana facing d'in su baba jummai d'in ta ce, "ya hanya? tana murmushi.
"Alhamdulillah," baba jummai ta ce, "oh tare da yarinyar kuka zo kenan gaskiya naji dadi" fatuha dake ra6e jikin baba jummai ta gaida Mom cikin girmamawa, baba jummai ce ta washe baki ta ce, "Ai diyar qanina ce jauro"
"a'a ki ce min yar tashi ta yi girman haka"
"aiko dai hajiya" Sunyi hira sama-sama inda fatuha ke ra6e jikin baba junmai tana qarewa gidan kallo tare da santinsa.
Lafiyayan abinci Mom ta basu shinkafa da miyar kaji wadda taji coslow kauyanci ko wajan fatuha ba'a cewa komai, saboda bata ta6a cin irin abinci ba dan haka ta saki tinbi ta ci har da sid'e kwano da qari, Baba jummai dadi taji dan taga fatuha ta saki jikinta.
Bayan sun gama cin abinci Mom ta kai fatuha d'akin jidda ta gwada mata toilet da duk yadda zatayi anfani da komai na toilet d'in tare da ciro mata uniform din yan'aiki farar Riga da skirt dai-dai gwiwa.
ba laifi fatuha duk abinda Mom ta gwada mata haka tayi..
wanka sosai tayi ta dirje jikinta tare da wanke kanta da shafo, masha Allah gashin fatuha har gadan baya sai dai rashin kulla da shine yasa duk ya cure gu d'aya amma hakan bazai hanaka ganin kyan gashin ba,d'aure da towel ta fito, Mom na zaune saman sofa tana jiran fitowar ta, koda ta d'ago kanta Mom d'in, tayaba da kyau irin na fatuha, Hakan yasata yin murmushi ita ko saitahau sunne kai Mom ta katse ta da cewa, "Ah har kin fito? D'aga mata kai tayi alamar Eh , uniform din Mom ta d'auka ta bata ta ce, "ga wannan kayan kullun su zaki rinqa sawa akwai su da yawa cikin wardrobe ranar Friday ne kadai zaki sa kayan gida suma akwai su cikin wardrobe, na ki kuma anfidda su waje sannan in kayan sunyi dati ki aje su akwai mai wanki zai wanke maki su ya goge" Washe da baki fatuha ta ce, "toh.!
Mom har takai bakin kofa ta dawo tare da cewa, "gobe ki shirya za'a kaiki wankin kai" to tace tare da yima mata godiya Mom na fita ta shafe jikin ta da mai tare janyo kayan da Mom d'in ta aje mata a saman gado farar rigar ta fara janyowa ta saka amma sai da tasha wuya sannan ta iya balle ma6allin rigar, dai-dai gwiwa rigar ta tsaya mata kallon rigar fatu tayi ta furta a fili "Kwarankwatsi gidan ga gidan yan'iska ne yo jifa yadda rigar ta min" skirt din ta janyo ta sa tana sawa taga ya tsaya a gwiwa shima ta ce, "kut amma Qur'an mutanan sun rainani yo in ban da iskanci haka zanbi gari qafafu bude ta6 bilahilazi ban fita haka" guri ta samu tayi zamanta tana ta kunfar baki tare da jero Allah ya isa.
Mom dake zaune parlour jin fatuha shuru bata fito ba yasa ta leqo dakin zaune ta same ta har bacci ya fara neman d'auketa saboda gajiyar tafiya, ta6ata tayi tare da cewa "Fatuha.! Nanta ware manyan idanunta Mom tasakar mata murmushi take ce, "hala kin kasa sa kayan tashi kiga yadda ake sawa" nan Mom ta shiga gwada mata masha Allah kayan sun mata kyau duk da fatuha tsine wa kayan take a zuciyar tare da jin haushi kayan.
Bayan Mom ta gama gwada mata ta bata d'ankwali ta rufe kanta ruf kamar wadda tayi acuci yadda kan ya gwada, sannan ta ja ta suka je parlour suka zaune saboda Sadiq sun fita da jidda shan ice cream.