← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 67

Sashe 14

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Bayan sun gama shan ice cream suka biya shoprite ya siya wa jidda new Teddy's masu kyau da kayan wasa jidda ko sai murna take a gajiye suka dawo gida, Sadiq na d'auke da jidda a hannusa yana  mata cakulkuli tana dariya *ola* na bayan su riqe da kaya cikin sallama suka shigo, Mom na zaune tana kallo fatuha na gefan ta a takure, a ahankali Sadiq ya qaraso jidda na maqale a jikin sa ya kai ma Mom peck a kumatu, Mom ce ta murmusa ta ce, "baby har kun dawo?
            "yes Mom" sweet voice din Sadiq ne ya doki dodan kunnan fatuha ta waigo baki bud'e tana qare masa kallo shi da jidda sakin baki tayi a zuciyarta ta ce, "dama ashe ina da raban ganin yan makka kai baba jummai kwarankwatsi kin dubamin, duk wannan zancan da take idanun ta na kan su jidda, dagowar da Sadiq zaiyi su kayi 4 eye's da  Fatu harara ya wurga mata saboda yarda  ta  tsare sa  da  idanu ya kauda kansa ya  ce, "wannan wacece bata  iya  gaisuwa  ba  sai  kallon" murmushi Mom tayi ta ce "wadda zata dinga kulla da jidda ce diyar qanin baba jummai ce" kallon fatuhan yayi wadda ke kallon su bata dauke ido ba baki  sake harara ya qara banka mata sannan fatuha ta ankara ashe harara yake aika mata aiko itama ta fakaici idon Mom ta banka masa harara har da murgud'a masa baki,  sakin  baki  baki  captain  sadiq yayi yana mamakin wannan wacce mara kunyar mai aiki ce Mom ta samu wadda bata da kunya haka  har  lokacin  tana  banka  masa  harara a fusace ya tashi ya ce, "keeeee!! Ni sa'an kine..! Kike  kallo  na  haka? Mom da ke zaune ta ce "Sadiq lafiya yarinya na zaman zamanta ka fara yi mata bala'i ka bari mana ta kwana biyu sannan ka nuna mata bakin halin naka, wai me yasa kake haka ne baby? fad'a Mom  ta masa sosai cikin zafi rai ya bar parlour sannan ta shiga ba fatuha hakuri  washe da baki ta ce "ba komai" Mom ta gwada mata jidda ba qaramin dad'i fatuha taji ba zata kulla da balarabiya bayan Mom ta gama yi mata bayani sannan taqara mata da batun zata riqa gyara part din baban jidda sosai fatuha taji dadin hakan.
   a cikin zuciyar ta kuwa cewa ta ke Qur'an daba balarabiya ba ce da wallahi bani kula da Ita, shi kuma wancan balaraban ni zaiwa iskaci  wai dan yana da kyau. Qur'an gyara mai zama zanyi bilahilazi duk wannan maganar tana yin tane a cikin  zuciyar ta.

Written by
        Salma mas'ud nadabo

Edit by
      Raheenat

    📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★

https//,mobile.facebook. com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&_yn_=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

                      29_30

Mom ce ta haura upstairs ta bar jidda da fatuha zaune a parlour ,a hankali fatuha ta matso kusa da jidda washe da baki tace "Ya sunan ki?" smile jidda tayi tare da fad'a mata sunan ta, sun dad'e a parlour zaune sannan jidda ta ja fatuha suka koma bedroom d'in jidda, jidda ta fara kwaso wa fatuha kayan wasa, washe da baki fatuha ta amshi teddy tana  cewa, "kai Al Qur'an birni dad'i garai yanzu saboda Allah ji wanga halita duk wasa ake da ita kai jama'a" jidda ce ta katse mata zance da cewa, "Anuty garin ku ba wannan teddy ne? nima daddy ke siyo min" dariya fatuha ta fashe da ita ke kekika san wani Daddy mtsss, kuma me Anuty da tedil (teddy)? jidda dariya tayi ta ce, "Aunty  ba sunan shi tedil ba sunan shi teddy, Anuty kuma idan mutun ya girme kane sai ka dinga ce masa Anuty"
           "aiyo ai mu a kauyen mu yaya ake cewa ko gwaggo, Ah wanga suna Qur'an dad'i garai haka birni ya ke" jidda dai washe baki take tayi ta samu yar'uwa kamar ta me shegen surutu.
             Haka suka rinqa zuba hira tare da wasa ita dai fatuha, zuciyar ta fes dan a ganin ta ta samu gurin zama kiran sallah magrib ne yasa suka tashi, fatuha tayi alwala tare da jidda sannan suka fito dan gabatar da  sallah.

            Bayan sun gama sallah suka dawo parlour, parlour ba kowa sai baba jummai da ke ta jera abinci ita da rabi'a washe da baki fatuha ta gaida baba jummai da rabi'a, baba jummai ce tac e, "Ah fatuha anware kenan?" dariya kawai tayi "toh ga abinci nan idan kuna jin yunwa ku zo ku ci ki tabatar kin ba jidda ta ci ta koshi" inji baba jummai, "toh.! kawai fatuha ta ce mata sannan baba jummai da rabi'a suka shiga  kitchen.
            Kamar jira take su shige tayi tsale ta haye kujera dining area dakyar ta iya bud'e kulolin farfesun yan'ciki ne sai dafafan doya da miyar kifi, tunkan ta fara ci miyan bakinta ya tsinkewa, zubawa ta fara yi sai da kwanan ya kai har baki sannan ta tsayar da zubawa, jidda ko sai zaro ido take tana mamaki irin ci na sabuwar Aunty ta,
lol.

   Washe baki tayi ta ce, "Yauwa jidda sauko muci dan Qur'an ban iya ci a saman wannan abin," haka ko akayi suka sauko qasa suka fara ci, fatuha na ci tana zaro ido saboda dadi kuma ba wai qaramar loma take ba haka zata dauko doya biyo ta turawa kanta ta kuma turawa jidda.

        Zaune yake saman sofa da alama daga wanka ya fito, shafe jikinsa yayi da lotion  mai kamshi, yana gamawa ya feshe jikinsa da turare mai sanyi dad'i, wardrobe ya bud'e ya ciru 3quarte black sai fara t-shirt hannu rigar  dai-dai tamatsa ba qaramin kyau yayi ba bodybuilding  nasa  yafi  gwanin ban  sha'awa da  birgewa gashin nan nashi ya kwanta abin sha'awa luf-luf, ahankali ya kama handle d'in kofar part nashi ya fito.
        Cikin natsuwa yake  sakowa daga upstairs, sanye yake da bakin Sweet yayi masifar yi masa kyau, fatuha da jidda na  zaune a k'asa ga plate a gabansu sai loma fatuha ke tura wa jidda, dan ita har ta koshi kuma da hannu take bata abincin, a fusace sadiq ya qaraso tare da dakawa fatuha tsawa "Keeee.! Are you mad? you are very stupid" futaha ko ware ido tayi washe da baki ta kalle shi tace, "Ta6 kai ka san wannan gwalangwatsin Qur'an" sannan ta cigaba ta d'irkawa jidda doya jidda ko sai amsa take hankali kwance, lumshe ido sadiq yayi ji yake kamar ya shaqe fatuha dan haushi daka mata wata tsawar yayi ya ce, "Dan ubanki baki jin nane? uban waye yace kiyi feeding  angel da  hannu ba  spoon ne eeeh?" Turo baki gaba fatuha tayi ta ce, "yo ni ban san inda fida (feeding) take ba ashe ba'a yaye taba Qur'an ban sani ba" sannan fatuha ta ce da jidda "shine kika saki tinbi ina ta dirka maki abinci,to ta yaye kanta sai ka zubar da fida(feeding)lol.
           Wani irin baqin cikine ya turniqe sadiq  ya qara wurga mata harara , aiko itama ta rama tana  cewa, "yo a kan me mutun tunda na zo gidan su sai aika min harara yake, ba dan nayima Hajiya Alkawari zan zauna da ita iya wuya ba, da  sai nace banyin aikin ko ana dole ne, kama gode wa Allah saboda Kuna kama da larabawane shiyasa na tsaya da bilahilazi da tuni nayi tafiya ta aha" tare da gyara tsayuwar ta, sadiq ko baki ya saki yana mamaki irin wannan iskancin da  kauyanci tare da  tsantsar  rashin  kunya da  rashin  tarbiya irin  na  fatu  wanda  ko  girman  sa  bata  gani, tsawa ya kuma daka ma fatuha wadda tasa yan'hancita katsawa "dan ubanki ni sa'an kine ni eeeeeh? ido fatuha ta qara zarowa, sannan ya nuna ta da yatsa ya ce "Wallahi duk sanda na qara magana wannan dan banzan bakin naki ya maida min sai na fasa shi" ya qara wurga mata harara sannan ya sa hannu zai d'auki jidda, ihu fatuha ta saka hakan yasa sadiq  juyowa yana mata kallon  wulaqanci, "Qur'an ba inda zaka da balarabiyan nan kwarankwatsi, ko na fada ma hajiya tunda ita ta bani ita" dariya abin ya kusa ba ma sadiq amma sai ya d'aure ya wurga mata harara, a rayuwarsa  bai  ta6a ganin mara  kunya  irinta  ba  yar  kauye wadda  bata  jin  ko  tsoron sa.

    Mom dake bedroom taji ihu fatuha hakan yasa ta fito da sauri, ganin sadiq d'auke da jidda fatu  na gefe tana ihu yasa mom qarasowa, harara ta aikawa  sadiq tare da cewa, "Lafiya fatuha? me kuma ya miki?" turo baki tayi ta ce, "Yanzu saboda Allah hajiya ba ke kika bani wannan balarabiyar ba, na kulla da ita, to shine wai daga yaga ina bata abinci ya hau zagina har da ce min wai fida take sha" hajiya ko dariya abin  ya bata saboda ta gano abinda fatuha take nufi, sannan fatuha ta ce, "To shine hajiya yasa hannu zai d'auke min ita Qur'an ban yadda ya maido min abuta" murmusawa hajiya tayi  tana  konshe dariyarta ta ce "Yi hakuri fatuha ai baban ta ne shiyasa"
             "aiyo toh shine hajiya bai iya fada min dan girman Allah, ki ce ya ban  yarinyar dan Qur'an sonta nake" tare da matse kwalla, Mom ko dariya abin ke bata sadiq ko mamaki abin ke ba shi yau shida d'iyar sa za'a masa qarfin hali, Mom  ta  ce, "Toh shikenan sadiq bani jidda idan ta mata wanka sai ta kawo ma ita, ai shikenan anraba rigama ko fatuha? sadiq 6ata fuska yayi ji yake kamar ya shaqe fatuha dan haushi.
                Haka sadiq ya miqa wa Mom jidda tare da haurawa sama, sannan ya d'au alwashin sai ya gyarawa wannan yarinyar zama dan yaga alamar da rashin kunya tazo.

       Fatuha ko washe da baki ta amshi jidda, jidda ko sai raba ido take gashi cikin ta ya cika dam kamar yayi magana......

Written by
        Salma mas'ud nadabo

Edit by
    Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★we are the best★

https//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial&_yn_=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook. com/REAL HAUSAFULANIWRITRESFORUM.com

*rip rip this page is for you my lovely one so enjoy the page this na for u no be so*😉

                        31_32
Chapter 14 · 0% Book details