← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 67

Sashe 36

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Cikin sanyi murya ta kuma cewa "Mai kyau.! ware sexy eye's ball's din yayi ya qara sauke su kan lips din ta cikin shagwaba da sanyi murya ta ce, "Mai kyau dan Allah ka ci farfesun  nan ka ga likita yace ka ci abinci"   hade rai sadiq yayi tare da lumshe ido tare da yin magana cikin cool voice nashi ya ce "Bana jin yunwa fatuha" dan bata rai tayi tare da rausaya kai ta ce "Dan Allah kaga ko akauye idan bani lafiya idan banci abinci ba inna har dure take min, dan na samu lafiya ka ga yanzu Mom bata nan bale ama dure, dan Allah ka ci" ta ida zancan tana rausaya kai tana kallon sadiq dake kallon ta kamar qaramin yaro qara hade rai yayi ya ce "ba fa naci leave me alone pls" zaro ido fatuha tayi ta ce "Kai kasan wannan"  murmushi yayi wadda bai yi niya ba ya ce "Fatuha wai yaushe zaki waye?" dariya tayi ta ce "Sai ranar dana fara zuwa boko ka ga da jidda nan ita ke koyamin yanzu kuma tana gidan Aunty bilki" ta ida zancan tare da yin raurau da ido sadiq  ya  ce, "ai ta kusa dawowa kin ji, uhm to kina san karantun ne? bai ida rufe bakin shi ba Dr yakub ya shigo, cikin sallama tare wurgawa sadiq harara dake kwance gaisheshi fatuha tayi har qasa sannan ta dau boll din farfesun ta aje a tray tana qoqarin fita doctor  yakub ya  ce, "ah wai fita zakiyi da kin tsaya ai" murmushi fatuha tayi ta ce "Ina da abinyi ne a kitchen shiyasa"
    "ok.! wannan abincin fa nawaye? kallon sadiq tayi dake ta faman aika mata harara tayi tsaye tare da sada kanta qasa, juyowa Dr yakub yayi su kayi ido hudu da sadiq "mtww haba captain me yasa kake haka ne please, wai bana sha fada ma ba ka rage damuwa ba uhm saboda tsabar damuwa  ka daurawa kanka hawan jini, me yasa kake abune kamar mara tawakali ai kowa ya sani duk me rai mamaci ne tunda kausar ta bar duniya ka daina walwala ka maida zuwa asibiti kamar zuwa kasuwa, haba captain ko dan lafiyar ka da matsayin ka ka hakura da wannan tunanin please," lumshe ido sadiq yayi kamar yakub na magana da dutse tsaki Dr yakub yaja ya ce "To wannan abincin da kaqi ci  me hakan ke nufi?" ware ido yayi yana aika ma fatuha harara dan shi kwata-kwata baya buqatar wani abinci a cikin shi amma saboda tsabar naci irin na fatuha yanzu tasa sai ya ci abinci dan guntun tsaki yaja yana kallon yakub dake ta masifa yanzu "ka daure ka ci abinci ko nama alura ai dai ba saina fadama ila da alura kema mutun ba idan ba abinci ba" duk yadda ya so ya kauce ma qincin abinci sai da yakub ya takura masa ya sha farfesun kad'an  ba tare da bread ba ba laifi farfesun ya masa dadi duk da bakinsa ba test aje boll din yayi fatuha ta dau tray din ta fita alura Dr yakub ya masa tare da daura masa ledar ruwa saboda ya lura sadiq baya san cin abinci yana lafiyar ma yaci kadan bale yanzu.

     Dawowar fatuha ce tasa Dr miqewa ya ce "To ni zan wuce dan Allah ki kulla da cin abincin shi idan bai ci ba ki kira Aunty bilki ki fada mata ai yasan halin ta"  d'aga kai fatuha tayi sannan ta taimakamasa da daukar masa  briefcase din har sai da suka zo bakin kofa ta masa sallama ta rufe gidan bedroom din sadiq ta kuma.
           Tana dawowa harara ya bita da shi sannan ya ja saki murguda masa baki itama tayi tare da zama saman sofa sanin  ba  zai  iya  tashi ba  yasa  fatu  haha sadiq  ya  ce, "keee wakike murgudawa baki? raurau da ido fatuha tayi ta ce "Bada kai nake ba"
           "Dawa kike to? ya fada cikin sigar masifa "uhm ba da kai nake ba wallahi"
        "mtww wallahi karki bari na tashi dan na tashi saina karairayaki, bama na hana ki yawo ba hijabi ba eh?
    "amma ai a waje ka ce ba'a gida ba,"  tsaki ya  ja, mtww  sannan ya juya ya lumshe ido.Written by
      Salma mas'ud nadabo

Edit by
     Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★We are the best★

http/Mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=,H-R

*_Email_* [email protected]

*_Facebook_*www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                   63_64

Juya bayan da sadiq yayi yasa fatuha jan dan guntun tsaki tare da kallon agogan dake maqale a bango kusan karfe 8:30 na dare, tashi tayi ta bar part din ta koma part din su tana shiga bedroom ta rage kayan jiki ta, ta  shiga toilet ta sheqa wanka ta fito daure da towel ko shafa mai ba tayi ba, ta bude wardrobe ta ciro kayan baccin ta riga da wando pink masu mayan flowers da zanan ya'yan cartoon, d'aure gashi kanta tayi da wata yar kibiya ta d'aure kai sannan ta fesa turara har zata kwanta sadiq ya fado mata a rai ta barshi a d'aki shi kad'ai, gashi baya da lafiya tashi tayi zubur zata fita sai kuma taci birki ta ce "Ko naje tijara zai mun dan ba mutunci gare shi ba, karma ya tsinka ni.! wata zuciyar tace haba fatuha duk rashin mutuncin mutu bai da lafiya ai dole ya shafa wa mutane lafiya riqe handle din kofar tayi kamar me na zari can kuma ta bude ta wuce part din sadiq  ta shiga dakin har yanzu bacci yake parlour ta dawo ta kuna kallo dan ba wani bacci take ji ba  cikin jin dadi take kallon arewa24 suna shirin tarkon kauna  gaba ki d'aya film din ya mata d'adi sosai sai da aka kamala film din misalin karfe 10:00 na dare sannan ta leqa dakin sadiq, bakin bed din ta tsaya tana qaremasa kallo a hankali ta kai hannu zata taba goshinsa amma ta kasa dunqule hannu tayi tana nazarin jikin nasa ganin ya motsa ya sata gyara tsayuwa tana kallon yanayinsa lumshe ido tayi a hankali ta kai hannu tata6a goshin sadiq ji tayi zafi rau kamar garwashi mamaki ne ya kamata da tsoro cikin rawar murya ta ce "Mai kyau?" shuru sadiq yayi saboda shi kad'ai yasan yadda yake jin fever na damu shi kneeldown fatuha tayi gaba gadon ta qara cewa, "mai kyau.! a qaro na biyu, bude sexy eye's ball's dinsa yayi a hankali yana kallon fatuha data fara matsar kwalla smile yayi ya ce cikin cool voice nashi "Menene fatuha? kin kasa bacci ne?" girgiza kai tayi alamar a'a "to menene? kallonsa fatuha ta kumayi ta ce "har  yanzu masasaran nan bata  sauka  ba  duk  da  likita  ya  duba  ka  tana matsama baka ji jikin ka da zafi ba? da a kauye ne da inna ta dafa ma magunguna kuma da kasha zaka warke, amma nan likita sai duba ka yake amma ka qi warkewa mai kyau, dan Allah ka daina tunani kaji shiyasa kaqi warkewa" ta fadi zancan tana zubar  da  hawaye kallon ta sadiq kawai yake yana mamaki irin tausayi na fatuha gabaki d'aya tabi ta rude tunda taga bai da lafiya lumshe ido yayi tare da warewa ya sauke so a kanta ya  ce, "insha Allah fatuha zan daina kinji" murmushi ta saki mai hade da kuka-kuka ta tashi ta shiga toilet din sadiq shi kuma ya bita da kallo ruwa ta d'ebo a babba boll na  roba tasa towel a ciki ta dawo d'akin har yanzu idanuwan sadiq na kan fatuha ko qif tawa bayayi, sai da ta qaraso gaban shi ya lumshe ido aje boll din tayi a gefen bedside drawer idanuwanta  taf  da  hawaye cikin nutsuwa ta shiga matse towel din a hankali ta nufo towel din goshin sadiq ta fara dadanna masa kamar yadda inna ke mata idan tana masasara,  ko ina na jikinsa take  bi inda ke bude tana danna masa towel din a hankali fever ta fara sauka shi kanshi Sadiq yaji dadin jikinsa sai dai dan dumin da jikin yayi bacci ne ya fara fisgar shi kafin ka ce me bacci ya kwashe shi, sai fatuha dake ta faman dannamasa towel.
      A hankali ta fara gyangyadi dan ta fara jin bacci, sai bacci ya fisgeta sai firgigit ta tashi ta cigaba sai da bacci yaci karfin ta, ta fada fadadan qirjin sadiq bacci ya kwashe ta.

         Kiran sallah asuba ne ya tashi sadiq a hankali yake bude sexy eye's ball's din shi ya sauke su kan fatuha da ke bacci male-male a qirjinsa gashin kanta ya baje saman qirjinsa ta  kankame sa, matsar da gashin kanta yayi gefe yana qarema fuskar ta kallo, har mamaki wayau irin na fatuha yake gata qarama amma sai dai tana da halin manya, kasa  dauke  idanusa  yayi  kanta, yunqurin tashi yayi yaji ta motsa komawa yayi ya lumshe ido yayi  lamo kamar mai bacci.
         tashi fatuha tayi tare da ware ido ganin  ta  jikin  sadiq  kwace a  zabure ta  mike  tsaye ta ce "Nashiga uku yaushe bacci ya kwashe ni? wayo Allah na da mai kyau ya tashi ya ganni dana bani" hannu ta kai goshin sadiq jin ba zafi yasata sakin ajiyar zuciya ta  furta, "Alhamdulillah jikin yayi sauki bari nayi sauri na d'auro alwala" part din ta bari ta wuce nasu.

      Alwala kawai ta dauro ta gabatar da sallah, bayan ta idar ta tsaya lazumi da bita qaratun ta saboda anjima da rana malam zai amsa.

     Fatuha na fita sadiq ya ware idanuwan shi tare da ta6e baki ya yunqura zai  tashi  yaji hannu shi yayi zafi, sai a lokacin ya tuna da ledar ruwan da aka qara masa har ruwan ya qare ga hannu ya kunbura, ya manta shaf bai cire ba yaye blanket din jikinsa yayi ya shiga bathroom sai da yayi wanka ya fito sanye da bathrobe da qaramin towel a hannu shi yana goge sumar shi da hannu daya, saboda  d'aya hannu namasa
zafi  sosai.
Chapter 36 · 0% Book details