← Book details Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 67

Sashe 34

Captain Sadiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

  bashi ya dawo gida ba sai bayan sallah isha'i, yana shigowa parlour dining area ya wuce yana b'ude kulolin yaga alamar fatuha bata ci abinci ba dogon tsaki yaja tare da rufe kulolin, Kwala mata kira yashiga yi shiru ba'a amsa ba dan haka cikin nutsuwa ya nufi dakin fatuha ya murda handle din kofar can saman gado ya hango fatuha cikin cool voice din shi ya ce mata " Yanzu dan iskanci
kina jina  kikayi   banza dani? tayi shiru bata tanka masa ba, rashin yayi mugun bacci dan haka ya daka mata wani uban  tsawa  wadda ta sata zabura ta sauko daga bed tare da fashewa da wani sabon  kuka😭, harara ya aika mata ya mata nuni da ta biyoshi, bin shi take har tana sarke kafa dining area ya isa itama taja ta tsaya ya  ce, "oya wuce kici abinci" a takaice tace masa ta koshi, wata tsawa ya kuma daka mata jiki na bari tana kuka ta fara zuba abincin dan kadan ta zuba, wani irin kallo sadiq ya wurga mata tare da yin magana cikin daure fuska "Haka kike zuba abinci eeeh?"  kuka tasa tana  mamakin  yarda  sadiq  ya  karanci  cin  abincin ta tare da cigaba da zuba abincin har ya kai bakin plate din, tana qoqarin qara zuba wani sadiq ya matse hannunta da karfi har sai da ta saki qara, saboda ya lura bata da niyar daina zuba abincin kuka ta  saki  tare  da  zaman  dole, juya abincin ta shigayi ta qasaci  sai kuka, cikin  murya mai sauti sadiq ya ce "Ko kiyi ma matune shuru! ko nasa alburushi  na bula maki kai kowama ya huta, kuma abincin karki ci ki bari na tashi tsaye Allah danne ki zanyi na dura maki har da plate din" cikin hawaye fatuha tashiga dura abinci har tana jin kamar zatayi amai amma sai da ta cinye shi tana gama ci tayi qoqari tashi cikin sauri sadiq dake saman kujera dining area ya lumshe ido kamar me jin bacci, har tayi nisa ya ce "Fatuha..! juyowa tayi tana kallon shi hawaya da ke maqale a idanuwan ta suka gangaro bisa kumatunta tayi  kala  tausayi  baby face  nata  yayi  jawur, wani irin yerr sadiq yaji ajikinsa   kallon  ta yashiga yi kamar yau yafara ganinta har wani  langwa6e kai  yake  yana  kankance  ida yakara Kiran ta akaro nabiyu   "Fatuha..! gaban tane ya yanke ya fadi kuka ta kuma saki tare da dawowa ta durqusa gaban shi tana rera wani saban kukan, a hankali sadiq ya kai lallausan hannun shi ya cigaba da gogema fatuha hawayan ta, lumshe ido tayi tare da ware su kan  sadiq dake  kallonta, yana gama goge mata hawayan  ya mata alama da  ta tafi har tayi gaba ya ruqo hannun ta  juyowa tayi da sauri idanu  ta  waje  tana  sauke  numfashi  da  sauri  da  sauri domin ita yanzu yafara bata tsoro,  langabar da kai yayi ya ce,    "Fatuha please kukan ya isa  haka"  kallon shi take shima din haka,     wasu sabin hawayan ne suka qara zubowa wani irin kallo sadiq ke bin ta dashi ya koma abin tausayi kamar bashi ba  hakan yasa fatuha hadiye wasu hawayen, smile yayi tare da sakin ta cikin sauri ta shige daki tare da fada wa saman  bed.
        shima sadiq upstairs ya haura cike da farinciki dashi kansa mamakin haka yake..... Hmmm kayi bayani Sadiq😘.

Written by
     salma mas'ud nadabo

Edit by
    Raheenat

📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
  ★we are the beat★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*_Email_* [email protected]

*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM

                   59_60

       Tun ranar da fatuha tasha maqara ta shiga wasan 6uya da sadiq, kwata-kwata bata bari su had'u dan ta lura aljanu gare shi, lol ko gyaran part nashi za tayi sai ta bari ya tafi office haka shima bangaran sadiq bai wani damu da rashin ganin na ta ba, saboda yasan lafiyar ta lau of cos yana ganin part nashi fes.

      Fatuha da rabi'a sun wani qara shaquwa musanman yanzu rabi'a bata tafiya gida sai 4, shiyasa fatuha ke dan jin dad'in gidan ita dai burin ta bai wuce ace su Mom sun dawo ba ko Jidda dan ta gaji da zaman kad'aici, ku san tare suke aikin ma yanzu dan fatuha yanzu ta fara gogewa da girke-girke dan yanzu kusan abinci gidan ita ke yin shi duk da rabi'a na hana ta.

      Misalin karfe goma na dare ya shigo gidan tsit ba motsin kowa, idan da sabo ya saba dama shi mutun ne ba mai son hayaniya ba part nashi ya wuce  tare da shigewa bathroom ya sheqa wanka, yana  fitowa ko mai bai shafa ba ya zura jallabiya white ba qaramin kyau ta masa ba, fitowa yayi daga part din na shi ya wuce main parlour direct dining area ya wuce abinci ya zuba dan kad'an shinkafa da miya ce tasha kayan had'i loma biyu zuwa uku yayi ya ture plate din dan kwata-kwata baya jin dad'in jikinsa gabaki daya, yayi missing din jidda bama ya ganewa yayi missing nata sai ya je bacci  zai ji bed din wayam sai dai yayata juyi har ya samu bacci ya dauke shi, gashi baya so ya je gidan Aunty bilki yasan yana zuwa zata ce Jidda ta kawo shi shiyasa yake hakura.
         bangaran su Mom ko duk san da ya tanbayi ranar dawowar su sai Mom ta ce sai sun gama abinda suke.

         Jiki ba kwari ya koma part din shi,  wata irin fever yake ji sama-sama ga qirjin shi na masa zafi, magani ya cura daga bedside drawer  ya sha sannan ya kwata ta tare da rufe jikin shi da blanket.

         Asuba ta gari fatuha na tashi ta tsala wanka tare da gabatar da sallah, sannan ta koma bacci cike da kewar su inna, dan gabaki d'aya yanzu kauye take so ta koma, zama gidan yanzu ya fara hawar mata kai abu d'aya ke mata dadi yanzu shine idan malam ya zo koya mata karatu shima da sun gama ya tafi zata shigo gida kamar maya, gaskiya ta gaji da irin wannan rayuwar gashi kwanan ta lura mai kyau ko abinci baya ci, anya yana gidan ma kuwa ba ita kad'ai suka bari ba sannan ta ja dan guntun tsaki tare da gyara kwaciyar ta.
Chapter 34 · 0% Book details