Sashe 59
Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Cikin masallaci ko MALAM JAURO YA BADA DIYARSA KAN SADAKI NAIRA DUBU DARI GA DAN ALHAJI IBRAHIM WATO SADIQ IBRAHIM, MALAM ALIYU YA MIQA DIYARSA KAN NAIRA DUBU DARI WATO FATSIMA ALIYU GA DAN ALHAJI KHABIR WATO ABDULMAJEED KHABIR, TARE DIYARSA BASMA YA MIQA TA GA DAN ALHAJI SANI WATO KHALEED KAN SADAKI NAIRA DUBU DARI kowa na masallaci kallon-kallo aka koma mamaki ne ya lullu6e kowa.
sadiq wanda fitowarsa kenan majeed ya biyosa ya kwalla masa kira da cewa "Baby..! waigowa yayi idanusa jawur ya galabaita sosai ya fita hayacinsa yana sauke numfashi a hankali tafe da zuciyarsa hawayan wahala na bin kumatunsa ya jike sharkaf da zufa zaro ido majeed yayi da karfi ya murfa, "sadiq..! dim sadiq ya durkushe a kasa duniyar na juya masa yana sauke numfashin wahala dakyar-dakyar ya sulale baya numfashi, da gudu majeed ya qaraso tare da sakin kuka yana cewa "No..! no..! Baby karka min haka ka tashi ka ji baby.! Majeed na maganar yana dan dukan fuskar sadiq da ko motsi bayayi cikin matsanan cin kuka ya ce, " in dai fatu ce na bar maka sadiq bana son ta Allah, duk laifi nane na kashe baby da kai na tashi ka ji baby kasan bama haka sadiqqq..! majeed ya koma tamkar zarare yana magana hawaye na masa zarya Dr yakub da kusan tare suka iso wurin daskarewa yayi tsaye ganin halin da sadiq yake cikin jikinsa rawa ya dauka kaf-kaf dan baya tunanin akwai sauran wani abu rai jikin sadiq su Baba da Abba dake cikin masallaci da alhaji babba jin yarda majeed yake kururuwar kiran sadiq suka fito da gudu liman ya rufa masu baya da yan daurin aure.
Dakyar Dr yakub ya samu damar bud'e baki yana tsiyayar hawaye ya ce "Ba kuka zamuyi ba, muyi sauri mu kai shi asibiti" jikin majeed na rawa ya dauki sadiq chak ya bud'e murfin mota yana kuka ganin ba zai iya tuqin ba yasa doctor yakub ya amshi car key din suka bar harabar masallaci da gudu su Abba suka rufa masu baya.
kuka majeed yake yana cewa "Ban taba tunanin abin ya kai haka ba? am so sorry sadiq ka yafemin, duk nine sila" sanbatu yake sosai a haka suka iso asibitin sai da aka wuce dashi emergency sannan majeed ya zame jikin bango tare da sakin kuka, wayarsa ya curo cikin aljihu ya danna number Umma bugu daya zuwa biyu ta dauka kuka majeed ya saki yana cewa "Umma saboda ni ina ji ina gani baby zai rasa ransa? Ya fadi hakan tare da sakin kuka ita kanta Umma kuka take dan labarin tuni ya cin masu ta tausayawa sadiq.
Kafin ka ce me, asibitin ya cika da yan'uwa, majeed na ganin Abba ya mike da sasarfa ya qarasa garesa ya fada jikinsa yana kuka kamar qaramin yaro ya ce, "Shikenan Abba bakin ciki na zai kashe baby, bazan ta6a yafewa kai na ba har sai sadiq ya tashi lafiya Abba ka ce su ceto rayuwar baby duk nine sila komai, na tafka babban kuskure nayi anfani da son da baby ke min na cutar da shi..! a hankali Abba ke shafa bayan shi tare da zaunar da shi d'aya d'aga ciki'n kujerin dake gurin, ajiyar zuciya kawai majeed ke saki cikin sanyin murya Abba ya ce, "Ba laifin ka bane majeed ka ji.! har da laifin sadiq da yayi nauyin baki ya kasa fad'a, da kansa yayi wasa da damar daya samu, hasali yarinyar nan kullun suna tare gida daya kusan komai nasa ita ce amma yayi zurfin ciki da nauyin baki? ko yanzu da kukayi magana aka sauya daurin auran? indai fatuha tace bata son sa dole ya sake ta" kuka majeed ya saki tare da cewa, "Abba da kunne na naji irin son da suke ma juna su, kamar yarda basu rintsa ba jiya, nima ban rintsa ba ina jin irin kalaman da suke fadawa juna, kuma dama na dade ina zargin akwai so tsakanin su amma baby yaki furtawa, tun ranar da aka sa bikin mu, sannan Dr yakub ya karamin bayani daran jiya, Abba dan Allah a taimaki rayuwar baby? ya ida zancan yana qara sakin kuka, haka abba ya dinga lallashinsa har yayi shuru, Ammi ko sai kuka take tana share majina saboda tausayin sadiq, sai yanzu suka san abinda ke damun sadiq.
Duk iya bakin qoqarin likitoncin asibintin sun kasa duk da suna manya-manyan likitoci wayanda ake ji da su, sosai hankalin su ya tashi suka fara fidda rai da sadiq, da sauri suka fito daga emergency suka ba Abba shawara ya fidda sadiq waje kawai duk da can ma basu da tabbacin warakasa domin ya riga da ya zo ga6a, biza Abba yasa aka masa dan a fitar da shi waje saboda a wannan karan ciwon yayi tsanani, dan yafi buqatar a masa aiki gaggawa tahanyar samun qwararin likitoci.
Su Baffa na isa wudil jiki bakwari sanin halin da suka bar sadiq ya sanar da su, Inna an daura auran fatuha, wani irin kuka fatuha ta saki dan yanzu ta tabatar da ta zama malakin majeed kuka take kamar ranta zai fita, lallashin ta su Aunty bilki suka shigayi dakyar aka samu fatuha ta shirya.
ko da ta shirya dakin Baffa aka kaita ya mata nasiha sosai duk wannan nasihar da Baffa ke ma fatuha kuka take har da shesheqa abun gwanin ban tausayi, a haka aka tataro ta aka sata mota taci kuka sosai sai anjiyar zuciya da take ta saki, dan ko fatsima bata nema ba.
Bangaran fatsima ko su gwaggo sun gyara ta sosai duk da bata jin son majeed amma a yarda ya mata bayani da yarda su gwaggo suka mata hakan yasa ta fara jin son sa, dan tayima kanta alqawarin bashi farin ciki, haka suka shige motoci amaran aka harba da su kan titi ,
Tunda fatuha ta ga an iso kano ta qara sakin kuka mai cin rai, sosai take kuka kamar ranta zai fita, a yanzu kam kukan fatu ya fara d'agawa su Aunty bilki hankali dan ba kukan lafiya fatu take ba, suna isowa family house aka bude mata murfin mota fatu na fitowa ta yanke jiki ta fadi luuuu jikin Aunty bilki sumamiya...
Vote
Comment
Written by
Salma mas'ud nadabo
Edit by
Raheenat
📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best ★
http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-
*Email* [email protected]
*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFUROM.COM
93_94
Daukar fatuha akayi chak aka maida ta mota aka ja suka bar harabar gidan Hanan sai matsar kwalla take basu zame ko ina ba sai asibitin da aka kai sadiq, suna shiga lokaci majeed na qoqarin fita kamewa yayi yana bin su da kallo kamar gunki ganin halin da fatu ke ciki duk saboda shi, bin bayan su yayi wasu hawaye masu zafi na masa zarya duk wannan abun da ya faru saboda shine, shiga da fatuha emergency akayi.
Bayan yan mintoci aka fito da fatu har lokacin bata farfado ba tana kwance amma Dr yace da sauki tashin hankali da tunanin ne ya haifar mata da yankewar jiki ta fadi, dakin da aka kwantar da sadiq aka kwantar da fatu kafin anjima jirgin su ya tashi har yanzu kwance yake bai san halin da ake ciki ba